YAU DA GOBE 11-12

Inya kamata na sanin”very soon Zaki sani”yafad’a Yana cewa yanzun kirufe idonki zamiki albishir”tana murmushi ta rufe idonta…ledar dake hannunsa yabude yaciro kwalin waya torch screen ya ajiye Mata kan cinya”Yana murmushi yace ta bud’e idonta”tana budewa idanunta suka hasko Mata kwalin wayar”wow ! tafad’a cikin murmushi tana d’aukar kwalin wayar”tace Yaya wannan dalleliyar wayarfa?”yanata aikin kallon ta yace takice sumy”banajin dad’in ganinki da baby Nokia”su jidda nacanzama wa ,shine nasiyo dake…sosai cikin yaba wayar tamasa godiya da adduar samun bud’i na alkhairi..Yana murmushi yace ameen my sumy godiyar tayi yawa”sai ayita chats ko?”Amma banson ganin contact din kowane k’ato ,kina jina?”eh Yaya zankiyaye”sallama yamata ya wuce cikin gd”sumayya cike da d’oki ta kwashe kayanta ta nufi part d’insu d amurnarta….
a bed room d’in maman tasameta zaune tayi tagumi”ga hawaye Shar afuskarta na zuba! cikeda tsoro sumayya tasaki kwalin wayar ta duk’a gaban mama “cikin tashin hankali tace lfy mama meke damun ki,anmiki wani abu???”girgiza Kai kawai maman tayi tana share hawayenta “had’e da yiwa sumayya kallon tausayi…tace bbu abinda akamun sumayya!dangin mahaifinki kesan jefa rayuwarmu acikin tashin hankali konace fitina”Inna lillahi wa inna ilaihir raju’un”mama kisanar Dani Dan ALLAH”ajiyar zuciya mama tayi had’e da cewa”kinsan kwanaki nace Miki kafin na auri alh naga aminu akasuwa,yazo garin nan neman kud’i.”(dan baffa habibu yayan baban sumayya) ya amshi number ta”Wai arik’a gaisawa”tunda ya amshi number d’in sau d’aya muka gaisa da binta mamansa “shine Wai yanzun takirani take shaidamun Wai baffanki habibu zaizo nan Kano ackin satin nan yakarb’eki “zai aurawa muttala ke…nasan itama bintar badan Allah tasanarmunba tasanar mun ne tunda muttala d’an kishiyarta ne”da ita ta haifesa bazata fad’a ba”damuwata sumayya muttala ba d’an arziki bane”sannan tun kina Yar shekara 12 babanki yarasu shekara8 kenan da mutuwarsa”ko sau d’aya aasu tab’a kamiki wani abu naci ko Sha ko sutura, ko abinda yashafi karatunki da lafiyarki”sai yanzun za’a ce Wai za’a hadaki aure da muttala! Sbd ya lalace sai sace sace da shaye shaye”abata Miki rayuwa sbd suna dangin mahaifinki…wlh Ina hakuri da kauda Kai akan abinda sukemun amma wlh wannan karon zanbasu mamaki ko sama da k’asa zasu had’u bbu Wanda ya isa ya karbeki ko Miki auren dole matukar Ina Raye…fashewa da kuka sumayya tayi sbd tasan halin waye muttala”cikin kuka tace Dan ALLAH mama kije gdn baba Iliya kisanar Masa “adauki mataki kafin suzo tunda ance asatin nan zasuzo….bazataje ko inaba sumayya!nine nan zan d’auki mataki amatsayina na ubah agareki”da sauri mama da sumayya suka kalli bakin k’ofa”Abba ne tsaye Yana sauraron tattaunawar su”yashigo yacewa mama yadawo yasamesu suna mgn…Ida shigowa d’akin yyi ya zauna gefen mama yace! sumayya ki kwantar da hankalinki”bazaki auri kowaba sai mijin dana zab’a Miki”inhar sunzo zancemusu da saka ranar wani akanki”insun Musa har kotu Zan ce Zan kaisu “sbd sune matsayin iyayen ki” amma tsawon shekara8 bbu wata kulawa ko damuwa dasukayi da rayuwar ki, sannan Rana tsaka suce Zaki auri wani,.waninma Kuma lalatacce…Maryam karku damu kubar komai ahannuna” tashi kije sumayya… ajiyar zuciya sumayya tayi had’e da d’aukar kwalin wayar ta ta fice…
Abba yakalli mama” ahankali yace Kinga banisan kina saka damuwa aranki”bacin bake d’aya bace ko?”share hawayenki banasan ganinsu insha Allah kingama zubbada hawaye akan mutanan na”ninasan maganinsu Allah yasa suzo…ajiyar zuciya mama tayi tace shikenan alh nagode k’warai da…..inkinamun godiya kin nuna banina haifi sumayya ba ko?”ah ah alh yanzun sumayya batada mahaifin daya wuce Kai”yace alhmdllh kin bani damar zab’awa sumayya mijin daya dace da ita?” Mama tace k’warai kuwa sbd nasan bazaka Mata zab’en tumun dareba…Abba yace Masha Allah!tashi muje nayi wanka”mama tace to suka fice atare…
#######
Da safe Gurin karfe8 da rabi”musty ne zaune Yana break fast ga trolley dinsa agefensa”ummi da zarah nagefensa!kallo d’aya zakama zarah kasan tana cikin damuwa”musty ya ajiye cup d’in hannunsa yamik’e tsaye Yana cewa ummi”ban sanar mikiba tare da Yasmeen zamuje”kinsan itama can aka mik’ata “ummi tace Allah sarki”nikuwa banison mace tayi nisa,shiyasa gara zarah tayi nata anan kusa d gida”
Wani dummm zarah taji sbd jin sunan Yasmeen abakin musty Kuma tare zasuje”dama tasan Yasmeen na mugun son musty”shine ke be kulata…tsintar kanta tayi dajin haushin Yasmeen d’in”ga gabanta nata fad’uwa…ummi muje kimun addua,nabiya ta gdnsu na d’auketa” muryar musty takatse ma ta tunaninta”saidai musty yyi mugun bata mamakin akan be Mata sallama ba zai tafi”zuciyar ta nasanar Mata ,yaza ai yadamu dake bacin kince bakya sonsa”bata ankaraba taga bbu ummi da musty a parlourn”gyalenta ta gyara ta fito zuwa haraban gdn”tahango driver nasaka trolley dinsa aboot”ummi suna mgn da musty…jikinta asanyaye ta Ida isowa”adedenan ummi tabar Gurin byn sungama sallama da musty…musty kuwa ajiyar zuciya yasaki aboye”sbd daurewa kawai yyi yaga zatazo masa sallama shiyasa be Mata mgn dazunba”niyarsa in bata zoba inya Isa yakirata ta waya…ko maganar Yasmeen k’aryane duk Yana cikin plan ne kozai gane tafara sonsa..cikin rauni murya zarah tace broth nagode sosai akan irin abinda kakemun “yanzun inbanzoba bazakamun sallama ba??”yanxun bagashi kinxo muyiba” yafad’a atakaice yanata latsa wayarsa”cikin b’acin Rai zarah tace ohk tunda bata tawa kakeba bara natafi”sbd wata banza Ina mgn zaka share kana latsa waya?”in har kanso ka burgeni ku tabbata acan kaida ita..baby meyayi zafi?”wacece kike nufi?”harara ta galla mishi ta juya tayi tafiyarta”shikuwa wani tsalle yyi yabude motar yashige Yana fad’in yesssss! wlh… driver yaja suka bar gdn…
Zarah kuwa rasa meke Mata dad’i tayi…saikawai tasaka kuka tamkar k’aramar yarinya”ta shigo parlourn”ummi ta dubeta tace lfy xarah”yanzun ummi saikibar broth suje tare da Yasmeen bacin ba maharamar bace…sbd zasuje tare kike hawaye kome?”nifa ba haka bane wata kawata ce tarasu aka kirani yanzun ta waya.. murmushi ummi tayi sbd tsab tagano zarah “ta girgiza Kai batace komaiba..
Abba yadubi Sadiq dake zaune gabansa yace katabbata itama sumayyar tana sonka?”uhmmm Abba”Abba yace to inda ban kiraka natambayeka waka fitar bazaka gayamun ba?”ah ah Abba Zan sanar maka ai…ok jeka zanyi nazari akan maganar….tashi Sadiq yyi Yana murmushi,gefe guda Kuma na zuciyar na fargaba in mahaifiyar’sa taji yace sumayya yakeso…
Byn fitar Sadiq saiga hjy jamilah ta shigo da tray na da kayan abinci ke akai, kasancewar itace da girki”murmushi Abba yyi yace zauna zamuyi mgn”
Tab’e baki tayi had’e da cewa Allah yasa maganar bata shafi mutanan cikin gdn ba”beyi mamakin furucintaba”yyi gyaran murya had’e da cewa”amatsayina na ubah ga Sadiq nabashi lokaci yafitar da wacce yakeso be fitarba”har lokacin ya wuce nazab’a Masa matar dazai aura amatsayina na mahaifin sa”Kuma dole yamun biyayya…hakane Alh!amma wacece matar daka zab’a mishi?
abba ya girgiza Kai yace SUMAYYA wacce kika sani !y’ar Maryam wacce kike Kira da agola…????????????????