???????????????????????????????????? ????YAU DA GOBE ???? ???????????????????????????????????????? Story & writing by mmn fareesa ????️11&12 ......Cike da mamaki Dr safana ke kallon musty dake kwance kan bed Yana kallon duka "wad'an da kecikin d'akin"azuciyar sa yace kodai mafarki yakeyi ne?"amma yanzun...baby do you love me?"muryar musty takatse ma safana tunani"baby tasaki kuka had'e ga girgiza Kai" tace ba irin son dakakeso ba nakema inamaka SO na y'an uwan taka...tsaki Dr safana yaja had'e da cewa bamasan shirme da shiririta"inzakuyi bayani kuyi bawai kuyita mgn azaurance ba"ummi kuwa d'ukar da kanta k'asa tayi tana tunanin abinda take gudu yafaru kenan...ummi!Dr safana yakira sunanta"babana ya akayi?"cewar ummin tana kallonsa.ahankali yace abashi abinci yasha da magani"musty yakarbe zancen da cewa abinci d magani bashine damuwata ba Yaya... tab'e Baki Dr safana yyi had'e da cewa kabani mamaki wlh dazaka kwanta ciwo sbd mace"ciwon zaisaka tasoka?"bazaka nemi soyayya agunta ba?dajan ra'ayinta har wata Rana YAU DA GOBE tasoka"bazaka ganeba Yaya"cewar musty awahale"ai dama bana buk'atar nagane d'in"yafad'a Yana hararar zarah had'e da cewa kekuma kizauna sbd ke har yakwanta asibiti"meye yasa bazaki soshiba?"shagwabe fuska zarah tayi had'e da cewa K'ANINA fane Yaya"tsaki Dr safana yyi had'e da cewa so what?"ink'anin kine,kokuwa haramun ne?"cikin tura Baki zarah tace ah ah"yatsina fuska Dr safana yyi yace kuka sani can ta matse muku"inkunshirya fine akasin hakanma fine...bejira cewarta suba yafice...ummi kuwa had'e Rai tayi had'e da ajiye plate din abinci d cup din tea Mai kauri yana turiri"kusada musty tace maza tashi kaci kasha magani" tafad'a fuska a'daure"kafin ta harari zarah tace wuce kije driver yamayar dake gd" musty tamkar yyi kuka haka yayita kallon zarah" yanason su had'a ido tak'i yarda harta fice,ummi ta dubesa tace inada babban dalili Mai k'arfi Wanda nasan duk Daren dad'ewa YAU DA GOBE wata rana gsky zatayi halinta"auta kayi hakuri da zarah ko kayi k'ok'arin saka soyayyarka aranta"inrabon kace ka aureta"amma banaso ka aureta kaikad'ai kesonta"kasan dalilina na hakan?"jikinsa asanyaye yace ah ah ummi"tace dalilin farko bazan fad'a ba"YAU DA GOBE zaka sani"dalili na 2.shine bazakaji dad'in Zama da itaba tunda tasan kaike sonta, sannan bazata maka biyayya ba sbd tana ganin ta girmeka"kaga kuwa zaman aure ahaka be yuyuwa"nasan agd zarah namaka biyayya"Amma yanzun tunda kace kana sonta "wannan biyayyar ta rushe tunda kaike sonta"kakuma daure ka rarrashi kanka"kadage da addua da neman zab'in alkhairi inzarah rabonkace zaka sameta"amma saka tunani da damuwa aranka" bashi bane mafita ba... musammun kwanciya ciwon dakayi...ajiyar zuciya musty yasauke cike da gamsuwa da mamakin k'aifin hankali irin na ummi... lallai duk Wanda yaraina mace besan abinda yakeyi ba" ahankali yace ummi naji shawarar ki,nakuma d'auka"nagode Ina alfahari dake amatsayin uwa ta gari agareni"yafad'a azuciyar sa yasha alwashin cusa soyayyarsa azuciyar zarah...cikin sakin jiki yasha tea da abinci harda magani...ummi ta kara masa pillow jikin bango yajingina suna fira.. tamkar bashine d'azun magashiyan ba.... Dr safana kuwa cike da jin haushin musty yanufi office d'in Dr Nasir"yasa meshi yagama duba patient Yana hutawa ,suna waya da Mina matarsa"Zama Dr safana yyi had'e da cewa mlm koka kashe wayar Kona fice"Kuna bani mamaki wlh"ace Koda wane time Kuna wahalar dakanku da soyayya... murmushi Dr Nasir yyi yace me yafi ranmu?"yafad'a Yana kashe wayar byn yamata sallama! Yadora d fad'in safana kenan"wacce kuke soyayya Baku daceba d juna ,shiyasa kake ganin bata time ne soyayya"Ina rok'on Allah yasa kaso wata son dabanyi tunaniba....tsaki Dr safana yyi yace d'an iska kawai narasa me my rukky takashe maka "azahiri kake nuna bakason na aureta...hmmm yanzun yamai jiki?"wani tsakin yakoma ja"had'e da labartawa Dr Nasir halin da musty yake...Dr Nasir yace kamasa uzuri abokina"bazaka gane ba sai hakan yazo kanka" Harararsa yyi yace Allah yatsareni...yauwa Dan Allah Wai me yahad'a ka da yarinyar nan sumayya?"atake Dr safana yahad'e rai..yatashi tsaye yace kaga mlm inkana maganr mutane dena sakota"nalura bakason zamana a office naka ko?"to sai anjima"dariya Dr Nasir yakece da ita"afili yace ohni Nasir safana anya zaka canza?"hmmm mace kawai zata canzaka "irinku inkuka fad'a tarkon SO Baku iyaba wlh... ???????????????????????? Jikin musty da sauk'i bbu laifi"kafin magrib aka bashi sallama suka wuce gd.ummi kawai tashiga cikin gdn"musty da Yaya Aliyu part nasu suka wuce" Zarah na zaune tayi tagumi "tana tunanin koyaya jikin musty?"zamanta kenan bayan tagama abincin dare"kasan cewar bataje islamiyar marece ba"da safema bataje skul ba"ahakan ummi tashigo tasameta,ko amsa sallamar ummi batayiba,ta Mike zunbur had'e da cewa ummi yajikin broth ?"Yana inane?"da mamaki ummi keta kallon ta"kafin tace Yana d'akinsu an sallameshi...ajiyar zuciya zarah tayi Takoma ta zauna , yyinda ummi t shige bed room d'in ta.. ************** Hakafa rayuwar gdnsu Dr safana tacigaba da tafiya"tsakanin zarah d musty mgn saita Kama"har kulawar dayake Bata askul ko agd yadena"da bautar siya Mata wannan da wannan dayakeyi ada duk yadena"besakar Mata fuska "mgn saita Kama yake Mata ita"hakan yyi mugun d'aga hankalin zarah "Kai hatta keys din d'akinsa dake hannunta tana gyara Masa dak'i duk ya amshe"sakata tadafa mishi kaza da kaza duk yadena"sannan zai iya shigowa agdn yyita fira da ummi ko kallo bata ishe shiba"babban damuwarta shine wannan week din zaitafi kaduna service"itakuma anan Kano Yaya Aliyu yasa marmata... kasancewar sunkusa degree"kusan wata 3 kenan suna wannan takun sakar"Wanda musty daurewa kawai yakeyi"amma sonta Yana nan daram aransa" """"Bangaren su sumayya kuwa "mamanta na nan da tsohon ciki"yyinda sumayya tashak'u da Yaya Sadiq sosai"Gefe guda Kuma Yana nuna Mata soyayyarsa"saidai tak'i nuna tagane sbd tsoron hjy jamilah mahaifiyar'sa"Abba kuwa yagama gano Sadiq son sumayya yakeyi"musammun akan yawan zaryar da Sadiq d'in keyi part d'in mama dakuma yawan ganinsa tare da sumayyar dayakeyi"wata Rana ma"shike kaita skul"sumayya nason sanarma Sadiq akan matsawar da hamsahak'i kemata tana tsoro aganinta karta zak'e !amatsayinta na agola"hjy jamilah kuwa bata canzaba saima k'aruwa abinta yyi sbd ganin mama da ciki "hankalinta yasake tashi"gefe guda Kuma sai cusa jidda akeyi ga Dr safana shikuma Yana basarwa"har gidn su jidda kezuwa amatsayin takaimusu ziyarar zumunci...bacin gaisuwa besakar Mata fuskar yin wata mgn...sadai hjy jamilah taci alwashin ko Abba Tama mgn "akan yabawa Dr safana umarnin ya auri jidda... Kamar kullum indai alhamis ne ko jumma'a"sumayya na lanbun gdn tana duba books nata"zaune take kan plastic chair..sanye take da pink &white na lace riga da siket da hijab pink iya gwiwa"fuskarta da light make up"kanta bbu d'an kwali tayi acuci da gashinta"tana duba hand out"k'amshin turaren sa yadaki hancinta"ta d'ago kanta da sauri,suka had'a ido"shagwabe fuska tayi had'e da cewa shine ka tsoratani? tattausan murmushi yyi had'e Jan kujera guda yazauna Yana fuskantarta"ahankali yace sorry my sumy banyi zaton Zaki tsorataba...hmmm kawai tace tana cigaba da abinda takeyi...muskutawa yyi murya can k'asa yace SUMAYYA! Inaso kibani shawara!ajiye hand out d'in tayi jin yakirata bbu wasa afuskarsa"ahankali tace inajinka Yaya"tafad'a batare data kallesa ba and batasan yawan had'a ido dashi...Abba yabani 3 month nafito da wacce nakeso"gashi lokaci yyi amma ban fitarba....meye shawara?"to Yaya dama bakada budurwane?"eh sumy"meyasa to?"da yawan matan sun Zama abin tsoro"amma kinsan akwai wacce nikeso"amma bansanar mataba"murmushi tayi had'e d'agowa ta dubesa tace wacece?"yace hmmm Kumafa nasan abba zaiyi farin ciki dajin hakan.uhumm kawai tace"murmushi yyi yamik'e tsaye yace kinason sanin ko wacece "ahankali tace eh" Inya kamata na sanin"very soon Zaki sani"yafad'a Yana cewa yanzun kirufe idonki zamiki albishir"tana murmushi ta rufe idonta...ledar dake hannunsa yabude yaciro kwalin waya torch screen ya ajiye Mata kan cinya"Yana murmushi yace ta bud'e idonta"tana budewa idanunta suka hasko Mata kwalin wayar"wow ! tafad'a cikin murmushi tana d'aukar kwalin wayar"tace Yaya wannan dalleliyar wayarfa?"yanata aikin kallon ta yace takice sumy"banajin dad'in ganinki da baby Nokia"su jidda nacanzama wa ,shine nasiyo dake...sosai cikin yaba wayar tamasa godiya da adduar samun bud'i na alkhairi..Yana murmushi yace ameen my sumy godiyar tayi yawa"sai ayita chats ko?"Amma banson ganin contact din kowane k'ato ,kina jina?"eh Yaya zankiyaye"sallama yamata ya wuce cikin gd"sumayya cike da d'oki ta kwashe kayanta ta nufi part d'insu d amurnarta.... a bed room d'in maman tasameta zaune tayi tagumi"ga hawaye Shar afuskarta na zuba! cikeda tsoro sumayya tasaki kwalin wayar ta duk'a gaban mama "cikin tashin hankali tace lfy mama meke damun ki,anmiki wani abu???"girgiza Kai kawai maman tayi tana share hawayenta "had'e da yiwa sumayya kallon tausayi...tace bbu abinda akamun sumayya!dangin mahaifinki kesan jefa rayuwarmu acikin tashin hankali konace fitina"Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un"mama kisanar Dani Dan ALLAH"ajiyar zuciya mama tayi had'e da cewa"kinsan kwanaki nace Miki kafin na auri alh naga aminu akasuwa,yazo garin nan neman kud'i."(dan baffa habibu yayan baban sumayya) ya amshi number ta"Wai arik'a gaisawa"tunda ya amshi number d'in sau d'aya muka gaisa da binta mamansa "shine Wai yanzun takirani take shaidamun Wai baffanki habibu zaizo nan Kano ackin satin nan yakarb'eki "zai aurawa muttala ke...nasan itama bintar badan Allah tasanarmunba tasanar mun ne tunda muttala d'an kishiyarta ne"da ita ta haifesa bazata fad'a ba"damuwata sumayya muttala ba d'an arziki bane"sannan tun kina Yar shekara 12 babanki yarasu shekara8 kenan da mutuwarsa"ko sau d'aya aasu tab'a kamiki wani abu naci ko Sha ko sutura, ko abinda yashafi karatunki da lafiyarki"sai yanzun za'a ce Wai za'a hadaki aure da muttala! Sbd ya lalace sai sace sace da shaye shaye"abata Miki rayuwa sbd suna dangin mahaifinki...wlh Ina hakuri da kauda Kai akan abinda sukemun amma wlh wannan karon zanbasu mamaki ko sama da k'asa zasu had'u bbu Wanda ya isa ya karbeki ko Miki auren dole matukar Ina Raye...fashewa da kuka sumayya tayi sbd tasan halin waye muttala"cikin kuka tace Dan ALLAH mama kije gdn baba Iliya kisanar Masa "adauki mataki kafin suzo tunda ance asatin nan zasuzo....bazataje ko inaba sumayya!nine nan zan d'auki mataki amatsayina na ubah agareki"da sauri mama da sumayya suka kalli bakin k'ofa"Abba ne tsaye Yana sauraron tattaunawar su"yashigo yacewa mama yadawo yasamesu suna mgn...Ida shigowa d'akin yyi ya zauna gefen mama yace! sumayya ki kwantar da hankalinki"bazaki auri kowaba sai mijin dana zab'a Miki"inhar sunzo zancemusu da saka ranar wani akanki"insun Musa har kotu Zan ce Zan kaisu "sbd sune matsayin iyayen ki" amma tsawon shekara8 bbu wata kulawa ko damuwa dasukayi da rayuwar ki, sannan Rana tsaka suce Zaki auri wani,.waninma Kuma lalatacce...Maryam karku damu kubar komai ahannuna" tashi kije sumayya... ajiyar zuciya sumayya tayi had'e da d'aukar kwalin wayar ta ta fice... Abba yakalli mama" ahankali yace Kinga banisan kina saka damuwa aranki"bacin bake d'aya bace ko?"share hawayenki banasan ganinsu insha Allah kingama zubbada hawaye akan mutanan na"ninasan maganinsu Allah yasa suzo...ajiyar zuciya mama tayi tace shikenan alh nagode k'warai da.....inkinamun godiya kin nuna banina haifi sumayya ba ko?"ah ah alh yanzun sumayya batada mahaifin daya wuce Kai"yace alhmdllh kin bani damar zab'awa sumayya mijin daya dace da ita?" Mama tace k'warai kuwa sbd nasan bazaka Mata zab'en tumun dareba...Abba yace Masha Allah!tashi muje nayi wanka"mama tace to suka fice atare... ####### Da safe Gurin karfe8 da rabi"musty ne zaune Yana break fast ga trolley dinsa agefensa"ummi da zarah nagefensa!kallo d'aya zakama zarah kasan tana cikin damuwa"musty ya ajiye cup d'in hannunsa yamik'e tsaye Yana cewa ummi"ban sanar mikiba tare da Yasmeen zamuje"kinsan itama can aka mik'ata "ummi tace Allah sarki"nikuwa banison mace tayi nisa,shiyasa gara zarah tayi nata anan kusa d gida" Wani dummm zarah taji sbd jin sunan Yasmeen abakin musty Kuma tare zasuje"dama tasan Yasmeen na mugun son musty"shine ke be kulata...tsintar kanta tayi dajin haushin Yasmeen d'in"ga gabanta nata fad'uwa...ummi muje kimun addua,nabiya ta gdnsu na d'auketa" muryar musty takatse ma ta tunaninta"saidai musty yyi mugun bata mamakin akan be Mata sallama ba zai tafi"zuciyar ta nasanar Mata ,yaza ai yadamu dake bacin kince bakya sonsa"bata ankaraba taga bbu ummi da musty a parlourn"gyalenta ta gyara ta fito zuwa haraban gdn"tahango driver nasaka trolley dinsa aboot"ummi suna mgn da musty...jikinta asanyaye ta Ida isowa"adedenan ummi tabar Gurin byn sungama sallama da musty...musty kuwa ajiyar zuciya yasaki aboye"sbd daurewa kawai yyi yaga zatazo masa sallama shiyasa be Mata mgn dazunba"niyarsa in bata zoba inya Isa yakirata ta waya...ko maganar Yasmeen k'aryane duk Yana cikin plan ne kozai gane tafara sonsa..cikin rauni murya zarah tace broth nagode sosai akan irin abinda kakemun "yanzun inbanzoba bazakamun sallama ba??"yanxun bagashi kinxo muyiba" yafad'a atakaice yanata latsa wayarsa"cikin b'acin Rai zarah tace ohk tunda bata tawa kakeba bara natafi"sbd wata banza Ina mgn zaka share kana latsa waya?"in har kanso ka burgeni ku tabbata acan kaida ita..baby meyayi zafi?"wacece kike nufi?"harara ta galla mishi ta juya tayi tafiyarta"shikuwa wani tsalle yyi yabude motar yashige Yana fad'in yesssss! wlh... driver yaja suka bar gdn... Zarah kuwa rasa meke Mata dad'i tayi...saikawai tasaka kuka tamkar k'aramar yarinya"ta shigo parlourn"ummi ta dubeta tace lfy xarah"yanzun ummi saikibar broth suje tare da Yasmeen bacin ba maharamar bace...sbd zasuje tare kike hawaye kome?"nifa ba haka bane wata kawata ce tarasu aka kirani yanzun ta waya.. murmushi ummi tayi sbd tsab tagano zarah "ta girgiza Kai batace komaiba.. Abba yadubi Sadiq dake zaune gabansa yace katabbata itama sumayyar tana sonka?"uhmmm Abba"Abba yace to inda ban kiraka natambayeka waka fitar bazaka gayamun ba?"ah ah Abba Zan sanar maka ai...ok jeka zanyi nazari akan maganar....tashi Sadiq yyi Yana murmushi,gefe guda Kuma na zuciyar na fargaba in mahaifiyar'sa taji yace sumayya yakeso... Byn fitar Sadiq saiga hjy jamilah ta shigo da tray na da kayan abinci ke akai, kasancewar itace da girki"murmushi Abba yyi yace zauna zamuyi mgn" Tab'e baki tayi had'e da cewa Allah yasa maganar bata shafi mutanan cikin gdn ba"beyi mamakin furucintaba"yyi gyaran murya had'e da cewa"amatsayina na ubah ga Sadiq nabashi lokaci yafitar da wacce yakeso be fitarba"har lokacin ya wuce nazab'a Masa matar dazai aura amatsayina na mahaifin sa"Kuma dole yamun biyayya...hakane Alh!amma wacece matar daka zab'a mishi? abba ya girgiza Kai yace SUMAYYA wacce kika sani !y'ar Maryam wacce kike Kira da agola...???????????????? next page na team din Sadiq ne sai ku fito akafta..????????♀️ Share By mmn fareesa ????️