AFRA KO AMRAH HAUSA NOVEL

AFRA KO AMRAH 1-2

Da jijjihi kukan Afrah ne ya tashe su.
Farhan ne yayi saurin saukowa kan bed ya qarasa inda take ya dauke ta cikin hanzari ya nufi toilet da ita domin tayi fitsari sbd yasan ba abinda take ma kuka face fitsari sbd Afrah ta kasance yarinya wacce duk yadda take jin fitsari bata yin shi kan bed sai dai ta ajiye ma mutum kuka.
Bayan sun fito ne yayi zaune da ita kan bed,yayinda ta lafe kan jikinsa bacci na sake fizgar ta kadan kadan har ya fizge ta gabadaya.
Nan farhan ya shimfide ta wanda sai Allah Allah yake kar ta farka sbd so yake yaje masallaci lokacin sallah yayi.

Sai guraren qarfe tara Afrah ta farka daga bacci,lokacin farhan ya fito daga wanka kenan yana taje gashin kansa,
saurin kallon Afrah yayi wacce ke kuka irin nasu na yara idan sun tashi daga bacci
ganin idon ta a rufe yasa ya sauke ajiyar zuciya sbd yasan idan a bude suke da ta qyalla ido a kan shi ba makawa shine zai mata wanka gashi sauri yake sosai yana so ya hallarci meeting din da za a yi da qarfe goma,
kallon Amrah yayi wacce shigowar ta dakin kenan da alama daga kitchen ta fito sbd dauke take da trayn abinci,kallon da farhan ya mata ne yasa ta fahim ci me yake nufi nan ta ajiya tarayn da ke hannun ta ta nufi
Afrah cikin sauri ta dauke ta,
kafin Afrah ta bude idon ta har sun shiga toilet.

Koda suka fito basu sami farhan a dakin ba ya fita.
Amrah takai dubanta
gun break fast din da ta ajiye nan ta fahimci farhan ya dibi nashi kasancewar ba plate daya a cikin plates din ta ajiye.
Nan ta shafa ma Afrah Vaseline ta shirya ta cikin kayan sanyi kasancewar sanyin da ake sosai.

A 6anfaren farhan kuwa falo yaje ya zauna kan dining yana break fast sauri sauri.
Sai da ya kammala sannan ya koma gurin su amrah ya samu afrah kwance jikin pillow sai tsutsar babban yatsan ta take Amrah na riqe da plate din abinci sai faman lallashin ta take kan ta tashi taci abinci,amma mirsisi taqi tashi gashi tana jin yunwa sosai,ita ala dole farhan kadai ke bata abinci ta kar6a.
A hankali farhan ya qarasa gurin su ya zauna,Amrah ta ce “uncle nayi nayi taci abinci amma taqi”yace “dama nayi tunanin haka shiyasa naje na gaggauta yin nawa braek fast domin na samu na bata kafin lokaci ya qure min”
Yana gama fadar haka ya jawota kusa da shi ya shiga ciyar da ita har sai da ya tabbatar cikin ta ya cika.
Sannan ya bata ruwa ya tashi ya jawo suit din sa blue black in colour kallar wandon sa yayinda rigar sa ta ciki ta kasance milk haka talkalman da ke qafafunsa milk ne agogon hannun sa ma haka,briefcase din sa ya dauka hade da makullin mota,tare da fadin ni zan fita.
Nan Amrah ta tashi tare da daukar Afrah da niyar su raka shi farhan yace “a’a kuyi zaman Ku bana so taga shiga ta mota dmn na tabbatar kuka zata min sai naje da ita gashi bazai yiyu na shiga da ita taron meeting din da zamuyi sbd gabadaya likitawan state ne za a hadu wanda bansan iya tsawon lokacin da zamu dauka ba bare naje da ita na bayar a riqa min ita gun nurses,kuma gashi yau sanyi ake sosai hakan yasa nake so tayi zaman ta a gida”
Ya fadi haka ne tare da kallon agogon da ke hannun sa yaga 9:40am sannan ya maida duban shi gun afrah da ke kallon shi da alama so ta ke ya dauke ta,
bye bye kawai ya mata ya kama hanyar fita daga dakin wanda har ya bude qofar dakin ya jiyo sautin kukan ta,tsayawa yayi cak cike da damuwa sbd ko kadan baya son jin kukan ta musamman ma idan ya tuna cewa ita marainiyace kuma amana ce a gare shi.
Jiki sa6ule yaje ya kar6e ta yace bara na kai ta gun gwaggwo naga ko zata yarda ta zauna.

Nan ya fito ya nufi dayan 6angaren da muke sa ran nan ne 6angaren gwaggwor da ya ambata.

Da sallamar shi ya shiga ya same ta tana Karin kumallo ya russuna cike da ladabi ya gaishe ta sannan ya fadi buqatar shi na son Afrah ta zauna gurin ta har ya dawo.
Ba musu gwagwo ta miqa hannu domin ta kar6i Afrah,ai kuwa ta maqale kafada tana mai qara manne masa alamar baza ta je ba.
Gwaggwo tace dama shiru kawai nayi amma nasan baza ta yarda ta zauna ba kuma in banda abinka kai da kake zuwa da ita kullum yau kuma me ya kawo zancen baza ka je da ita ba?cike da damuwa ya nisa yace gwaggwo nima ba haka naso ba zuwan ne da ita ba zai yiyu ba kasancewar meeting din da zamuyi wanda tun jiya na sanar da ke irin di’n bin taron da za’ayi…..haka ne fa gaskiyar ka.
Nan ta kar6i Afrah wanda da qyar aka samu taje da kuka da komai har da su murmurje.
Farhan kuwa ya fita cike da rashin jin dadi har ya naji kamar da zai yiyu da ya fasa zuwa meeting d’in.

Futha Luv & Billy giro

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button