JARUMA YAZILA COMPLETE HAUSA NOVEL

JARUMA YAZILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau – kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau – manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau – Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that – we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that – pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that – our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
JARUMA YAZILA
Littafi na biyu 2
Na Abdul’aziz sani madakin gini
Created and design by:- Shuraih Usman
Publishing shuraih Usman
From http://shuraih.waphall.com
.
Lokacin da jaruma yazila ta tambayi boka musrid
bn Affan dalilin da ya sa takasa cire wannan laya
daga wuyanta da kuma yadda zata iya rabuwa da
ita sai ya yi ajiyar nunfashi sannan yai shiru ya
sunkui da kansa kasa cikin halin tunani tsawon
lokaci mai tsawo yana tunani baice komaiba daga
can sai ya dago kai ya dubeta cikin tsananin
damuwa sannan yace ya ke jarumar jarumai ki yi
sani cewa yau kin tambayeni babban al amari
wanda yafi karfina domin idan na ce zan matsa
bincike bisa wannan al amari zan iya rasa
rayuwata. Ita dai wannan laya ta wuyanki tun
kina jaririya mahaifinki Barzuk ya sanyata a
wuyanki kuma duk ranar da kika sami damar
cireta a ranar ne zaki sanwani babban sirri
dangane dake kanki da kuma mahaifinki da sarki
daksur har kiyi arba dashi in kuwa kika yi arba da
shi duk irin sihirin tsafin da yake da shi saikin
sameshi. Ina tabbatar miki da cewa duk duniya a
halin yanzu babu wanda zai iya cire maki wannan
laya face abokiyar gabarki dabira ta birnin misra.
Sa’adda boka mushrid yazo nan a zancensa sai
jaruma yazila ta cika da tsananin mamaki kuma
zuciyarta tayi bakikkirin ta dubi boka mushri ta
ce, “yanzu ashe ke Nan akwai wani babban sirri
dangane da rayuwata wanda ma haifiyata da
mahaifina suka boye mini?”
Boka mushrid yace kwarai kuwa akwai wannan
sirri kuma kada kiga Laifinsu domin sanar dake
bazai haifar da komaiba face tsananin ta shin
hankali agareki baki daya.
Koda jin haka sai hawaye ya zubowa jaruma
yazila tace, “Ai kuwa a yau dinnan sai na tambayi
mahaifiyata wannan al’amari ko menene zai faru
kuma zan yi shiri na tafi birnin misra wajen
abokiyar gabata jaruma dabira domin na san
dabarar dazan yi tacire min wannan sarka bare
bata saniba. “
Cikin firgici boka mushrib ya kama kafadun
jaruma yazila yace, “yake jarumar jarumai, kiyi
sani cewa abinda kike shirin yi tamkar ki aza
gammo ne a kanki kice zaki dauki duniyar nan
gabaki daya ina mai shawartar ki da ki hakura
dayin wannan abu domin a karshe allura ce zata
tono garma.”
Koda jin haka sai yazila ta mike tsaye zumbur! A
fusace tace, “ya kai wannan amintaccen bokana
kayi sani cewa babu wani abu da ya isa yahanani
yin waddannan abubuwa guda biyu face mutuwa
kuma yanzu_Yanzu zan tafi na fara gabatar dasu
.” Koda gama fadin haka sai yazila ta juya ta fice
daga daga gidan boka mushrib tana isa kofar
gidansu tayi kicibis da boka mushribtsaye
gabanta fuskarsa a murtuke babu annuri.Mushrid ya dubi yazila yace, “bazan barki kije ki
ai’watar da wannan al’amariba domin nifa zaki
jefani
cikin masifa da bala’i”.
Yazila tayi murmushi sannan tace, “kayi sani
cewa dan
zaki yagirma banga ta yadda zaka iya hananiba,
idan
kuma kana ganin zaka iya toka jarraba”.
Gama fadin hakan ke da wuya sai ta yun kura da
nufin
ta wuce ta gabansa. Take mushrid yayi nuni da
hannunsa izuwa gareta sai wata irin murtukekiyar
sarkar tsafi ta kanannadeta tun daga kan
kafafunta har
zuwa kanta ta daureta tamau, idanunta da
fuskarta ka
dai ake gani. Yazila ta girgiza jikinta don ta
tsinke
sarkar amma ta kasa kwancewa. Koda ganin
haka sai
boka mushrid ya bushe da dariyar mugunta yace
“kika
ce dan zaki yagirma kodai dan kyanwane?” Yazila
ta
kyalkyale da dariya sannan ta ce, tabbas dan
zakine
wannan ba dan kyanwa bane. “
Kafin boka mushrid ya kara cewa wani abu sai
yazila
ta ambaci wata kalma daya daga cikin da
lasiman tsafi.
Nan take wannan sarkar tsafi ta narke tazama
ruwa.
Kafin boka mushrid ya yi wani yun kuri tuni yazila
ta
fincikoshi da hannu daya tayi hajijiya da shi a
sama ta
fyada shi da kasa kuma tatake masa wuya da
kafadaya
ya fara kakarin mutuwa.
Yazila ta dauke kafarta guda daga kan boka
mushrid
tacce, “kaci albarkacin kyautatawar da kayimin
abaya
da yanzu zan kasheka. Kasani cewa dokata ta
farko.akan kowa itace, ba ayimini dole, kuma idan
nabada umarni ba a ketare shi daga yau idan ka
sake
saba wannan doka zan kau da batun mutunci
dake
tsakaninmu na yi maka hukunci dai-dai da
laifinka. “
Koda gama fadin haka sai jaruma yazila tayi
girgiza ta
bace bat ! Tamkar bata taba wanzuwaba a
wajen.
Al’amarin daya matukar baiwa boka mushrid
mamaki
kenan ya bita da kallo ka wai zuciyarsa cike da
wasa-
wasi yana mai cewa, “yaya akai yazila ta sami
wannan
sihirin tsafin mai karfi haka ? Abinda bai sani ba
shine, yazila ta ziyarci manyan bokayen duniya ta
sami sirrikan tsafi da yawa. Wadan da suka
finasa. “
Lokacin da jaruma yazila ta isa gida sai ta iske
mahaifiyarta nuzaira zaune a turakarta. Ko
masana
yazila bata mataba sai ta wuce kai tsaye izuwa
cikin
turakarta, al’amarin da ya matukar baiwa nuzaira
mamaki kenan domin a duk sa’adda yazila ta
dawo
gida da gudu take shigowa turakarta, ta
rungumeta
cikin farin ciki ta sumbaci goshinta.
A rayuwar jaruma yazila babu take kauna sama
da
nuzaira ko kadan bata son taga abin da zai sosa
mata
zuciya, haka kuma duk abin da nuzaira ta umarci
yazila tayi sai tayi shi bata taba yimata gar
dama.
Bayan yazila ta shige cikin dakinta sai nuzaira ta
mike
tsaye ta kira wata kuyanga mai suna rafina wacce
itace
ke kula da komai na yazila ta ce da ita taje ta
kawo
mata abincin yazila. Cikin mamaki rafina ta dubi
nuzaira tace , “ya shugabata ai yanzu zan je na
kai
mata abincin”. Nuzaira tace yau ni da kaina nake
son
na kai mata”
Koda jin haka sai rafina ta juya da sauri tatafi
dakin
girki ta dakko abincin yazila bisa faranti ta
kawowa
nuzaira ita kuma ta karba ta tafi dakin yazila “.
Yazila na zaune bisa gefen gadon ta tayi ta gumi
cikin
halin tunani mai zurfi. Ka wai sai taji anturo kofa
an
shigo. Yazila ta dago kai da sauri tayi arba da ma
haifiyarta Nuzaira kawai sai ta kau da kai ga
barin
kallonta ta sun kui da kanta kas. Cikin sanyin jiki
nuzaira ta matso daf daf da yazila ta ajiye
farantin
abincin wani benci karami sannan ta zauna bisa
wata
kujera dake fuskan tar yazila ta dafa cinyoyin
yazila
tace, “yake ‘yata yau kuma wanene yabata miki
rai a
waje har da fushinsa zai shafeni?” Koda jin
wannan
tambaya sai hawaye ya zubowa yazila ta kasa
cewa
komai. Al’amarin da ya matukar razana Nuzaira
kenan
ta cika da tsananin mamaki. Kawai sai yazila ta
kama
hannun nuzaira ta dora akanta tace, yake
mahaifiyata
ina son ki yi ran tsuwa bisa dara jar kaunar dake
tsakaninki dani ki gaya mini gaskiyar al’amarin da
zan
tambayeki a yanzu. Kisani cewa idan kika gaya
mini
sabanin gaskiya kuma na gano hakan anan gaba
lallai
zan kashe kaina domin ban ga amfanin
rayuwataba a
duniya tunda wadda na aminta da ita fiye da
kowa
bata aminta daniba”.
Cikin rudewa Nuzaira tace mene ya kawo duk
wannan
al’amarin haka yake ‘yata ? Shin wani ne yace
akwai
abu dana buye miki ?” Yazila ta share hawayen i
danunta tace, “dafarko ina so n’ki gaya mini
asalin
wannan layar dake wuyana da kuma dalilin da
yasa
aka sakamin ita. Ina son ki gaya mini sirrin dake
tare
da rayuwata da taki. Na ran tse da darajar
soyayyar da
nake miki idan kika boye mini gaskiyar al’amari
bazan
taba yafe miki ba “
Sa’adda Nuzaira taji wannan tambaya sai tacika
da
tsananin mamaki bisa abin da ya janyo yazila
tayi
mata wannan tambaya.
Nuzaira ta dubi yazila tace, “mene ne dalilin daya
sa
kika yi mini wannan tambaya?”
Koda jin haka sai yazila ta kwashe labarin duk
abin da
ya faru tsakanin ta da boka mushrid ta zaiyane
mata.
Sa’adda nuzaira taji wannan batu sai han kalinta
ya
dugunzuma ta dubi yazila tace, “yake ‘yata
hakika yau
kin zomini da babban al’amari don haka yana da
kyau
ki bani lokaci. Isasshe nayi tunani tukunna. Yanzu
dai
ina son ki kwantar da hankalinki sannan kici
abincinki
inyaso nan da wani lokaci na dawo gareki muci
gaba
da wannan magana”.
Har nuzaira ta mike tsaye zata fita daga dakin
sai
yazila taruko hannunta ta zaunar da ita alokacin
da
hawaye yaci gaba da zuba akan kumatunta.
Yazila tace,
“ya ke Ummina ina tabbatar miki da cewa idan
baki
bani amsar tambayata a yanzu ba ba zan kara
cin
abinci ba a rayuwata sai dai yunwa da kishirwa
su
kasheni”.Koda jin haka.sai hankalin nuzaira ya kara
dugunzuma fiye da ko yaushe domin ta san halin
yazila duk abin da ta ce za ta aikata bata fasawa
kawai sai yaZila ta ga hawaye ya zubowa nuzaira
sannan kuma ta fashe da kuka al amarin. Da ya
matukar dugunzuma hankalin yazila kenan taji ta
yi nadamar matsawar datayi mata a kan wannan
tambaya batare da nuzaira tace komai basai
tamike tsaye taje ta kulle kofar dakin sannan ta
kulle tagogin dakin ta dawo daf da nuzaira ta
zauna ta fara ba ta labari tun daga lokacin da
hukairu da humaira suka yi hijra daga kauyen
himsarul aswad suka koma can da birnin kisra
suka cigaba da rayuwa kawo izuwa lokacin da
nakuda ta kamata ta tafi can inda su humaira ta
haifi yan mata tagyaye ta dauki daya ta bata ta
dawo wajen mijinta barzuk suka koma cikin birnin
kisra da zama da duk irin dokokin da sarki daksur
ya kafawa jaririyar har barzuk ya kawo wannan
laya aka sanyawa jaririyar a wuyanta.
Lokacin da nuzaira ta gama baiwa yazila wannan
labari sai yazila ta fashe da matsanancin kuka
kamar baza ta daina ba. Kuma tacika da matukar
mamaki da bakin ciki da kyar da sidingoshi
nuzaira ta rarrashi ta tadaina kukan sannan ta
roketa akan tabar wannan magana a zuciyarta
domin idan tace zata dauki wani mataki akan
barzuk da sarki darkus bazata sami galababa.
Yazila ta gyada kai cikin matukar takaici sannan
tace yake ummata kiyi sani inda na san cewa
niba yarki bace bazan tsaya nayi yaki da
muyanen birnin misra ba tsawon shekaru kuma
ina tabbatar miki da cewa lallai sai na sami
nasarar cire wannan laya daga wuyana kuma
komai dadewa sai naga bayan mijinki da sarki
daksur. Domin sun kasance azzalumai kuma bara
gurbi a doron kasa shin yanzu kina da labari yar
uwarki humaira da yar uwata dake tare da ita ?“
Koda jin wannan tambaya sai nuzaira tayi ajiyar
zuciya tace ai rabona da su tun sa adda na rabu
da su a can gidansu daji amma na taba ji a bakin
sarkin yakin garin nada wato sadauki zaihar cewa
hukairu da humaira tare da yarsu sun gudu izuwa
birnin misra amma ya bisu har ya riskesu kafin
su shiga birnin har ya fafata yaki da mahaifin
naki hukairu ya sami nasarar kasheshi amma bai
sami damar kashe humaira da yar uwarki ba
domin dakarun birnin misra ne suka yiyo kansa
ya gudu ya yin da yazila taji haka sai zuciyarta
ta kama tafarfasa kamar za ta kone tace yanzu
sarkin yaki zaihar ne ya kashe mahaifina ?“.
Nuzaira tace tabbas haka ne babu shakka “
yazila kuwa indai makaifiyata da yar uwata suna
raye tabbas suna cikin birnin misra ni kuwa ta
kowanne hali sai na shiga birnin misra ni kuwa ta
kowanne hali sai na shiga birnin misra na sadu
da su dama ina da burin naje na sadudA jaruma
dabira domin ta cire mini wannan laya dag
wuyana kuma ina son muyi yakin karshe da ita
domin nasami damar kaita kas har na cire hular
karfen da take sawa a kanta domin naga fuskarta
kin ga kenan ina da manyan bukatu har guda uku
acikin birnin misra don haka zama bai kamani ba
dole ne nayi shiri na tafi birnin misra”.
Koda jin wannan batu sai hankalin Nuzaira ya
dugun zuma ta dubi yazila cikin firgici tace, “yake
‘yata kin sani cewa mutanen birnin misra sun
kasance ma’abota addinin muslunci saboda haka
zuwanki birninsu abu ne mai hadarin gaske da
zarar sun ganki zasu hallakaki tun da kin kasance
tsohuwar abokiyar gabarsu. Ki tuna cewa kin
kashe musu jama’a ba adadi. A bu na biyu koda
‘yar uwarki da mahaifiyarki suna nan araye yanzu
kodai suna kurkuku kokumaa suma sun zama
musulmai don haka baza suyi mar haban da keba
tun da kun banbanta addini da yanayin rayuwa.
Ke koma dai babu banbancin komai ai baza
sutaba shaidakiba tun da basu sankiba kema baki
sansuba. Shekara goma sha takwas ai ba kwana
goma sha takwasbane. Na tabbata yanzu ‘yar
uwata Humaira ta tsufa, kamar yadda nima na
tsufa, ta yaya zata shaidaki alhalin rabonta da ke
tun kina jaririya?”.
Lokacin da nuzaira ta zo nan a zancenta sai
yazila ta mike tsaye ta kama kai kawo sannan ta
tsaya cak ! Ta dubi nuzaira tace, “yake ummina ki
sani cewa dan uwa-dan uwane, har abada idan
ka hada jini da mutum sai kaga wani abu ya
zamo iri daya da nasa bare kuma ni da ‘yar
uwata mun kasance tagwaye ai dole ne asami
kama ni da ita kamar yadda kika bani labari cewa
tamkar an tsaga kara muke. “
Nuzaira tayi ajiyar zuciya sannan tace, “nidai na
umarceki da kada ki kuskura kice zaki ce zakiyi
wannan ta fiya izuwa birnin misra kuma ina mai
gargadinki da kada ki kuskura kice zaki je kiyiwa
sarkin yaki zaihar wani abu, domin kina tabashi
mijina da sarki daksur zasu gane cewa na sanar
dake sirrin rayuwarki don haka komai zai
iyafaruwa a gareni. Yake yazila ki tuna cewa nice
na shayar dake harkika girma kika zama mutum,
ki tuna nice naci kashinki, na sha fitsarinki, kuma
nice na sha wahalar renunki idan kika bari su
sarki daksur suka cutar dani lallai kinci amanata
kuma kinci amanar zumuncin dake tsakanina da
mahaifiyarki.”
Koda gama wannan jawabi sai nuzaira tayi shiru
bata kara cewa komai ba , sannan ta mike tsaye
ta fice daga cikin dakin ta bar jaruma yazila a
zaune cikin tsananin damuwa, gami da tunani
mai zurfi.Haka dai yazila taci gaba da sake-sake acikin
zuciyarta ta kulla wancan ta kwance wancen har
dare yaraba ya zamana taka sayin barci sai kai
kawo kawai takeyi acikin dakin nata tana zarya.
Bayan tayi dogon nazari da tunani akan abinda
zai fishsheta sai taje ta dakko takadda da
alkalami ta rubuta wata wasika ta ajiye a
karkashin matashin kanta sannan ta cire kayan
jikinta ta sanya wadansu bakaken sulke na yaki
ta dauki makamanta na yaki ta soke a jikinta nan
take tayi girgiza bace bata bayyana ako ina ba
sai a kofar gidan sarkin yaki zaihar da baiyanarta
sai taga masu gadi a tsaitsaye suna kan aikinsu
kai tsaye jaruma yazila ta durfafosu koda masu
gadin suka hangota sai suka cika da tsananin
mamaki bisa ganinta a cikin wannan lokaci na
tsawon dare cikin ladabi da biyayya masu gadin
suka risina suka gaisheta yazila ta dubeshi a
fusace tace kubude mini kofa da salama na shiga
dfomin naga mai gidanku idan kuma kuka yi
gardama yanzun nan takobina zata sha jininku !“.
Koda jin wannan batu sai jikin masu gadin ya
kama karkarwa cikin firgita sukayi sauri suka
bude mata kofar ta kunna kai ciki da shigar yazila
cikin gidan sai tazare takobinta taci gaba da
kutsa kai tana leka cikin dakunan gidan domin
taga inda sarkin yaki zaihar yake. Karar zare
takobin yazila daga cikin kubbenta ne yasa
sadauki zaihar ya bude idanunsa alokacin da
yake kwance tare da matarsa acikin turakarsa
dama bai dade da kwanciya ba bisa bata lokaci
da yayi wajen bincike a hallarar tsafinsa. A cikin
binciken da yayi ya ga wata gagarumar masifa
dake shirin afko masa amma sai ya kasa gane
irin masifar da kuma lokacin dazata zo masa abin
da ya saya kasa barci ke nan ya kwanta kawai
yana tunani cikin fargaba. Koda zaihar yaji karar
zare wannan takobi sai yayi wuf ya mike daga
kan gadonsa yayi sauri yasanya kayan yakinsa
sannan ya zare tasa takobin ya fita waje yana
neman wanda ya shigo masa gida cikin wannan
tsohon dare.
Lokacin da jaruma yazila ta shigo cikin wani
katon falo na gidan wanda babu komai acikinsa
face shimfidar jan kilishi mai taushi da kujeru na
alfarma sai tayi kicibus ! Da sarki yaki zaihar
tsaye ruke da takobi a wannan lokaci falon a
haskake yake dahasken fitilu tazarar dake
tsakanin zaihar da yazila bata wuce taku asirin
ba.
Koda zaihar ya ga ashe yazila ce ta shigo masa
gida acikin wannan dare sai ya cika da tsananin
mamaki kuma yaji ajikinsa cewa lallai ba lafiya ba
akwai wani abin daya faru da dai dai ba saboda
haka saiya tsaya a inda yake ya dubeta yace
yake halifata mene ne ya kawoki gidana a
wannan dare?“ Yazila ta dubi zaihar a fusace
tace ,“ nazo na dauki fansar mahaifina dakakashe
ne ya kai babban azzalumi !“
Cikin matukar mamaki zaihar ya dakawa yazila
tsawa yace ,” wannan kuma wacce irin maganar
banza kikeyi ? Shin ke ba yar mai girma barzuk
bace ? Yaza ayi kice na kashe mahaifinki alhalin
barzuk na nan araye ?”.
Dajin haka sai hawaye ya zubowa yazila tace ”
Kayi tunani izuwa shekaru goma sha takwas baya
lokacin da kabi bayan hukairu dan uwan barzuk
sa adda ya gudu tare da iyalinsa izuwa birnin
misra daf da kofar birnin misra kuka fafata yaki
kai da matarsa humaira tan goye da jaririyarta to
ka sani cewa wannan jaririr yar uwata ce mun
kasance tagyaye nida ita kuma hukairu ne ya
haifemu ita kuwa nuzaira abin data haifa mutuwa
yayi sai humaira taba ta daya daga cikin
tagyayen data haifa kuma ni ce jaririyar da aka
bata kagake nan hukairu shine mahaifina ba
barzuk ? Lallai mahaifina ka kashe , babu
makawa sai na dauki fansa a kanka kuma a
yanzu ”.
Sa adda yazila tazo nan a zancenta sai sarkin
yaki zaihar ya bushe da mahaukaciyar dariya. Ya
ce ” yake yarinya karyarki tasha karya. Ba a
zama wane a banza. Kafin na sami wannan
matsayi na sarkin yakin birnin kisra sai dana taka
mukamai masu daraja da yawa kuma sai dana
sha bakar wahala. Duk abin da kike takama da
shi a yanzu na mallakeshi tun kafin kizo duniya
saboda haka yanzu ga fili ga mai doki idan kina
ganin zaki iya daukar fansar mahaifinki ki jarraba
ki gani ina tabbatar miki da cewa kamar yadda na
kashe mahaifinki haka kema zanka sheki !”.
Kafin zaihar ya gama wannan jawabi tuni zuciyar
yazila ta fara tafarfasa kawai sai ta dag takobinta
sama ta ruga gareshi shima sai ya daga tasa
sama ya rugo gareta suna haduwa kowanne su
ya kaiwa dan uwansa mugun sara kowannensu
ya kare saran da takobinsa da takobinsa tara
tsatsin wuta ya fantsama izuwa kas. Nan fa suka
rugunzume da azababben yaki ya zamana cewa
suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin
nama juriya da bajinta.
Wohoho ! Idan sabon hannu da tsohon hannu
akahadu a gumurzu dolene aga tsagwaran
jarumta t ban al’ajabi. Ita yazila tana ta kama da
kuruciya gami da sadaukan taka ta zamani
shikuwa zaihar yana ta kama da kwarewa da
sanin makama ne. Da dabarun yaki irin na
tsofaffin sadaukai inda aka sami babban
bambanci shine, ita yazila tafi zaihar juriya da
dadewa ana gumurzu, shi kuma yafi ta zafin
nama.
Sai da aka shafe rabin sa’a ana wannan gumurzu
dayansu bai sami na sarar komai ba, ya zamana
cewa dauki ba dadin da sukeyi yasa gaba daya
hadiman gidan sun rugo izuwa falon da suke
fafatawa a dimauce. Itama matar zaihar saita
farka daga bacci a firgice ta ruga izuwa dakin da
danta ke barci, wani karamin yaro dan shekara
hudu kawai, saita sungumi yaron a kirjinta taruga
izuwa falon da ake gumurzu tsakanin yazila da
zaihar.
Dazuwa sai ta iskesu cikin masifaffen artabu.
Gaba daya hadiman gidan sun ra kabe a tsorace
suna kallon abin dake faruwa. Nan fa itama
matar zaihar ta kasa yin komai saita tsaya ka
wai tana kallon fafatawar cikin tsananin tsoro da
fargaba da mamaki bisa ganin wacce ke gumurzu
da mijinta.
Saboda zafin naman zaihar sai ya shammaci
yazila ya yanketa acinya. Kafin tayi wani yunkuri
ya sake yankarta a damtsen hannunta na hagu.
Bisa dole yazila tayi alkafira da baya ta koma
nesa kadan da shi ta durkushe kasa bisa
guiwowinta a lokacin da ta dafe raunikan jikinta
biyu cikin jin zugi da radadi.
Koda taga jini na zuba saita fusata ainun kuma
tayi sauri. Ta daure raunikan da wani tsumma
dake daure a kugunta. Ka wai sai ta mike tsaye
ta sake zare wata takobin a kuibin cinyarta ta
hagu ya zamana cewa ta hada takubba biyu
ahannunta.
Koda ganin haka sai shima zaihar yaciro wani
gatari dake rataye a bayansa ya hada da ta kobin
hannunsa ya fuskanceta. Kawai sai yazila ta rugo
gareshi suka sake kacamewa da sabon
azababben yaki amma awannan karon sai yazila
ta sauya salon fadan ya zamana cewa tana tsalle
tana alkafira a kasa da sama. Nan da nan kuwa
ta ruda zaihar, bai ankara ba sai yaji ta dan kara
masa sara acinyarsa. Take wajen ya dare jini yayi
tsartuwa. Zaihar ya rankwala uban ihu yatafi da
baya taga-taga ya fadi
Koda matar zaihar taga abinnda aka yiwa mijinta
zaihar sai itama tarusa ihu ta fashe da kuka.
Yazila ta kara rugowa da gudu izuwa kan zaihar
ta ci gaba da kaimai sara da suka cikin iya zafin
namanta bata yarda ta bashi damar da zai daure
raunin nasaba. Nan fa jini ya cigaba da zuba
daga cinyar zaihar har jiri yafara dibarsa amma
saboda naci da juriya irinta ‘YAN MAZAN JIYA sai
yaci gaba da yakin a haka. Ya yin da zai har ya
fus kanci cewa idan akaci gaba da wannan
gumurzun a haka har izuwa wani lokaci mai
tsawo zai iya gala baita yafadi saka makon jinin
dake zuba a kafarsa sabo da haka sai ya fara
amfani da karfin sihirinsa yana watsawa yazila
mugayen abubuwa kamar; masu, wuta, kibiyoyi
da sauransu. Bisa mamaki sai yaga tsafin baya
tasiri ajikinta, domin karfin sihirin nasu yazo daya
duk abin da ya watsa mata sai itama ta watso
masa irinsu sulalata juna. Al’amarin daya
dugunzuma hankalin zaihar kenan ya tabbatar da
cewa bashi da wata mafita face yayi amfani da
iyakar karfin dmtsensa da kwarewarsa ta yaki.
Bisa dole yakara ZAGE DAMTSE suka cigaba da
bakin gumurzun, yazamana cewa ta shi hankalin
komai da kowa dake cikin falon. Sai da suka
shafe sa’a biyu suna wannan gumurzu ya
zamana cewa kowannensu yasake samun nasarar
yiwa abokin gwamisa rauni. Zai har ya sami
nasarar saranta a kirji, ita kuma ta sami nasarar
sokarsa agefen kirjinsa na dama alokaci guda duk
subiyun suka kwala ihu suka ja da baya taga taga
kamar zasu fadi amma sai suka sake rugowa
suka kacame da a zababben yaki.
Hakika idan mutun ya ga irin wannan juriya, naci
da jarumta irin ta zaihar da yazila dolene ya
jinjina musu ya tabbatar da cewa sun cika
zaratan sadauki ababan misali. Bayan sun dada
kwarmazuwa bisa hadawa da naushi da bugun
juna sai suka jigata ainun ya zamana cewa da
kyarma suke kaiwa juna hari.
Duk wannan abu dake faruwa matar zaihar na
rakabe a gefe daya rungume da danta ta na
kallongumurzu cikin ta shin hankali kuma tana
kuka.
A na cikin wannan fafatawar ne duksu biyun sukA
yiwa juna wani irin mugun naushi a fuskokinsu
har jini yai tsartuwa bakunansu suka zube kasa
kafin yazila tamike tsaye sai zaihar yayi sauri ya
zaro wata wuka siririya mai kaifi da atsini ya
wurgawa yazila wutar da tafi tsananin gudu zata
cake ta cafi wukar ta maida ita inda aka jehota
nan take tsinin wukar ya lume acikin goshin
zaihar nan take zaihar ya sulale kasa matacce
koda ganin abin daya faru sai matar zaihar ta
kwala ihu ta rugo kan gawar mijinta ta ajiye
danta a gefe daya ta rungume gawar tana kuka
sauran hadiman gidan kuwa sai suka firgice suka
kama guje guje suna ficewa daga cikin gidan
gaba daya jaruma yazila ta yaka kafafunta da
kyar ta nufi inda matar zaihar take koda ganin
haka sai matar zaihar ta dago kai ta dubeta ba
tare da tsoron komai ba tace.” Yake dirkar birnin
kisra ma za ki kasaro ki kasheni ni da dana
domin na huta da wannan abin takaicin da kika
bar mini ban ga amfanin rayuwarmu a duniya tun
da kin yanke mana farin cikin rabamuda
masoyinmu. ”.
Yazila tayi shiru bta ce komai ba har ta iso kan
gawar zaihar kawai saitasa hannunta ta zare
wannan wukar wacce ta lumamai acikin goshin
zaihar sannan ta dubi matarsa a lokacin da
hawaye ya zubo mata. Tace ina bukatar alokacin
wannan wuka domin da sonki san cewa bazan
kashe kiba kuma bazawara kamar yadda uwata
humaira ta zama bazawara kuma inason wannan
da naki ya zama maraya kamar yadda ni da yar
uwata muka zama marayu ina son ki isar da
sakona ga sarki daksur cewa ni “jaruma yazila ”
na kashe sarkin yaki zaihar bisa sanin cewa shi
ne ya kashe mahaifina na gaskiya bisa umarninsa
don haka ya saurari ranar da zanzo daukar fansa
a kansa ki sanar dashi cewa na san sirrin layar
da suka rataya mini a wuya tun ina jaririya kuma
na tafi inda za ayi cire mini layar koda gama
wannan furuci sai jaruma yazila ya goge jinin
dake jikin wannan wukar daga jikinsa ta daura a
kugunta kawai sai ta juya ta fite daga cikin
gidana tana tafe tana tangadi ita kuwa matar
zaihar sai ta bita da kallo kawai cikin tsananin
mamaki bisa jin abubuwa data zaiyano mata a
matsayin sako sarki daksur.

1 2 3Next page

Leave a Reply

Back to top button