YAR SADAKA Page 1 to 10

Liman ne a gaba Sai Nasir da Bello tare da sauran mutane dake tayasu murna,,wasu Ko yan uwan mahaifiyar nijlah ne…
Tinda suka shigo yakumbo tabisu da kallo tana mamakin abinda ya kawosu adaidai wannan lokaci Kuma gaba dayansu,,kowanne ta Kalla fuskanshi dauke da annuri,,nan ta zauna Kan buhun dawa tana binsu da kallo..
Kinga yakumbo ruwa Zaki Basu ba wannan kallanba,,gaba daya suka Hada baki gurin cewa ah ah alhamdulillah ta zauna kawai muyi abinda ya kawomu..
Gaisu yakumbo tafara nan Taji suna yimata Allah ya Sanya alkairi” Seda suka gama ta juyo tana kallan Liman tace,,Liman me Kuma ya faru Naji ana yimin addu’a..
Eh yakumbo Yau Dai Allah yayi an daura auren yarinyarki” wacce yarinya Liman??, yakumbo ta tambaya mejin faduwar gaba,, nijlah dake kwance a qasa tana sharar hawaye tayi Shiru tana sauraransu tasan Dai ita dayace yarinyar yakumbo Dan haka ta Maida hankalinta gaba daya Kan Liman tanajin amsar dayake bawa yakumbo..
Yakumbo yarki nijlah,yanzun nan,Bayan idar da salla malam yabada aurenta ga…..Ai nijlah Bata jira Jin wane angon ba ta Tashi da gudu sabida Jin Kunya ya kamata,,Daki ta Shiga ta dauko dakalmin Danko Wanda yasha dinki da zare da allura tasa ta fita da gudu ta Bayan gidan,,kasan cewar gidan bashi da danga Babu Wanda ya Ganta.
Mashkur” zabura yakumbo tayi ta miqe tsaye cikin rashin hankali da dimuwa tace,,badai wannan yaran mashkur ba,da naira hamsin bashi masa wahalan badawa???
Eh shifa Malam ya fada Yana Kallan yadda yakumbo ta haukace ta tubure masa..
To Wallahi Baze taba yiwuwa ba ,Akan me Zaka auran da nijlah ga Bako Wanda bamusan asalinsa ba,hasalina karatun arnane ya kawoshi ruga…
Haba yakumbo be kamata kina fadar hakaba,,kinga Nasir yabamu labarin mashkur bashida Wani matsala ki kwantar da Hankalinki.
Cikin kuka yakumbo tace haba Liman yanzu shikenan nijlah zata tafi ta barni” Bazan iyaba,kugayamasa wallahi ki warware wannan aure aba Dan gari yadda koya na juya zanga marainiya,,Anya Ko Malam ka riqe amanar da danmu yabari,,kaico mutuwa kinyiwa yarinyar shigar sauri,wayyo niya Allah Na,,nan fa yakumbo ta juya tana fillanci Niko nayi zugun tare sauraranta sedai banji abinda take gayaba,,ta jima tana kuka kafin Daga bisani sukayi nasaran shawo hankalinta..
Haba yakumbo meyasa Zaki haka,,kinsan bakisan auren Kika yadda naje naba,,kaga Malam niba aureni Bani so Wanda Kaba auren nijlah Baze taba Zama kusa damu ba nijlah zatayi nesa damu bamusan rayuwar dazatayi ba.
Insha Allahu nijlah zatayi rayuwa me kyau ku kwantar da Hankalinku cewar nasir cike da tausayin yakumbo..
To Amma Dai ba yanzu Ze tafi da itaba ko??eh saimun gama service nan da wata 9 insha Allah” gaskiya yayi wuri yadai Yi hakuri Sai nijlah ta qara wayo nan shekara biyu saiya dauketa,,cewan yakumbo tana hawaye.
Shiru Nasir yayi ganin yadda tsohuwan ta Shiga Wani Hali yace to shikenan,,nan sukayi Mata sallama kowa ya tafi gida..
Nasir da Malam Sai Liman suka tsaya Suna tattaunawa..
Tinda nijlah ta fita da gudu ta Shiga gidan kawayenta tana Kiran su daya Bayan dayan,,bayan sun gama hallara ta fara rawa tana cewa Yau ranar auren nijlah Dan haka kowa ya shirya za’ayi wasa Na kece Raini Yau Yar gidan kaka da Malam zata Hada wasa a dandali..
Yeeeeeeee Yau akwai wasa,,ihu suka sa irin na murna suka sukafara zagaye Dan garin Suna waqa..
*’yan wasa ku fito wasa,Idan baku zoba samarinku suzo Bani Na fadaba angon nijlah ne,,angon nijlah ne me jan baki….*
Haka suka riqa waqa Suna wasa Suna Tara jama’a,,cikin lokaci kalilan nijlah da kawayenta suka cika dandali da jama’a” sosai gurin ya cika yakuma kawatar nan fa dandali me kidan kagane yasaki kalanginsa tare da masu kidan kwarya,,masu Kayan saidawa Suma baa barsu Baya ba sun zo..
Kamar yadda akeyi a kowanne biki haka nijlah da kawayenta sukayi Dan sun cika dandali da jama’a anata wasa irin na Fulani,tare da al”Ada irin ta da..
Liman dake tsaye Suna Magana yace,malam kama kida nakeji a dandali” eh Liman Nima haka nakeji Kuma Dai yanzu ba lokacin zuwa dandali bane”
Suna cikin haka saiga wasu yammata Suna tafiya,,Malam ne yace ku yara Ina zuwa,, Malam muna wasan bikin nijlah ne,,tafada tana cigaba da tafiya.
Cike da mamaki yace Ina ita nijlah,,tana dandali tabasu amsa ,, murmushi Malam yayi Dan yasan nijlah zata aikata Duba da yadda takesan auren,,a Fili yace yaro yaro ne kajifa Liman bikin aure sukeyi a dandali.
Eh Ai ta birgeni kaga baza’ayi aure irin Na yaseer da fatima ba,,dariya suka sa,,Liman yace Aiko Yau dandali Ze dauki jama’a Nima baza’a barni Abaya ba..
Tinda suka fita aka zo aka Gaya yakumbo nijlah Na dandali,, murmushi yakumbo tayi ta Rasa inda zatasa Kanta,shin me zatayi farin ciki Ko me..
Ta tabbata Idan tayi baqin ciki ta yiwa Allah butulci Dan haka ta karkata zuwa farin ciki nan itama ta tafi dandali Dan Taya diyar Tata farin ciki..
Bayan tafiyarsu Liman Nasir be bisu dandali ba Dan yace saiyaje ya taho da ango.
Sosai ya riqa sauri harya kai Daki,,nan ya Shiga Yana Kiran mashkur,, mashkur dake zaune Yana Hada Kaya zuciyarsa na quna ya dago jajayen idanunsa ya zuba Nasir.
Dasauri Nasir ya qarasa kusa dashi ,hannunsa ya riqe yace,, mashkur lafiya naganka haka kama Wanda yayi jinya Na wata guda.
Kabari kawai nasir Ina cikin tashin hankali,,ban taba Shiga cikin matsala irin na yanzu ba,,Dana dauki abun da sauqi yanzu Ko magane shayi ruwane,,
Nasir adaidai lokacin da aka dauramin aure Sai gashi a lokacin iyayena da ‘yan uwana sukesan rabani da wannan gari Nasir yaya zanyi..
Haba mashkur Kamar yaya, meyasa Zaka kayawa mummy wannan aure Bayan kasan halin mummy” cikin faduwar gaba mashkur yace.
Ban gayamata ba Nasir kafi kowa sanin yadda mummy take Sona take kaunata,,Na tabbata inda mutuwa zata zo daukana mummy zata Iya fansar Raina da nata” Amma kaga mummy tadau zafi Dani harta Kira manyan yayyena ta gayamusu..
Nasir Bani da yadda zanyi,,yazama Dole a Yau Dinan nabar garin nan indai inasan zaman lafiya.
What! Mashkur me kake nufi,,yaya zakayi da nijlah??
Nasir Zan dauki matata,da ita Zan tafi,,Iya wuya Ina tare da ita..
Niko Nace Kamar yadda muke Kenan lolxx….
Kudaure kuna sharing labarinan, Domin wasu su amfana.
Comments & share.
*Momn sultan ce*
???????? *’YAR SADAKA..*????????
*STORY & WRITING BY…*
*BY*
*MOMN SULTAN*
*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH*
*SPECIAL GIFT TO…*
*N@DI@*
&
Wayyo Allah,,yau Naga ta kaina yanzu mezan Gaya iyayen yarinyarnan,,zagaye titi Bello ya riqayi Yana kallan Motan har Saida suka bacewa ganinsa kafin ya daga qafa yaname danasanin amincewa da rakiyan nijlah..
Yanzu mezan Gaya Kaka,,wanne dalili nake dashi Wanda ze tabbatar musu da maganata gaskiya ce,,sosai ya zurfafa cikin tunani Yana tafiya Yana hada hanya a haka harya Kai kauyen kankan,Yana zuwa dakin Nasir ya Shiga nan ya Samu Nasir ya zuba tagumi Yana tinanin rayuwar kadaicin dazeyi a wannan kauye Shi Daya ba abokinsa..
Ko sallama Bello beba yafara da masifa,,Kai Ashe wannan abokin naka bashida kunya,,miskilancin banza yakewa mutane”” dagowa Nasir yayi Yana kallan Bello da jajayen idanunsa yace” lafiya Bello,,Naganka anan?
To a ina zaka ganni Saida muka Shiga mota abokinka ya hankadoni waje,,yace wai ba inda Zan bishi daga Shi sai matarsa zasu tafi,,yanzu me kake tsammanin yakumbo ya dauka,,ni wallahi harna Fara tinanin mashkur Dan yankan Kaine..