Uncategorized

WAYAFI SONTA 19


 Page 19

Marigayi Umar ta tuno alokacin da ya bata wayarsa shi yahak’ura”Fatanta ALLAH ya jik’an sa rahama” bazata gusheba Gurin yimasa addua sai tabar numfashi…

      DSP kuwa asace yaketa kallon zainab batare data saniba” yakuma fahimci”cewa tana cikin farinciki,dakuma tuna wani Abu marar dad’i….muje ko!cewar DSP Yana bud’e motar”zainab tayi ajiyar zuciya tafito ahankali tana k’arewa wurin kallo… azuciyarta tace oh dama haka station d’in nasu yake?”

DSP yabita da kallo”kafin yace yau gaki a police station ko?” Saina saka arufemunke! Yafad’a Yana murmushi….itama murmushin tayi had’e da cewa Kai ka Fara baccin hjy tace maka amanah” hakanefa Kuma, yafad’a suna tafiya jere gwanin shawa’a….

Gaba d’aya sai kallo yadawo gurinsu”anata k’us k’us,wasu nacewa ai k’anwarsa ce wacce akayi kiddnaping d’in ta.wasu nacewa ah ah wacce zai aura ce…Sarai DSP ya lura da kallonsu da akeyi ,amma ko ajikinsa ,sai office ma ya nufa zainab na bayansa”

Wani sanyayyen k’amshi yadaki hancin ta” ta lumshe Ido ….komai agyare tsab acikin office d’in nasa..kujerar dayake Zama yanuna Mata had’e da cewa” come & sit down pls!

Zama tyi tana kallon files d’in dake kan table d’in gabanta”

Telephone yalatsa yakara akunne”kana Ina ne?”ok jonamun CTV camera dg cell d’in zuwa office d’ina….ajiyewa yyi,yajawo wata loka, yafito da wata k’atuwar big borm ,yab’are had’e da tsotsa yagutsira”yadubi zainab daketa kalle kalle da dube dube” hii my friend! Kallonsa tayi yamik’a Mata big borm d’in Kisha kinji?” Girgiza Kai tayi”daure fuska yyi bece komaiba! da sauri ta karb’a tasaka ad’an tsukakken bakinta!wasu chacoolate ne yasake fitowa dasu ya ajiye agabanta”

Kafin yyi swech off d’in plasma d’in dake jikin bango…atake wasu mutane su 2 suka bayyana jikin akwatin tv d’in… zainab ta maida hankalinta akan tv d’in”wasu k’atti ne suka fito ta wata k’ofa da sanduna sukafara duhumar mutum 2″rintse Ido zainab tayi had’e da cewa Inna lillahi! Pls kasaka amusu mgn sudena dukansu…..kallonta yyi hankali kwance bbu wani tausayi a idonsa”yace jiyane akamusu dukan ai!amma kincika tsoro dakuma tausayi”kauda Kai tayi ta Dena kallon tv d’in tace pls Yaya haidar ni gd zanje dama haka kukeyi astation d’in?”taf ai bbu inda zakije yarinya”turo baki tayi cike da shagwaba tace basai nakira hjy ba ta turo amayar Dani gd”dawace wayar kenan?”cewar DSP Yana kashe tv d’in…

Da wayarka Mana “

Wayoyin nasa duka yamik’a Mata had’e da cewa inkinsan pass word d’in kicire saiki kirata….kallon wayoyin takeyi batayi mgn ba”yanzun tashi muje ki rakani “d’age kafad’a tayi alamar bazata jeba! Ok sarkin tsoro saiki jirani,inkinji bacci ki kwanta,ga wayoyina nan…bejira cewar ta ba yafice had’e da rufeta acikin office d’in…shiru tayi had’e da yin latse latse awayarsa ko zata iya gane password d’in”amma ta kasa”ga tata wayar ,Amma sim card d’in be fara aikiba!

Chacoolates d’in tashigaba Tasha , yyinda kujera ke juyawa da ita ,ta lumshe ido cike da nishad’i…Ringing d’in wayar sa tasakata bud’e Ido!kallon screen d’in wayar tayi taga bak’uwar number! d’agawa tayi had’e da karawa akunne batayi mgn ba….haba Yaya haidar! Kasan yau zanzo bakaje kad’akko niba,and’akkoni Kuma nasamu baka nan ,bacin kasan sbd ganin ka yasani zuwa hutun ko?”wani miyau Mai d’aci zainab ta had’e”ga faduwar gaba dataji sbd jin tamkar tasan muryar yarinyar dake mgn!hellow! hellow!! Kayi shiru kobaka jina ne nasake Kira?”ba me wayar bane…cewar zainab cikin fushi,murya adake! Wacece ke?”kibari sadda naga damar barinsa amsa Kiran mutane saiki tambayesa yasanar Miki wacece ni agurinsa… zainab bata jira cewarta ba takashe wayar…tana tunanin inda tasan me wannan muryar amma bata ganoba…

 

Ahankali DSP ya bud’e k’ofar ya murdo yashigo”da sallama , zainab wacce harta fara bacci ta tashi tana kallonsa” shima ita yake kallo”murya can k’asa yace tashi muje nakaiki gd… kafin tayi mgn ansake Kira da number d’in d’azun…kallon wayar yyi” yaja tsaki had’e da rejecting d’in Kiran sbd yasan wacce kekira” zainab kamar tamasa mgn saikuma taga beshafeta ba,duk k’asan zuciyar ta taji dad’i sosai dayyi rejecting d’in Kiran..

    Tashi tsaye tayi ta d’auki kwalin wayarta tace muje to!

Kema kin gaji da zaman ko?”

Eh Mana ” ni abinda nagani d’azun yatsaya mun arai,irin wannan duka haka…uhummm danbaki Saba bane” cewar DSP Yana bud’e k’ofar suka fice…

 

   Yana gaba tana biye dashi suka shigo cikin parlourn”hjy da bak’uwar zaune kan kujera… sallama zainab tayi cikin siririyar muryanta” hjy ta amsa fuska asake tana cewa gsky kun jima,ainazata sai dare kudawo… murmushi zainab tayi had’e da cewa muma Fara…yyinda DSP fuskarsa adaure sbd ganin bak’uwar” yace hjy sannu da gd” hjy tace yauwa!

D’ago Kai bak’uwar tayi” sukayi Ido hud’u da zainab…zaro Ido zainab tayi tana kallonsu HUSNA! Yyinda DSP dake zaune kan hannun kujera ke lura da yanayinsu” yalura zainab namamakin ganin husna, yyinda husna ke yima Zainab kallon bataso sun haduba dakuma rashin gsky dake tattare da husnar sbd ganin zainab d’in…saidai hjy batama luraba,idonta na kan TV..

Tashi tsaye DSP yyi zai wuce….Yaya haidar! Shine bazaka mun mgn ba ?” Katsaya mugaisa. Acikin nidake waya kamata yagaida wani?”cewar DSP cikin ko inkula..hmmm Dole kace haka Mana tunda nakira wayarka wata ta d’aga nasake Kira kak’i d’agawa ko?”

Eh hakane yagd dasu momy??” Cikin yatsina tace lfy lau”

Kallon zainab yyi wacce tayi kasak’e da kunne tanajin maganarsu ,amma inkallonta zakayi saika dauka tv d’in da gske take kallo..

Zainab bara naje nadawo ki gyaramun d’aki na! What? Haba Yaya haidar gani zaka bawa wata ta gyara maka d’aki! Cewar husna cikin fushi…dsp

batare da yakalleta ba! yabawa zainab key d’in yafice dg parlourn…

Husna tayi kwafa had’e da kallon hjy wacce uffan batace ba.. wacece wannan Kuma hjy”tafad’a tana nuna zainab” hjy ta dubeta”tace nan gdn take itama , sannan diyar alh ce mahaifinta k’aninsa ne,banasan fitina dg zuwanki ,kina jina?”

D’aure fuska husna tayi batace komai ba… yyinda zainab ketunani kusan shekara4 da rasuwar yah uwar ai ya isa ace husna tayi aure sbd ko acan baya yah Umar ba girmar husna yyiba, ak’alla yanxun husna tayi 27oh 28 years…tashi zainab tayi batare data sake kallon direction d’in da husna ke zaune ba…tanufi part d’in su DSP…

Tayiwa bedroom, toilet, parlournsa gyara ba nawasa ba,tayi kusan awa d’aya da wasu mintina…tana turare d’akin yashigo da sallama,ta amsa fuska asake”tace sannu da zuwa “yauwa zainab sannu da aiki”yafad’a Yana karewa parlourn kallo,kafin yazauna kan kujera Yana maida numfashi…kagaji da yawa ko?” Eh wlh”

Kaje ga ruwa can na had’a maka kayi wanka!to angama ranki yadad’e nagode…hararar wasa zainab tayi Masa tana murmushi”

Kafin yatashi yanufi k’ofar bed room d’in sa”saikuma yajuyo ahankali yakalli zainab wacce itama fitar zatayi” ahankali  yace inaso duk abinda yarinyar nan bak’uwa zatayi karki biye Mata pls”to shikenan zankiyaye…batajira cewar saba tafice..

 

 

   #########

Da dare misalin k’arfe 8:45 zainab ce tsaye akitchen tana dafa indomie, yyinda DSP ke zaune kan kujera Yana kurb’an coffee d’in da zainab ta had’a Masa…juye indomie d’in tayi tnata turiri”tana kokarin kashe gas d’in husna ta shigo bbu ko sallama!dg zainab har DSP yi sukayi tamkar basu ganta ba!

Zainab tasaka fork biyu cikin plate d’in ta ajiye kan table d’in dake gaban DSP,kafin ta ja kujera ta zauna ” cike da shagwaba tace pls Yaya bissimillah! Uhum nasanki da cin yaji beyi yajiba?” Eh Mana…keeee! Samun wuri tusar asuba kina nufin tare dashi zakici ko meye?””cewar husna tana huci.. Bbu Wanda yace Mata kanzil” k’asan zuciyar zainab fal farinciki sbd dama dan husna ta ji haushi tace suci tare..

Fork d’in yasaka ,itama tasaka suka Fara ci…wani mugun kallo husna ke binsu kafin ta fice…tana cin alwashin Dole tayiwa zainab gargadi na k’arshe akan DSP sbd yarinyar nashiga hancinta da k’udundune….

Husna na fita zainab tayi saurin Jan plate d’in tana cewa to wacce kaci tayi Aiko?” Tunda tayi na maka.

Kallonta yyi sbd yagane dan ta k’untatawa husna tace suci tare…yakuma lura akwai wani Abu tsakaninsu da juna,amma zai bi komai ahankali…cikin cool voice yace hmmm aikuwa yarinya Baki isaba ,dg yanxunma tare zamu ruk’a cin abinci…gwalo ta Masa ta fice da gudu dg kitchen d’in…

 

 

  Duk abinda tasan al’adartane kafin ta kwanta Saida tayi,kafin ta musu addua itada elham” sannan ta kwanta da tarin tambayoyi fal aranta gameda husna..shin meyasa husna ta nuna alamar rashin gsky data ganta?” Meyasa hjy tayi sauyin xance tace ita diyar alh ce?” Wata zuciyar tace sbd gudun kada zainab ta wulak’antaki  ko yimiki gori! Sannan shin dsp nason husna kokuwa husnar ke haukanta??””murda’k’ofar akayi da k’arfi aka turo husna ce ,tamkar anjehota batabi takan rufe k’ofar ba ” tafara mgn cikin gadara had’e da izzah! Umarni nazo nabaki ba shawara ba ! Kifita harkan Yaya haidar! Kokuwa kibi d’an uwanki inda yatafi..zaro Ido zainab tayi had’e da dafe k’irji! Tace mekike nufi da fad’in hakan?”

Dariyar rainin hankali husna tayi kafin tace Ina nufin Umar yayanki,Wanda yake Miki son daba yayiwa kansa” meyasa kikeson had’a hanya Dani?” Bacin mu basa’anin juna bane?”tadalilinki ne Umar yatsaneni yagayamun maganganu masu zafi da ciwo…hakan yasa ni alwashin rabaki da duniyar ,dg baya nadawo rayuwar Umar ,inhar na auresa sannan Zan d’andana Masa azabata!

Saidai kash” lokacin da nataho da mota me bak’in glass atsiyace Zan tashi dake! Sai Umar yatureki kika fad’a kwata,shinabi takansa,dukda naso kada hakan yafaru amma bbu yadda zanyi tunda kinada rabon kwana…..Nina kashe Umar nakuma kashe banza bbu yadda za’ayi Dani sbd ku matsiya tane..gsky na yadda ke jahila ce ta karshe tunda har kike ikirarin kin kashe Rai! To bari kiji kashe yah umar dakikayi bazai tashi abanzaba insha ALLAH dukda kina ganin anyi wasu shekaru… maganar DSP kuwa dakike ikrarin inrabu dashi ko?” To barikiji befi 4 month aurenmu dashiba….kutumar uba! Cewar husna arud’e…. k’arar dasukaji had’e da hasken flasha yasakasu yin shiru…da sauri husna ta nufi k’ofar da tabari bud’e,kafin ta iso anjawo k’ofar da k’arfi anrufe….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button