NOVELSUncategorized

KWARATA 92

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* ????
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



                       *KWARATA*
      _{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ ????????

*ASMA’U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

                         &

*RABI’ATU AMINU MAMMAN DEE*



???? —— 90



       Bayan na gama dubawa ajiye wayar nayi na nufi madafar abinci dan samawa cikina abinda zan bashi , ko uniform ina ban cire ba yunwa nakeji sosai kamar zan faɗi , Dikko kuwa bai wani daɗe ba yazo , kicin ya sameni wai gashi yazo ta ina zai fara kamfen in a yankin iyalin tashi , yayi maganar yana murmushi , dariya nayi sannan nace kaima sai kawai ka kama kayi wani tafiyar ka abunka , gaba ɗaya ka wani manta dani na ƙarasa maganar ina shiga jikinshi ,

        Dariya yayi cikin izza ya riƙe ƙuguna yace yi haƙuri An mata , naƙi inyi haƙurin , nine zahiri bakiyi ba tunda har kin faɗamin magana , wai na manta da yankin iyalina banyi kamfen ba , dariya kika bani nace tou ? ???? bari in rugo kar aƙi bani ƙuri’a ranar zaɓe , wannan “yar yarinya har tayi ƙorafi gaskiya Dikko bai kyauta ba. Ey mana inata jin babu daɗi na zama kamar wata marainiya dubeni da Allah duk na wani zama abin tausayi , na ƙarasa maganar a shagwaɓe ina kallon idonshi da yanayin kallon da yake so , murmushi yayi tare da lumshe idanuwanshi yace An mata……… Ya ƙarasa maganar yana sumbatar bakina.

     Fita nayi daga jikinshi na juya da niyar tafiya inda na ɗora girki , riƙo ƙuguna yayi ta baya yana jawoni jikinshi , ai ƙarya kikeyi bayan nazo kamfen , da Allah ka ƙyaleni yunwa nakeji , taɓe baki yayi tare da ɗaga gira yace , tou ? Ya faɗa cikin yanayin mamaki sannan yace , idan nayi tafiyata karki sake kirana kice inzo kamfen , tou ka tafi mana sai me…. ? Juyawa yayi yaɗanyi tafiya , inajin ƙarar takalmin shi , na juyo a dabarance naga shin da gaske tafiyar zaiyi , ina juyowa muka haɗa ido , dariya yayi tare da cewa yes ???????? , da baki juyo ba dana tsaya amma kinga tafiyata , da za’aimin yanga a wani latsani sai Allah ya kamaki nima saina rama , yana faɗin haka ya fita daga kicin in da sauri , kashe gas in nayi na bishi nima da sauri , ɗakinshi ya wuce yana dariyar mugunta.

       Lokacin dana shiga harya cire agogon hannunshi , da farin ciki ya rumgumeni wai oyoyo An mata , ya faɗa yana tsuke bakinshi tare da lumshe idanuwanshi yana ɗan kaɗa kanshi cikin yanayin shauƙin so , ya riƙeni sosai a jikinshi , murmushi yayi mai sauti ya sake maimaita wai kana can kana yawon kamfen ka manta da yankin iyalinka , kai An mata , tou ya akeyin kamfen a yankin iyali ya ƙarasa maganar yana haɗa idanuwanmu wuri ɗaya kowa yana kallon kowa , bayan wani lokaci yace caf aiko lallai nan ne ya kamata inyi kamfen muje a gama abincin inci nima in ƙara tsatsubo ƙarfina.

      Bayan mun koma ya zauna a saman matakalar da zaka shiga kicin yana yanka albarsa , da yaji azabar yaji yace kai ban iyawa anshi harna yanke , kawo dai in miki wani abun wannan wahala ji naji ciwo yana nunamin inda ya yanke tare da goge idonshi yace wai wahala , nidai albasar zaka yankamin , ke ban iyawa kinji , nima ban iyawa saidai a dafa abincin ba albarsa , ai yama fi daɗi yi sauri ki gama.

     Ciki ya shiga yana wanke hannunshi wayashi ta fara ringing , ni yasa na ciro mishi ita daga aljihu , dana faɗa masa Momy ce da sauri ya anshi wayar tare dayin sallama , bansan abinda Momy tace masa ba saidai yanayin idonshi ya canza zuwa launin ja , ya tsareni da kallo har naji tsoro ya kamani , gani nan zuwa ya faɗa tare da fita daga kicin in cikin tsananin ɓacin rai , ajiyar zuciya na sauke tare da cewa Allah ya tsare hanya , bai ansa ba ni kuma naci gaba da abinda ya shafeni.

       Hankalin kaf “yan ɗakinsu Dikko idan yayi dubu ya tashi har Momy gaba ɗayansu sun hallara a bedroom inta sai koke² sukeyi , wai Jiddah ta bawa Perpy fiya² a lemu , Dikko yayi tashin hankali shi ba kanshi yakeji ba An mata yake tausayi , yasan zata shiga damuwa duk da tana nuna kawaici da kara akan yaron amma ai tana san ɗanta kodan bata fito ta faɗa ba ? Yarinya mai kunya da kawaici waye ma zaiyi irin haƙurin da An mata tayi ? Idan da wata mara kunya ce aka ɗauki ɗanta ba uwar miji ba ko uwar waye sai anyi tashin hankali , Allah kaɗai yasan ciwon da takeji akan rashin Papi baya kusa da ita , amma bata taɓa faɗa ba bata kuma taɓa nunawa ba , koshi bata taɓa nuna mishi ba daɗi ba akan rashin Papi , ta daiyi haƙuri tabar ma ranta , kuma babu wanda yasan ina ma Jiddahr tayi , Dikko kuwa cewa yayi shi baiga ma duk dalilin wannan fitinar da tashin hankalin da yasa aka ɗauko Papi ba , mema yasa tun farko aka ɗauko yaron daga wurin An mata , shi ina zaisa ranshi ? Wane hali rayuwar Sultana zata shiga ? Gaskiya fa ba’ayi ma rayuwarta adalci ba , me yasa ׳………….. ? Wallahi idan har Papi ya mutu saiya kashe Jiddah , sannan shima ya kashe kanshi dan wallahi yana jin kunyar An mata.

      Shima Dady cikin tashin hankali ya iso , ganin Dikko yana kuka yasa Dady shiga wani irin mawuyanci hali , yace Babana yi haƙuri ka daina kuka , a shagwaɓe Dikko yace kuka Dady ? Ai yanzu ma na fara , yi haƙuri Babana zai samu sauƙi bazai mutu ba , ya faɗa yana kallon idon Dikko cikin yanayin shi Dikko ya tausaya mishi , Dikko yace haba Dady misali nine a irin wannan yanayi nayi imani kai da suma zakayi , yadda kakejin ni nine zuciyarka ya nuna kanshi , sannan yaci gaba da cewa nima uwarshi itace zuciyata , idan har yaron nan ya mutu , An mata ɗan ƙaramin hauka zatayi , wane irin hali kake tunanin zan shiga idan ta shiga wani hali ? Idan na shiga wani hali kaima shiga zakayi , kana shiga Momy ta shiga , Momy na shiga kaf “ya “yanta sun shiga , na rantse da girman Allah idan yaron nan ya mutu tou tabbas nima mutuwa zanyi dan bazan yadda inga tashin hankalin da An mata zata shiga ba , saina hau saman bene zanyo ƙundubala kuma nima saina sha fiya²n in faɗo matacce…….. Yana faɗin haka ya fita yabar ɗakin.

     Cikin damuwa Dady yake kiran Dikko , Babana² , amma Dikko yai tafiyarshi , hankalinshi kuma ya tafi wurin Sultana da tace masa yana can yana yawon kamfen ya manta da yankin iyalinshi , dole yaje ya bata natsuwa duk haƙurin ta saida ta cire kunyarta ta nemi haƙƙinta wurinshi , itama Jiddah sai yaci uwarta idan ya riƙeta babu wanda ya isa ya tashi hankalin An mata idan dai yana numfashi , ƙaramar yarinya mai haƙuri , ai haƙurin An mata yayi haƙuri ko sai an kasheta ne wai…………?

        Cikin wani irin ɓacin rai mai tsananin ɓaci ya dawo , ni bana san ganinshi a yanayin fushi tsoro yake bani wallahi , tunda na gama abincin banci ba naje nayi wanka ina zaune ina zaman jiran dawowarshi , sannu da zuwa nayi mishi bai amsa ba , saida yazo dai² inda nake zaune yaja hannu na har zuwa ɗakinshi kuma baiyi magana ba.

      Dakel ya rufe ƙofa sannan yazo inda nake tsaye ya fara cire kayan jikina , kallonshi nayi cikin damuwa nace baka da lafiya ne ? Baimin magana ba yaci gaba , saida ya saukeni duka sannan ya jani zuwa bakin gado , da hannu ya turani na faɗa sama ina kallonshi , bargo na ɗauka na rufe jikina tare da saukowa ina matsawa inda kayana suke nace masa ka barshi kawai ngode , yaye bargon yayi tare da maidani saman gadon , ban sake saukowa ba , a damuwance shima ya hau gadon , har yayi abinda zaiyi ya gama baiyi magana ba kuma bai wani nuna yanajin shauƙi ko farin cikin kasancewa dani ba , kuma duk fushin da yakeyi bai hanashi maidai nushi ba , ya maida duka sosai , saida ya tabbatar na samu natsuwa kuma ya bani natsuwar da farin ciki da ƙoƙari ba wani lalaci , saida ya tabbatar nakai sosai sannan ya barni , ya rigani yin wanka , yana fitowa ya shirya , godiya nayi masa tare da masa addu’ar Allah ya ƙara mishi lafiya kuma ya bashi wata lafiyar a fagen wasan danbe , yayi nisan kwana mai albarka , baiyi magana ba ya shirya ya fita daga ɗakin amma duk wayoyinshi a nan ya barsu kila ba fita zaiyi ba.

      Bayan ya fita nima na gyara jikina na fito , palon ɗakinshi na sameshi zaune saman kujera ya kwantar da kanshi saman hannun kujera , ina fitowa ya fara faɗa wai ba ya hanani wannan ƙazantar ba ? Kodai in rabo kayana ɗakinshi da nawa , yana nufin in ibo wasu in ajiye a ɗakinshi , ko kuma duk lokacin da zanzo in riƙa tahowa da wasu kayan , daga yau bazai sake min magana akan idan na cire kaya na daina maidasu ba saidai zai zanemin jiki tunda kunnen ƙashi nake da , murmushi nayi ba tare da nace masa komai ba , nasan kila wani ya ɓata mishi rai yana neman hanyar da zai dakeni ne danya huce shi yasa yake nemen ya tsakuloni faɗa tunda banda haƙuri in masa rashin kunya ya zaneni yai tafiyarshi , dole kimin dariya tunda kin raina ni , haba niɗin banza ? Ni na isa in raina ka tunda nasan amfaninka ina faɗin haka nayi waje…..

      Cike da tausayi yabi bayan Sultana da kallo , wata zuciyar tace masa kodai ya faɗawa An mata abinda ya faru , yayin da wata zuciyar ta gargaɗeshi akan ya barta kawai tayi farin ciki , idan kuwa ba haka ba yau bata iya bacci kuka zatai tayi mishi kuma yace zai daketa , ya ƙyaleta Allah dai ya bawa Papi lafiya kawai ya ɗauko mata ɗanta , ashe shi yana ta hasashen Jiddah zata barbaɗe An mata ashe tunaninta ya karkata ne akan ɗanta , hmmm Allah ya kauda ɓacin rana , dan ya ɗaukar ma kanshi idan har Perpy ya mutu wallahi saiya kashe Jiddah ,

       Dady kuwa ya kira Dikko baisan adadi ba amma Dikko yayi fushi bai ɗauki wayar ba , Momy ma ta kirashi itama har ta gode Allah amma sam Dikko yanaji kuma yana gani amma ya basar da kiransu , Dady kuwa yayi ma Momy fata² yace bata da lissafi kwata² in banda hauka da rashin tunani irin na mata , yace yarinyar da uwarta ta kashe auren “yarta da ɗanta akan wani dalili banza can nasu na mata , kuma “yar ta fita da ciki taje ta zubar da cikin kuma ta kirata ta faɗa mata dan taga iyakarta , duk abinda sukayi hakan baisa ta gane inda duniya ta nufa ba taje ta sake jajibo Jiddah ta kawo cikin zuri’arta , dama ita Momyn Jiddah ta zubawa fiya²r ta mutu kowa ya huta , ya ƙara da cewa kuma idan har Papi wani abu ya sameshi ba abinda ya dameshi da yadda zuminchin su yake saiya ɗaure Jiddah daga ita har uwarta. Momy zatayi magana Dady yace ta rufe mishi baki , ba abinda zata faɗa mishi , batayi ma Mom Papi adalci ba , ko albarkacin yadda Babanshi ya jefo yarinyar mutane daga sama kuma ta dawo daga duniyar ƙanwar mutuwa a hakan bata rabu da Babanshi ba ta haƙura ta zauna dashi , idan bata sani ba Babanshi dukan yarinyar nan yakeyi wahalarshi takesha kamar tashin hankali amma ahakan tayi haƙuri ta zauna dashi bata taɓa guduwa ta barshi ba , 

      Cike da nadama Momy tace taya zai daketa ne ? Dady yace da kanshi ya faɗamin ko nasan sunyi ne ? Yaje ya ɗauko amanar yarinyar mutane yazo ya kulle yarinya a gida yana ta gana mata azaba , nayi imani da Jiddahr ce tuni saita faɗa kuma sai anyi tashin hankali , ita kuwa ya doketa ya zageta duk haukarshi idan ya tasoshi akanta yake sauke masifarshi , ko wani ya ɓata mishi rai saiya je ya juye akanta ko ita jakace ne ? Ita iyayenta basa santa ? Ko ita ba haifarta akayi ba ? Amma duk wannan baiyi ba da masifa saida sukaje suka fitar mata da ciki tun farko ya nuna Rabiya , yace duk da haka tayi haƙuri kullum tana liƙe dashi haba baki da adalci , da kece akayi ma wani daga cikin “ya “yan naki ko aka taɓoki a gidan nan haka zaki ƙurmusashi a ɗaki ki haukatoshi ya fita yaita hauka yana saiya kashe² , baƙin halinki yasa aka birkita miki tunanin ɗa , baya auren karuwa , ita karuwa ce ki kiyayi kanki da duniya , da hannunshi ya nuna yace duk sirrin dake rufe ki kiyayi buɗeshi idan kuwa ba haka ba wata rana sai kunya ya hanaki fita , mtswww ya fita daga ɗakin…..

       Dikko nidai banajin daɗi , ba tare daya kalleni ba yace An mata me ya sameki ne ? Ya tambaya a sakatance , kallonshi nayi tare da cewa cikina ne ke ciwo na faɗa ina kwanciya jikinshi , yana burgeni idan yayi magana da shagwaɓe ko sakata irin nasu na “ya “yan “yan gayu , sannan yayi murmushi dakel yace to ko sai na ƙara kamfen in ne ? Yayi maganar yana riƙeni da riƙon da nake so , ƙara lafewa nayi sosai a jikinshi , gyara kwanciyarshi yayi tare da ɗagoni daga saman gadon ya ɗora rabin jikina a jikinshi yace ta ina kikejin ciwon ne ? Ya ƙarasa maganar yana laluba cikina da lallausan hannunshi , agogo ya kalla da sauri ya saukeni daga jikinshi yace Dady yayi maganar yana sauka daga saman gadon jikinshi yana ƙyarma , lafiya yazo gidan nan ? Yayi maganar cikin tashin hankali , a zuciyarshi yace na shiga3 kardai Papi ya mutu Dady ya taho , da sauri yasa talkaminshi ya fita ,

     Sauka nayi daga saman gadon na fita palonshi ta jikin window na tsaya tare da yaye labulaye , a dai² lokacin da naga Dikko ya isa wurin Dady da gudu ya riƙeshi yana magana , wurin da nisa sosai banajin abinda yake ce masa , amma shi Dikko yanayin maganar da yanayin fushi yana nuna kanshi sai kuma ya nuno bayanshi , da hannu Dadyn ya nuna mishi yayi haƙuri yana shafa kanshi , girgije hannun Dady yayi daga saman kanshin da yake taɓawa ya juyo cikin fushi , riƙoshi Dady yayi ya rumgumeshi yana magana cikin yanayin lallashi , shima Dikkon riƙe Dady yayi ya rufe idanuwanshi yana ci gaba da magana , bansan yadda akayi ba naga Dikko da Dady sun shiga mota sun fita daga gidan , Ashiru da Abbakar kuma sun fita a motar Dikko sunbi bayansu , tsoki nayi tare da cewa wannan siyasar banza Allah ya raba Dikko da ita……

      Yau bai kwana gida ba , kuma washe gari bai dawo ba sai 11:30 na dare , ko makaranta yau ni naje da kaina ba Ashiru ya kaini ba , kuma daya dawo gidan baifi mintuna 5 ba ya fita , dan naji shigowarshi amma kafin in fito harya fita ban samu haɗuwa dashi ba , saida yayi kwana biyar baya gida kuma yana Katsina , ranar daya dawo , dashi da Papi dasu Nabeela suka sauka gidan , palo na samesu su dukansu “yan uwanshi manyansu da yaransu , Papi sai kuka yakeyi yana kiran Momy , Dikko kuma yana kwance saman kujera 3siater da yanayin damuwa , Rabiya tana zaune saman hannun kujera sai cewa takeyi yayi haƙuri , kai gaskiya bazan gaji da faɗa ba , “yan uwan Dikko wayayyin matana ne , “yan gayun billahillazi , ibar ƙarshen ƙarni , gogaggi masu ilimi da buɗewar ido , duk iya gogewarki idan kika tun karesu wallahi sai kin kama kanki dakarun mata ne da zamani kebinsu , sannu nayi musu nima na samu wuri kusa da Nabeela na zauna ina kallon Dikko , kaɗan ya buɗe bakinshi yaja iska ta ciki da yanayin da idan muna cikin wani yanayi dani dashi , murmushi nayi tare da sauke kaina ƙasa , shima murmushin yayi tare da cewa An mata ga ɗakinki nan yana kiranki , da gudu Papi yayi wurin Rabiya yana ci gaba da kiran Momy ya maƙale ƙafaɗarshi ya riƙeta ya juyo yana kallona.

      Jawoshi Dikko yayi gabanshi yace kai sa idonka nan , kallonshi Papi yayi yana kuka , nan ne gidanku ɗan ƙwaƙwar tsiya kana can kana ƙwaƙwa za’a kashe ka bari inji ka sakemin kuka kaga yadda zanci maka , dariya akayi gaba ɗaya , duk suna kallon Dikko da Papi , ƙara ɓata fuska da baki Papi yayi saida yayi ajiyar zuciya yace Momy , Dikko yace ga Momy can ya nunoni tare da cewa kai fashin iyaye kakeyi ne ? Ajiyar zuciya ya sake saukewa a karo na biyu yana kallon Dikko , murmushi Dikko yayi cewa zaka hau doki ? Ya ƙarasa tambayar da girarshi , kai ya ɗaga alamar zai hau , waya Dikko ya ɗauka ya fara kiran Umar , bayan ya ɗauka yace a kawo doki Papi ya dawo gida , yana faɗin haka ya tsinke kiran yace je ka wurin Momy itace zata ɗoraka a doki , wurina ya taho yana ajiyar zuciya , amma da yazo saiya tsaya wurin Nabeela yana kallona , 

Dikko yace kace mata ka daina kuka zaka hau doki , cikin shaƙaƙƙiyar murya ya faɗa yana kallon cikin idanuwana , dan kauda kaina nayi cikin yanayin jin kunya , dariya Dikko yayi tare da cewa Papi riƙeta idan baka riƙeta ba bazata ɗoraka ba tace , da sauri na tashi , dariya Dikko yayi sosai yace ku kalli fulani da kawaici , yau ni ga ɗan farko gaban An mata , kam aiko yau saina ɓanɓare miki kunya tashi yayi ya ɗauki Papi suka biyoni ɗaki ,

      A kona ya sani ya sauke Papi ya riƙe hannunshi yana daga ta bayanshi , cikin kwantacciyar murya yace riƙeni ya faɗa yana min kallon ƙauna , riƙeshi nayi cike da soyayya , yace sumbaceni ya nunamin saman bakinshi da ɗan yatsa kuma bai daina kallona ba , matsawa nayi na sumbaci bakinshi , da hannun ya riƙo ƙeyata ya haɗe bakuna wuri ɗaya yana sauke ajiyar zuciya cikin ƙaramin sauti mai tada hankali , bakinshi a cikin bakina yace ke Papin ne baki ɗauka ? Ni bana san wannan kunyar gaskiya so kikeyi yazo bai saba dake ba kullum yana kiran Momy ? Haba An mata nidai bamu iya irin wannan abun ba kinji ? Kija ɗakin a jiki idan Umar yazo da doki ki ɗorashi da kanki , yana san doki sosai , kuma zan bar muku doki ɗaya anan zaki ga ya liƙema gidan nan bazai wani sake tunanin gidanmu ba , kiyi wasa da ɗanki kija shi jikinki idan kina wannan kunyar haka zasuyi ta ibe miki “ya “ya suna tafiya dasu su kuma zasu saba da can ke kuma ko oho , idan kika bar “ya “yanki sake haka za’ayita labbatarki ana kakkashe miki su , ki koya ma “ya “yanki tsoron mutane , banda Allah yasa Papi yana da sauran rayuwa yanzu da an kashe miki ɗa , kuma ai nasan zakiyi kuka ko ? Ya ƙarasa maganar yana ci gaba da tsotsar bakina cikin wani irin bahaggon yanayi , mutsurniya na fara ya girgaza kanshi alamar in bari , kuma in bashi harshe na , riƙe harshen yayi tare dayin murmushi mai sauti yana kallon idona cike da tsantsar ƙauna , gaba ɗaya jikina mutuwa yayi na kasa wani ƙwaƙwƙwaran motsi , da ɗayan hannunshi ya kamo hannuna ya ɗoramin inda yake so na riƙe mishi kanshi , nice na ajiye ɗayan da irin yadda yake so ya kasance , dan nima zuwa wannan lokacin na fara zama “yar hannu , ina riƙeshi kukan Papi ya fara fitowa , sakeni yayi tare da jana ya kwantar dani gefen gado dan yasan bazan iya tsayuwa ba , dan cewa yayi wai da an taɓani sai kawai in wani mutu murus , shi wannan abun yana mishi baƙin ciki ragguwa da ni , fita yayi daga ɗakin dashi da Papi…..

     Har dare duk basu tafi ba , nima ban sake fita ba , koda Umar yazo da doki shine ya ɗora Papi , abinci ma Momy ce ta bada aka kawo musu , bayan abinci yazo Nabeela tazo ta kirani muci abinci , gaba ɗayansu sun hallara a saman tebirin cin abinci nima kujera naja na zauna , mai bin Rabiya take ba Dikko labarin yadda suka ƙare da mijinta da zaiyi aure , bansan farkon labarin ba , amma tunda naga Dikko yana gaggaɓa dariya nasan cuta akayi , jakarta ta buɗe ta fiddo irin maganin da Dikko ke bani , ƙara ƙyalƙalewa yayi dariya yace nafa yadda basai na gani ba , mata ? Mata ? Hmmm , Rabiya tace ai raina ta ma yayi ni tayama namiji zai fara hasashen ƙara aure bare ya fara tunkarar matan , dariya Dikko yayi tare da riƙe kanshi da hannun haggunshi yaci gaba da cin abinci kanshi yana kallon filet in da yake cin abinci , Nabeela tace ai wallahi ba wanda ya isa ya auramin tsoho tayi maganar tana fashewa da kuka , Rabiya tace banza karki ma kanki baƙin baki wannan jakar matar tashi ba a bakin komai take ba wurinshi , koma komai ce ke a wurinki mayinos ce , cikin kuka tace ni sai kace nice kaɗai ɗiya a gidan ? Dikko yace tou auren tsoho miye kuma ? Yayi maganar yana ɗaure fuska , yace ko dan anyi magana a gabanki zaki mana rashin kunya , cikin kuka tace Yaya amma waye aka haɗa da tsoho ? Saini ? Rabiya tace ai tsohon yafi saukin shigarwar lungu , ga matarshi wata tutar ƙasa ce , ke har akwai macen da zata tayar miki da hankali ? Dikko yace ƙyale sakara , Nabeela tace nifa banajin matarshi kawai dai yamin tsufa ne , Dikko yace to zani ne shi da zaki ce ya miki tsufa wurin ɗaurashi ? Ko zani ne shi ai abun iyawa ne ma , idan ya miki tsufa ai kinsan irin wanka ke da zaki ɗauka iya wankuwarki iya adadin yadda tsufan zai ɓoye a jikin tsuhuwar sitirar da kika saka , kinga tunda ya haɗu dake basai ki rage mishi tsufan ba ? Nuna Rabiya yayi tare da cewa ai kamar Hajjaju ce da atamfar data ɗaura tun ina rakiyar zance take da atamfar nan har yanzu kullum kyau take mata duk tsufarta , dariya akayi gaba ɗaya amma banda ni , Rabiya tace lallai Baban Dady amma wallahi ka rainani da yawa , kai lokacin da nayi zance ma ina kazo duniya ? Ɗaure fuska yayi , gaba ɗaya suka sake ɗaukar dariya , maibin Rabiya tace bar ɗan iska saboda yaga ya ajiye wannan gemun yake raina mutane sai munbi dare mu askeshi , dariya yayi tare da cewa da kuwa kun asko masifa , mai bin Nabeela ta canja firar da cewa mukam dai sai baba gomna muma muna bayan Dady , Nabeela tace idan ya faɗi zaɓen fa ? Kike wani kiran gwamna , mai bin Rabiya tace bama zai faɗi ba sai yaje insha Allah , ah munga su Nabeela as matar gwamna , kwarkwasa kenan ,

     Dikko kuwa cewa yayi oh , An mata kin daiji ko ? Wai ita matar ta gidan itace tutar ƙasa , bata miƙe ba kenan tana kwance , jinjina kanshi yayi tare da cewa lallai matan ciki sai sun dage , ai ya kama ace idan mijinki zaiyi aure ita wacce zata shigo ya zamana gabanta na halbawa saboda shakkunki da tsoron kishi dake , amma sai ya zama ita mai shigowar wai itace zata halba zuciyar ta ciki , kina aikin me mace ? Haba mata ? Idan ke tutar ƙasarce kamar yadda kuka faɗar saita shigo gidan dake da mijinki da “ya “yanki tazo ta gigita miki miji , kina can kina haukar banza zakiji karatun yasha banban , idan kuma mara adalci ne saidai ya yarfeki tunda shi ya samu lallausar rayuwa , nidai idan zan ƙara aure nasan amaryar sai taji tsoron An mata , Rabiya tace ƙwarai kuwa ita bama zata yadda ta fara shigowa ba ko Sultana ? Tayi maganar tana kallona , Dikko kuwa cewa yayi ai zanyi auren da wuri ne , 

       Gyara zamanshi yayi tare da cewa bara in baku labari , a london na haɗu da wata “yar tasha , tunda ta shigo jirgi kawai tayo wurina ta zauna kusa dani , ɗan yamutsa fuska yayi tare da nuna yadda mata keyi , da irin maganar mata , yaci gaba da cewa aka wani cemin sannu ko ? Ya nuna yadda tayi maganar da yadda ta zauna , yadda yayi abun ne ya ba kowa dariya gaba ɗaya harni saida nayi dariya ina kallon Dikko , wallahi Dikko baijin magana ko kaɗan , shi kuma baiyi dariya ba yaci gaba da cewa da wutsiyar idona na kalli sakarai a zuciyata nace suna can na baro gidanmu , nidai ban mata magana ba , riƙe take yarinya tana da aji sosai gaskiya “yar gayu ce kuma ta iya wanka tana fama da wani irin girman kai , amma duk girman kanta da tazo wurina saida ta saukeshi , nidai banyi mata magana ba kuma ban kalli inda take ba , can bayan wani lokaci sai ga Abbakar yazo , yana zuwa yace DK ya haka kuma ? Shima Abbakar ya kwaikwayi maganarshi , yaci gaba cewa keda ke Katsina idan kin gansu ko kinji maganarsu tou Dikko yasan suna nan daga ita har Abbakar in , Abbakar yace malama da Allah tashi , batayi ma Abbakar magana ba ta juyo wurina tace suna na Yusra , haka nan naji zuciyata ta tashi kamar zanyi amai wallahi , da sauri naci cingom ,

      Abbakar kuwa yaci gaba da cewa bara ki tashi a wurin ba ? Wurin zamanta ta nuna mishi da hannu tare da cewa ni ba’amin magana a saman kai , danni maza basa burgeni , saboda hauka irin na Abbakar ƙiƙi² ya kamata da kokowa , yana bara ki tashi a wurin ba ? Naso in musu dariya amma sai nace ya barta , bayan ya saketa ni saina tashi nace shi ya zauna , ina tashi ta taso da yanga sai ƙwarƙwasa take tana yauƙi tafiya cikin tsari da ɗaukar hankali irin tafiyarki Hajjaju ya nuna Rabiya , yace cikin kissa tace haba Yayana ya nuna da salo mai burgewa yana ci gaba da cewa tace yi haƙuri idan na ɓata maka rai , tana maganar tana wani kakkafe ido , ya nuna yadda takeyi , gaba ɗaya aka sakeyin dariya amma yanzu banda ni , Dikko yayi wata irin dariya , yace kamar wani sakarai haka na kalleta , kallona yayi tare da cewa tafa burge , kunga kenan ya ɓadda labarin akan yadda ya ɗaukoshi , ai farkon labarin cewa yayi duk girman kanta da tazo wurinshi saida ta sauke , kuma yace data faɗi sunanta yaji zuciyarshi ta tashi , amma da yaga naji kishi saiya juya labarin kunga kenan ya fasa faɗar yadda labarin yake kenan , bai ci gaba da labarin ba , duk yadda akayi kila Yusra ƙawar Sadiyya matarshi data mutu , irin tafiyar Rabiya da ya faɗa kenan yana so ni na koya kenan.

      Cikin fushi na tashi , amma kafin in miƙe ya zaunar dani da ƙarfarshi yana kallona , Rabiya kuma tace , tou ya kukayi ? An mata najin kishi mubar maganar , Rabiya tace haba Sultana ai laifin kine ma fuska kika bashi har yazo gabanki ya samu ikon maganar mace , Dikko yace ai ban shanyu ba shi yasa zanyi ma Perpy wata Momyn.

      Canza labarinsu sukayi akan kishiryar Nabeela wai ƙazama ce ba gogewar rayuwa , bata iya komai ba saidai taci ta jibge a wurin , Dikko dai bai sake magana ba ni yake kallo , yanajin yadda ake ta aibata sakarkarin mata , sai ƙara yi ma Nabeela ɗamara ake ana ƙara ɗorata a hanya , bayan wani lokaci kuma sai suka koma labarin kayan mata , tashi Dikko yayi dan har yanzu Umar bai dawo da Papi ba ,

      Nima tashi nayi na barsu , ina shiga ɗaki wanka na shiga , lokacin dana fito har sun tafi , sai Nabeela da Papi kaɗai , ina fitowa suka shiga danyi mishi wanka , kafin ta fito na ɗauki kayana nayi ɗakin Dikko , sannu da zuwa yayi min tare da ansar kayan cikin ladabi , yace Allah ya taimakeni kenan ? Ai ina nan nace tou kai Dikko me ya kaika ? Ila marin mace da mangariba , ???? ai na ɗauka yau dahuwar kan rago zakimin ? Nayi tunani kila a saman wuta zan kwana dan nayi wannan maganar , nace Dikko yau zakaci ubanka An mata tayi fushi kuma ga Nabeela , Allah dai ya rufamin asiri ashe ina da rabon zanyi farin ciki a daren nan yayi maganar yana zaunar dani gefen gado , yaci gaba da cewa ai ban sani ba “Yar matan nawa ta girma ba.

    Kusa dani ya zauna ya rungumoni , sannan ya shiga rattaɓamin kaf abinda ya faru da Papi , naji babu daɗi sosai amma shi saina nuna mishi ai ba komai , yace munafuka ce Jiddar nan , yace lokacin da nayi rashin lafiya , wanda na tafi na barshi kenan , yace tazo ta zauna tayi ta haɗa masifa , kuma itace ta kai Momy ta barota suka ɗauko Papi kila tun lokacin take so ta kashe shi….

 Bayan kin tafi kin barni………..


      Kai……………….. Saina kashe kaina , wallahi saina mutu tunda baki so na mutuwa zanyi , Yazeed kike so ko ? To ni zan mutu in bar mishi ke , buɗe ƙofa nayi na fito , na biyo bayanki amma ban ganki ba , komawa nayi ina ihu , na ɗauki wayar wuta da aka sauke ƙasa na koma ciki , ina shiga na hau sama ina ihu saina kashe kaina , mai gadi ya fara kiransu Ashiru , nasan na ɗaura waya a wuyana bayan na ɗaure ƙarshen a jikin ƙarfen bene nayo ƙasa ,

     Daga haka ban sake sanin abinda ya faru ba , Ashiru yacemin da mai gadi yai mishi waya gaba ɗayansu suka zo , hankalin kowa ya tashi gani na zube a ƙasa , kila wayar bai ɗauru ba , ko kuma nayi ma ɗaurin nauhi shi yasa ban tsaya a saman iska na mutu ba , a haka suka sameni , da suka tambayi mai gadi abinda ya faru , yace bai sani ba amma ya ganki kin fita da gudu ni kuma ina kiran Yazeed , Dady suka kira kai tsaye suka sanar dashi cewa Mai gida ya mutu , Dady yana jin haka ya maƙale wurin ya daina aiki kwata² , sune suka sanar da kowa Dikko ya mutu , Dady kuwa daya dawo saidai yace Babana , haka yaita ɗaukewa kamar “yan nepa suna wasa da wuta , tafiyar ƙarshe ce da yayi saida aka kaini government house Dady ya dawo , yayi kuka wanda bana san ina faɗa , saida aka taru Dikko ya mutu , An mata da anyi gaggawa rufeni da an binneni da raina.

      Bayan an tabbatar ban mutu ba wanda shima Dady ne ya kafe ban mutu ba , irin sabbatun nan na wanda zafin rashi ya ɗimauta , haka Dady yasa akaita kirayen² likitoci , a ido ni na mutu amma a baɗinance Dikko yana nan , murmushi yayi tare da cewa wai aljannu sun shanye numfashi na , haka aka fita dani waje akayi ta magani daban ciwo daban , jinyar nan da Dady akayita bawan Allah….

      Abinda yasa dana samu sauƙi ban wani ji damuwa akanki ba , nasan ina da fushi sosai kuma haka nike da riƙo kuma ina da halin ko oho , duk abinda na bashi baya na gama dashi har abadan duniya wallahi , bansan abinda yasa ni bana iya fushi dake ba , ko nace zanyi zuciya dake bana iyawa , tunda nake a rayuwata ban taɓa gardama wa iyayena saida kika zo rayuwata ,

      Labarin mafarkin da kikeyi kaf abinda kika faɗamin saida Mustapa ya faɗawa Ashiru , kuma shine yace wai anyi ma Al ‘ Ameen lamba su duba kanshi zasu ga aski da lambar mutuwarshi , ni bansan Al ‘ Ameen yana tsafi ba kwata² , tou tayama zan fara mishi wannan mummunan zaton bayan rayuwar kowa a rufe take , babu wanda yasan sirrin wani sai wanda ya faɗa , Mustapha yasa aka fitar da Al ‘ Ameen yace wallahi mutuwa zaiyi kuma idan ya mutu hannuna zan tabbata matsafin kamar yadda mutane duniya ke kallona.

     Naso naga Al ‘ Ameen dan naso zanyi magana dashi amma hakan bai yuwu ba , shi Mustaphan yayi ma Ashiru jagoranci zuwa inda sukayi tsafe²nsu , komai Ashiru yayi saida suka gama komai lumfashi na ya dawo , tunda nake ban tabajin irin wannan tashin hankali ba wai an shanyemin nufashi kiji wani masifa , hmmmm , Yazeed kuwa Ashiru yaci ubanshi kuma shine ya maido Abbakar company duk bansan anyi ba ,

      Waye shiɗin ? Kawai abokina ne amma abotar ba wani can² ba ya faɗa yana yatsina fuska , tou shi me yasa Ashiru ya ɗaukoshi ne ? Munyi maganar shi da Ashiru anyi ma wata “yar uwarshi fyaɗe harta mutu , da na shiga cikin lamarin Ashiru ya fitar dani , amma ni Mustapha yacemin wai matan Babanku dasa hannunsu a damuwarka , kwanciya yayi tare da kwanto dani jikinshi yace can damuwarsu duk abinda mutum yayi kanshi , idan nayi maganarta nayi imani Dady saiya saketa ni kuma bazanji daɗin haka ba , saboda duk Momy za’a ɗorawa laifi , familyn su Dady haushinta sukeji sosai danma suna shakkun su Rabiya ai da yanzu sunyi waje da ita , ya faɗa yana nunawa da hannunshi , yaci gaba da cewa “yan uwan Dady basujin magana yadda baki tunani amma zaki gani tunda zaki shiga cikinsu , suma dai wayayyi ne amma Momy ta raina ma wayewarsu shi yasa “ya “yanta suka fita daban , tsarinsu ya fita daban idan kun shiga zakiga yadda su Rabiya ke bada haske a taro , gasu da rainin wayau , idan su Rabiya suka raina miki ƙura tom hmmm ya jinjina kanshi , amma duk wani banzar wayewar familyn Dady idan “ya “yan Momy sunzo to kin zama “yar kallo da koyon gyara inda aka tsere miki a wanka , zamani yazo anan zaki gani ki koya ki kuma yi gyara , ni dama bana wani shiga sabgar kowa , tunda bana binsu biki ko suna , iyakata dasu gida , idan basa nan zanji babu daɗi gidan yamin ba daɗi kuma Momy bata da magana , ni kuma faɗan da mukeyi dasu ne nakejin kewarsu idan basa nan , ko wuri zasu zasuce munafiki yau idan muka tafi bazamu dawo da wuri ba , kuma kowa baya rayuwa da “yan wasu ɗakin sai “yan ɗakinsu , haka zan gaji da zama in fita cikin gida bana nan bana can kamar wani maraya tunda ni bana fita waje iyakata gida Dady baya bari naje wani wuri saidai in saci hanya idan baya nan , idan suka dawo zanyi farin ciki , kuma zasu bani labarin duk abinda ya faru idan sunje wuri sun dawo , ni ba abinda ya dameni da rayuwar wani tawa nakeyi , sai “yan uwana mata sune kaɗai abokaina muyi faɗa mu shirya , suma “yan uwan Dady ni babu wani ruwana dasu dan Momy ta koyamin tsoronsu tun ina ƙarami , su kuma suna so na saboda yadda Dady yake ƙaunata dan soyayyar Dady a kaina bai ɓoye ba , amma iyakata da mutum sannu daga nan kawai zan zama kurma , kenan bayaji bare ya bada amsa , idan kuma ba’aci sa’a ba ko kayimin magana sai in maka shiru bazan ma ce maka sannun ba sai in tsare ka da ido ya faɗa yana murmushi , yace sai kiga simi² mutum ya kama gabanshi , kuma ba ƙarya ya faɗa ba , ashe  yana sane da duk iskancin da yakeyi , dan aradu idan Dikko ya riƙeka da ido sai kaji babu daɗi har ka kama kanka , tou gashi baida yawan murmushi kuma shi dariya ma sam² da bayayi sai yaji mugunta zakiji shi ƙa׳ yana dariya , kuma dariya ba ƙaramin kyau take mishi ba , Allah sarki mai uwa baya san laifinta , amma gaskiya Momy gaba ɗayanta batayi ba bata da mutunci ko kaɗan , gata da raini , rankatakaf ta ɓata “ya “yanta da baƙin hali basu san mutunci kowa ba saina mazajensu shi yasa mazan nasu kamar sun masu asiri biye mazajensu suke dasu , kuma ita bata iya neman asiri ba saidai bariki da duniyanci wurin iya nannaɗe zuciyar namiji , shi yasa Momy ta share kowa a wurin Dady dan yanaji da ita sosai , amma basa san ace Momynsu tana da miyagun halaye , kai , amma gaskiya “yan uwan Dikko da suke ɗaki ɗaya zamani ne su , makaranta ce mai zaman kanta , sunyi׳ , sun haɗu׳ wayayyi ajin farko , kuma sunfi “yan ko wane ɗaki yawa a gidan , ga kuma Mai gida DK nasu…..

       Satin Papi 3 a wurina amma har yanzu bai daina kukan Momy ba , kuma Nabeela tana nan ta dawo gidan kwata² da zama , ga Dikko baya zama , ni kuma banda lafiya , dana ce masa ko akai Papi wurin Momy cewa yayi kar a sake akai mishi ɗa wani wuri yaje yaita kukan idan ya gaji zai daina , Nabeela kuwa ta faɗawa Momy Papi yana ta kuka shidai Momy , tazo da kanta itama dai tayi kewar Papi , cike da soyayya Papi ya riƙe Momy su tafi wurin Dady , har ranar da suka dawo dasu Rabiya saida yaba Momy labari amma wasu ya manta sai ya tambayi Nabeela , murmushi Momy tayi irin na ƙasaitaccin mata da irin yanayin kallon Dikko , dai² gani sukeyin kallon amma idan kasa ido sosai zakaga kallon nasu yanayin ƙasa kuma basa motsa idon , baka ganin lokacin da idon yake tafiya idan suna rageshi , idan kuma suka gyara kallon nasu sai kallon ya bada wani iri mai burgewa , da irin kallon ta tsare Papi tana cewa ni duk naga ka zama wani baƙauye ta faɗa tana murmushi da gefen bakinta tana ci gaba da cewa Nabeela anya zanyi auren nan ? Kafin Nabeela tayi magana Papi yace ni nayi cau ya faɗa yana harar Momy.

       Dariya tayi tare da cewa ni bakaimin wani kyau ba , iyayenka basu iya raino ba kuma bazanje dakai ba , kuka ya farayi yace ina juwa , dama da yawo ta kama Papi , duk wankan da akayi Papi saida Momy tasa Nabeela ta sake wankeshi aka gayeshi tace Nabeela taje anjima ta dawo dashi , gaba ɗayanmu mukayi mata rakiya ta tafi.

       Dikko kuwa ya kirani yayi faɗa sosai yace an ce masa wai anga Papi gidansu , meya faɗa min ne ? Zanyi magana yace in mishi shiru ni dama na raina mutane , ya ƙara da cewa ya rantse da Allah idan wani abu ya sameshi ni idan nayi mishi kuka saiya zaneni , itama Nabeela zai haɗu da ita shima Papin zaici ubanshi bari ya dawo , yana faɗin aka ya tsinke wayarshi.

Ashiru ya bashi haƙuri , Dikko yace shi bawai yana hana Papi zama wurin Momy ba , fiya² fa aka bashi sai kace wani ƙwaro , idan suka kashe mata ɗa ni ba abinda ya dameni kuka ne dai bata isa tayi min ba , gidan nan munafinki gida ne kuma na faɗa mata , mu kanmu “yan gidan ya muka ƙare bare kuma wani jika , kadai san halin Momy haka take zama ta tisa Papi taita habaice² , tana irin wannan maganganun nasu na mata. Haƙuri Ashiru yai ta bashi ƙarshe dai Dikko yayi shiru ya ƙyale Ashiru.

      Nabeela kuwa kila shi ya kirata yaci mata mutunci , bansan yadda akayi ba taje ta taho da Papi , yana ta kuka , ta waya Dikko ya zageshi yace kuma bari yaji ance masa ya sake kiran Momy saiya turo Jiddah ta kashe shi aje can a jefar dashi , bazai sake ganin Momy ba kuma bazai sake cin abinci ba ,

    Na faɗawa Inna banda lafiya , kuma na faɗa mata ciki nake da , na ɗauka zatayi farin ciki ta kirani tunda saƙo na tura mata , cewa tayi can ni ya dama , kuma bata faɗamin duk abinda ya shafeni da Dikko kar na sake faɗa mata ba ? Dole na haƙura naci gaba da rayuwata daga ni sai Dikko da “yan uwanshi mata.

       Rabona da Inna kenan , saida ta kirani ta faɗamin rasuwar ɗan uwanta baban Sultan , yayi haɗarin mota , a nan gidan Kaka ake zaman ta’aziyya , za’ayi jana’izarshi da bayan azahar , dani da Nabeela da Papi muka tafi , kuma kaf “yan uwan Dikko sunje min a ranar da akayi rasuwar suna nan akayi jana’iza bayan an dawo sukayi gaisuwa wa Inna Kaka da matan mamacin sukayi tafiyarsu , amma muna tare da Nabeela , Dikko kuwa bai zo ba dama baya gari , yadai turomin text in tafi gida haka nan bawai nan zanje in jibge ba harsai an raina ni ba , dana nuna masa ya bari zuwa anjima cemin yayi ya gama magana , dana faɗa ma Inna zan tafi taji damuwa tace in bari sai anjima nace mata shi yace in tafi , taji ba daɗi dan kowa da “ya “yanshi a kusa dashi haka na tafi tanaji kuma tana gani bataji daɗi ba , gashi ba dama ta kira Dikko.

        Tun daga ranar ban sake zuwa ba sai ranar addu’ar 3 , Momy ma taje min a ranar kuma su Inna anji daɗi matar gwamna tazo , haka taita tattaro mutane tana cewa ga surukar Sultana suje tayi musu ta’aziyya Momy kuwa riƙenta take tana wannan rainin nata , da ta tashi tafiya ta bada kuɗi masu yawan gaske sadaka , shima Dikko ranar addu’ar 3 yazo , kuma yana zuwa yayi gaisuwa yai tafiyarshi bayan shima ya haukatasu da kuɗi sadaka , ranar mu kuma sai dare muka koma gida dani da Nabeela bayan nima na bada tawa sadakar dan nima yanzu inaji na dai² nake da duk wani mai jin shi yana da hatimin nasarar shi , dan duk wata damuwa ko takaici Dikko ya shanyemin shi , baya bari inyi tagumi shi yasa ya sakarmin ragamar girman kuɗi , buɗa min fili kawai yakeyi ina yadda naga dama da rayuwata….

         Yana nan bazai sake tafiya ba sai an gama zaɓe , itama Nabeela bayan zaɓe za’asa ranar aurenta , addu’arta Allah ya maida Dady a mulki sai kuma wanda zata aura shima ya haye , shima Dikko addu’arshi kenan Dady ya koma mulki , nima ina mishi fatan komawa bana so su faɗi…….


         



24/12/2019 ????????




*JAMILA MUSA…* ????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button