NOVELSUncategorized

YAU DA GOBE 2&3

 ????????????????????????????????????

  ????YAU DA GOBE ????

????????????????????????????????????????

Story & writing by mmn fareesa

????️3&4

Sunana Sumayya Ahmed batsari!mahaifina d’an jihar batsarine dake hukumar katsina da mahaifiya ta Maryam.

   Mamana marainiya ce iyayenta sun mutu “byn aurensu da babana”dangin mahaifinta wasunsu suka dawo Kano da Zama sbd neman kud’i “Amma dangin mahaifiyarta suna nan abatsari”

   Mlm Ahmed su 3 me Gurin iyayen su’ habibu,Ahmed sai hayatu…gaba d’ayansu babana yafisu rufin asiri da abin hannu”yanama mamana abubuwa da yawa na YAU DA GOBE… Tun kafin ahaifeni har aka haifeni”hakan yasa kishin saurinta jin zafinta da Inna kakata”..babana Yana ji Dani Yana kulawa Dani “Ina y’ar shekara5 mamana tasake haihuwar nmj bbu rai dg nan batasake haihuwa ba”nan dangin miji suka saka agaba da k’ananun maganganu… yyinda babana hakan be dameshiba”ahaka natasa aka sani nursery skul & primary….ahaka natasa har naje js..

Kwatsam babana wata Rana ana ruwan sama da dare…duk Muna a parlourn mu matsakaici na me rufin asiri”sai babana yafito zai shiga bayi”akayi walk’iya…kawai yaga wani Abu Mai haske saikace Rana dukda darene”da sauri yanufi abun…yadauka yanata dubawa”can ya ajiye ya wuce bayi”byn yafito yadauka yashigo dashi parlour”da sauri nida mama mukace meye wannan abun daketa walk’iya haka?”baba yace wlh innace ga kominene nayi karya ,yanzun akayi walk’iya naganshi atsakar gd..

    Da sauri na karb’a Ina dubawa…zaro ido nayi…nace wlh baba wannan gold ne d’anye….nabuga tsalle nace wlh Allah yabaka muma munyi arziki…cike da mamaki babana da mamana sukayita duba’abun suna al’ajabi har  washe gari”

Baba yaje gun Inna da y’an uwansa yanuna musu”sunyi murna sbd aganinsu suma sunyi arziki….acikin kwana2 garin duk kowa yasan abinda babana yasamu”baffa habibu da baffa hayatu “sun Sami babana akan yabasu gold d’in sukai birni “asiyar sai yyi amfani da kudin”yace ah ah sai yyi shawara…hakan kuwa yab’ata musu Rai sosai”kwana 10 da faruwar hakan “cikin dare barayi suka shigo gdnmu”suka nemi babana yabasu gold” yafad’a  musu baya hannunsa…sukayi binkice Basu ganiba”haka agabanmu suka yiwa babana kisan gillah”duk rok’on da mukayi musu…ba k’aramin tashin hankali muka shigaba”nida mamana” byn fitarsu muna kuka Yana cikin jini Yana kakarin mutuwa”yakalli mamana yarik’e Mata hannu yace duk rintsi karki rabu da sumayya inba aure ba zairabaku…. sannan gold na damk’a amanarsa awurin wani mutum”insha ALLAH YAU DA GOBE wata Rana mutumin zaizo yak….iyanan maganarsa tatsaya Yana tari….mamana namaimaita Masa kalmar shahada ya amsa atake Rai yyi halinsa.. dangin mahaifina basuyi wani binkiceba akan mutuwar babana”wani abun tashin hankali byn sadakar 40 saiga wasu mutane dg birni Wai suna bin babana bashi kud’i million d’aya da dubu dari 2″bbu wani binkice dangin babana suka siyar da gdnmu da gonar babana da shanunsa suka biya Masa bashi acewarsu….munshiga k’uncin rayuwa da bakin ciki” inda zamu zauna yagagaremu d abinci nida mamana” byn ansiyar d gdnmu gdn Inna kakata muka koma har mamana tagama * takaba*

Su baffa hayatu bbu kunya bbu tsoron Allah sukace to maryam sai ki koma gun y’an uwanki ki zauna kirik’e y’arki sbd alokacin da mijinki keda rai duk abinda yasamu dg ke sai y’arki yasani sbd haka saiku k’arata…Mamana batace komaiba “ta kwashe Mana kayanmu muka koma gdn kawunta aminu k’anin mamanta ana batsarin…saidai canma duk kanwar Jace”Basu bamu abinci da komai “inbacin dak’i1dasuka bamu muka zuba kayanmu”nan mamana tarik’a yin wankau Ina tayata”da kitso na kud’i ana biyanta da hakan muke rufawa kanmu asiri”Amma dukda hakan matan  kawu aminu sai tsangwama da kyara atsakaninmu”abokin babana baba salisu shine yacigaba da d’aukar nauyin karatuna Dana bokon da islamiyar “har nayi J S C E nayi saukar alk’ur’ani Mai girma…

Gefe guda Kuma zawarawa nata fitowa neman aurenmamana Amma tace ita aure baya gabanta..kwatsam kawu aminu yarasu “dole bayan wasu kwanaki muka kwashe kayanmu muka dawo Kano da Zama gdn yayan baban mahaifiyata”


Zaman mu a janbulo Kano “Acan ma dai kusan hakanne Amma suna bamu abinci sauran abubuwa ne mukeyi da kanmmu”mamana  tarik’a yin abincin siyarwa “da wannan sana’ar aka sakani skul naje SS1…Masha Allah alhmdllh haka muke zaune gdn baba Iliya da dad’i babu dad’i …YAU DA GOBE sai Allah har nashiga nashiga ss3 “alokacin Kuma duk wani girma da kyawu yagama bayyana ajikina..bana kula kowane saurayi acikin masu cewa suna Sona ko askul ma haka…sbd mama ta gargadeni da nayi abinda yakaini…k’awata guda sameerah wacce class namu d’aya sit d’aya da ita”munshak’u sosai da ita “ada bani sakin jiki da ita amma dg baya Dana karanci halayenta masu kyaune sai muka Zama aminan juna…mamana tayi gwanin kyau sbd munacin me kyau ga Kuma kwanciyar hankali”tunda mukadawo Kano ko sau d’aya bamu tab’a zuwa batsariba” kosu suzo dasunan sunxo ganina..amatsayinsu na dangin babana…. 
wata rana nadawo dg skul” nasami Inna mariya! matar baba Iliya tayi tagumi  cikin damuwa…nace lfy Inna? Tace yuwa sumayya mmnki bbu lfy ! Ke nake jira muje akaita asibiti…hawaye suka zubomin sbd kusan kwanan mama3 bbu lfy ko abinci tadainayi…dak’inmu na shiga na sameta kwance namata sannu’ kafin nacanza Kaya nayi Sallar azahar ” nace mama Dan ALLAH muje asibiti” murmushin karfin hali tayi tace ah ah sumayya” nasami sauk’i sosai ai” haba Maryam wlh gara kibita kuje asibitin nan inma bakida kud’i saina ara Miki…cewar Inna mariya” da sauri nace eh Inna…


     Koda muka isa asibitin” nace ta zauna naje yankar kati…nasami wani babban mutum tsaye sai kallona yake hakan yasa nagaidashi”ya amsa ,inaji suna mgn har suka Gama mgn da wani ya juya yatafi…nikuma nabiya kud’in Kati…sainaji ance ke yarinya tare kuke da waccen matar?

    Da sauri najuyo naga mutumin yanxun nace eh cike da tsoro” Ina kallon gefen da mamana take naganta tafadi ta sume…da gudu na nufi gurinta”da taimakon  wannan mutum(alh Usman) aka Bata taimakon gaggawa suka bamu kwanciyya”Kuma duk wani abu shine yabiya…nadinga Masa godiya,ya tambayeni sunana na fad’a Masa”Saida aka bamu dak’i aka saka Mata drip tukum yatafi…da dare alokacin nakira Inna mariya nasanar maka anbamu gado”sannan nayi magrib da isha’i “alokacin mama ta farka Dan har ancire Mata drip d’in..nan nabata labarin taimakon da alhaji nan yamana”kafin tace wani Abu…anyi knocking d’in k’ofar nabada izinin ashigo saiga alh da wani mutum biye dashi da Kaya nik’i nik’i…sallama yyi “na amsa Ina gaidashi”cike da godiya akan d’awainiyarsa”mutumin ya ajiye kayan ya fice “nabawa alh kujera akan yazauna yace ah ah y’ata  zan wuce…ahankali mama tace Ina wuni”?d’agowa yyi yakalleta suka had’a ido”tai saurin kawar da kanta”yace lfy qlau ya karfin jikin?tace alhmdllh”munga d’awainiya mungode”amma dan ALLAH kayi hakuri akoma da wad’an nan kayan… murmushi yyi yace bewar Allah sbd Allah nayi badan komai ba”Kuma bani nufin komai”inhar kin yarda alhmdllh ku karb’a”nina wuce…anan nayi Masa godiya yafice..shiru mama tayi tana kallon kayan…abincine a cikin take aways da kayan tea da bread sai nama ga sasshe da sauransu …

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button