AFRA KO AMRAH HAUSA NOVEL

AFRA KO AMRAH 5-6

Yana cewa “wacce aka ce kurma ce ya akayi taji abinda Amrah ta fada har da su gyada mata kai”.

Nan dai ya basar da zancen ya nufi hanyar fita class din sbd hango malami da yayi zai shigo.

Da aka tashi daga makaranta JB yaje har class din su Afrah ya jawo hannun ta yaje da ita domin ganin wanda zai zo daukar ta.

Basu wani jima a tsaye ba sai ga motar farhan ta kunno kai,
Afrah na hango motar ta saki hannun JB ta tafi da gudu kan ta qarasa har farhan ya fito daga cikin mota ya qaraso da murnar sa ya tarbe ta.
Cike da murmushi JB ya qaraso gurin su yana fad’in “‘a’ah farhan na husna mai awara!murmushi farhan yayi mai cike da dariya yace”ka fara ko”JB yace to ai gaskiya na fad’a ya fadi haka ne yayin da ya riqo hannayen Afrah yana wasa da su yace ” a ina ka samo hadaddar yarinyar nan?kai JB Amanata ce fa ko ka manta da ita?oh sorry Allah ba mantawa nayi ba kawai dai ban ta6a ganin ta ba sae yau,
Farhan yace “haka ne fa inace yanzu ka ganta da kyau kar wata rana kace min baka gane ta ba…na isa bare a yanzu da ta zamo d’aliba ta, nan gaba kuwa mata ta zata zamo inshaAllah,,sosai farhan yayi dariya yace wace ce zata zamo matar ta ka?”Zarah mana” cewar JB wanda ya fadi haka ne yayinda ya nuna Afrah yaci gaba da cewa “ko baza ka bani auren ta ba?Farhan ya girgiza kansa yayinda yake ci gaba da dariya yace “JB baka rabo da abin dariya”JB yace “nifa da gaske nake yi daina kiran zancen da abin dariya”…hm to naji zaka iya jiranta kenan har ta girma?qwarai ma kuwa ai kasan idan ina son abu zan iya yin komai a kansa,farhan yace “to Allah ya nuna mana lokaci sae musha biki….bikin da ba a ta6a irin sa ba ma kuwa cewar JB yayinda farhan ya riqo hannun Afrah yace kaga mu zamu fice domin idan nace na biye ma zamu jima a nan,ni kuwa gashi bana so Afrah ta gaji da tsayuwa har taje ta fara jin yunwa,JB yace “ok a gaida gwaggo da kuma amarya Amrah kafin yake kallon Afrah yace”bye my wife,Allah nuna mana ranar auren mu”wanda hakan yasa farhan ya shiga mota yana dariya domin duk a tunanin sa da wasa JB keyi ga shi kuwa har ga Allah JB ke zancen.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button