MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 11 to 20

    ***Baccin shi ya takarkare ya shaka kamar babu gobe sosai kwakwalwarshi da gangar jikinsa suka huta daidai yanda ake bukata shiyasa ras yatashi da asubah yayi salla sannan yasake dan komawa ya kwanta hankalinsa kwance wani lafiyayyen baccin yasake kwasheshi bashi yasamu farkawa ba sai misalin karfe 8 nasafe lokacin tuni andade da kai Aryan makaranta shi kansa yayi mamakin dalilin da yasa Aryan yau bai shigo dakinsa ba to kodai yazo yana bacci kuma bai samu nasarar tashinsa ba?

Wanka yayi yashirya cikin dark blue din shadda sabuwa fil sannan yafita,kamar koda yaushe table ashirye yake tsaf da kayan karyawa kala kala,

Shi arayuwarsa yana mutukar kaunar Irish amma yanayi yasa baya zama yaci yau dai ya zauna akan table domin karyawa saboda jiya Dr Al’amin yayi masa maganar rashin cin abinci kuma hakan na iya haifar masa da wata matsalar duk da dama matsala kam sai dai ayi fatan sauki amma yana tattare da ita,

Soyayyen dankali da kwai ya dan zuba sannan yahada coffee kamar yadda yasaba,dan ci yayi ba wani mai yawa ba sannan yasha coffee yana shirin tashi umma barira tashigo ganinshi saman table yasata dan murmusawa tana cewa,

“Mu’azzam yau ansamu damar cin abinci?,ai gara ka rinka dan ci ko kayi kumari…”

Murmushin shima yayi yasauka kasa ya gaidata sannan yamike yana fadin,

“Wallahi kuwa umma, yau banga mutumin ba ko laifi nayi shiyasa ba ako lekani ba?”

Dariya umma tayi taja kujera ta zauna,

“Ai Aryan yau akwai abinda ya dauke masa hankali amma yashiga wajen naka bai dai tasheka bane….”

“Nima nayi wannan tunanin nace duk yanda akayi yashiga bedroom din nawa tashina ne dai baiyi ba,umma ni bari inwuce wallahi mutane na can suna jirana a office tun 7”

“To shikenan adawo lafiya, Allah ya tsare yabada sa’a, Allah yadawo dakai lafiya”

“Amin umma nagode,sai nadawo”

Juyawa yayi yabi ta kofar babban falo yafita,duk da bai son maganar Hanan tazama issue acikin al’amuransa dan baida lokacinta amma sai da ta zama,abun ya tsaye masa arai bai san dalili ba,wai shi ta kira da mai budurwar zuciya,kasa yakice maganar yayi acikin ransa haka ya wuni da ita.

***

 Amarya Hanan kuwa kowa yaganta yasan acikin bacin rai take domin fuskarta babu walwala sam, ga haushin rashin baccin da bata samu jiyaba saboda bakin cikin abinda minister yayi mata, dama su masu kudin nan wulakanci garesu basa ganin kowa da gashi sai junansu,

Tana ta faman babbata fuska ta shirya ta tafi gidan anty salaha can ta iske mujahid yana jiranta cikin motarshi a kofar gidan. Bude side din mai zaman banza tayi tashiga ta zauna take tafara hawayen da tajima tana dakonsu acikin zuciyarta,

Tagumi mujahid ya rafka yana kallonta shima nasa idanuwan jajur kamar ya hadiyi kunama,shi kansa badan dauriya da juriya irin na maza ba da tuni yajima da fashewa da kukan amma dai yadaure,sunfi mintuna goma zaune shiru babu wanda yayi ko tari acikinsu sai sautin kukanta da yake fita kadan kadan,

“Hanan…. Ki daina kukan nan da kikeyi domin ahalin yanzu shi yafi komai tayar min da hankali… Kiyi shiru kinji,kiyi shiru kiji abinda zan fada miki”

Ahankali take rage sautin kukanta har tasamu nasarar tsayar dashi gaba daya sai ajiyar zuciya da takeyi kadan kadan,

“Kiyi shiru kinji…., Kin dai san ina sonki kuma najima ina son mallakarki a matsayin matata amma yau gashi k’addara na neman rabamu….. Kiyi shiru kar ki sake yimin asarar hawayenki”

Ajiyar zuciya ta ja mai karfi sannan ta kalleshi da idanuwanta wadanda suka yi ja,

“Mujahid ni wallahi idan bada kai ba bazan iya rayuwa ba, wallahi kai nake so….”

“Hanan nima ke nake so amma babu yanda zamuyi,kiyi hakuri ki yiwa iyayenki biyayya idan har na zugaki ko na goya miki baya kan ki bujirewa umarnin iyayenki to ban yimiki adalci ba sannan son da nake yimiki na karya ne,wallahi dagaske nake sonki kuma tsakani da Allah,tunda har k’addara ta raba to ni ina ganin kawai muyi hakuri kuma muyi wa juna addu’a da fatan alkhairi…..”

Wani kallo tayi masa mai cike da ma’anoni daban daban kafin daga bisani ta daure fuska cikin fushi da bacin rai tasoma magana,

“Dama ashe son da kake ikirarin kana yimin duk na karya ne kuma na yaudara,idan dagaske kana sona meye naka na fadin haka? Maimakon ka nemo mana mafita shine zaka ce wai inyi hakuri indauki k’addara, mujahid ni zaka yaudara? Ni zaka rainawa hankali? Wannan shine irin soyayyar da kake ikirarin kana yimin? Yayi kyau kuma nagode”

Bata saurari bayaninsa ba ta balle murfin motar tafita ta nufi cikin gidan anty salaha tana sake rushewa da wani sabon kukan mai cin rai.

Ganin shigowar ta tana kuka yasa anty salaha dake wanke wurin da tagama wanke wanke dakatawa da abinda takeyi ta nufi wurinta hankalinta atashe saboda duk zatonta ba kalau ba,

“Hanan…..meya faru kuma? Wanine ya mutu ko hatsari akayi? Ki fada ni abinda yafaru kin barni atsaye cikin zulumi…”

“Anty wai dama haka k’addara take? Idan ta afko maka kowa sai yajuya maka baya? Gaba daya sai ka kasa gane kan kowa? Wai haka k’addara take?”

Ajiyar zuciya anty salaha ta sauke sannan ta nemi wuri ta zauna nan cikin falonta tana kallon Hanan wacce har lokacin bata bar kuka ba,

“Hanan dan Allah ki dauki wannan auren amatsayin hanyar samun aljannar ki,ki dauka cewa wani nauyine iyayenki suka dora miki suke son ki sauke shi,kiyi hakuri dama shi aure mukaddari ne daga Allah,aduk inda mijinka yake sai yazo ya sameka anyi,kuma ke ki godewa Allah ma domin yayi miki gatan da ba kowa yayiwa ba,duk cikin danginmu da kawayenki babu wacce ta taba aurar babban mutum sai ke, minister fa Hanan,kin kuwa san suwa ake kira da minister? Wallahi ba kananan mutane bane…..”

“Anty ni babu ruwana da wani arzikinsa ni wallahi mujahid nake so,mujahid shine sa’an aurena shine yaro shine muka jima tare mun san halin juna mun san sirrin juna babu abinda bamu saniba na junanmu…..”

Sakar baki anty salaha tayi tana kallonta sannan cikin faduwar gaba tace,

“Hanan kar dai ko wani abu ya taba shiga tsakaninku da yaron nan..?”

Cigaba tayi da kukanta tana jin wayarta ana kiranta taki dagawa tasan bazai wuce mujahid ba,

“Tambayarki nakeyi,wani abu ya taba shiga tsakaninku?”

Girgiza kai tayi alamar a’a sannan taci gaba da kukanta,anty salaha zama tayi taci gaba yimata nasiha tana kwantar mata da hankali.

Dakyar ta daina wannan kukan ta share hawayen ta,wuni guda tayi agidan anty salaha har lokacin mujahid bai bar kiranta ba amma taki dauka yakirata yafi sau 20,sai magriba takoma gida,

Tunda ta koma kuma taci gaba da kuncinta har lokacin bacci yayi nan ta shirya ta kwanta bakin ciki kuma yace muje zuwa,saida taci kukanta ta share sannan ta dauki wayarta,

_Akwai Allah._ shine kadai abinda ta turawa Khalil ta ajiye wayar.

***

Yana kwance saman Rug da laptop agabanshi Aryan na gefenshi yana bacci yaji shigowar text,bai duba ba har saida yagama abinda yake yi sannan yadauki wayar yaduba ganin abinda tace yasashi girgiza kai sannan yasoma tura mata da reply,

_Nifa bawai yimin kikayi ba, kawai zan aureki ne saboda ki rike min yarona amma ni bakida wani abu da zai burgeni ko yaja hankali na atare dake infact ma ni banko san kamanninki ba bare insan ya kike,soo kisan inda yake yimiki ciwo._

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button