AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 17-18

??17 and 18??

Via OHW????

tunda sassafe natashi, naci gaba da rubutuna,
babu abinda yachanza game da chart dinda Ameela takeyi, amma dai jiya bata samu damar chart din dareba,

Ko yau hilal bai tsaya karyawa cikin gidan ba, wanka kawai yayi yadauki jakarsa yawuce gurin aikinsa,

Bayan fitar hilal ta dauki wayarta tayita chart domin bata aikin komai, sabuwar kawarta data samu wato anisa sunyi chart yau mai dadi kuma hartayi save din number ta domin taga anisa tana da kirki sosai, duk wadan da tacewa zasu hadu shabiyun dare jiya, tabashi hakuri tace musu baccine ya dauketa, bata farkaba sai safe… Kujimun karya irin ta Ameela,
*
A WANI GIDA

Wata wainar ake toyawa,

A Falo suke zaune sunyi jugum jugum, suna jiran amsar daga bakin AFHAM,
Afham yayi shiru ya sunkuyar da kansa kasa, yakasa magana

kawu bello yace “magana muke maka Amma kayi mana shiru, shin kanason AMAL ko kanada wadda kakesone”

Afham ya girgiza kai “aa kawu babu wadda nakeso amma kuma kawu maganar amal dince..”

Abban afham dayake zaune a gefe haushin afham yakamashi yayi saurin cewa “maganar amal dince.. To fada mana, abban afham yajuya ya kalli kawu bello yace “nifa kaine kake masa ta laluma, mumuka haifesa koshine ya haifemu, kagafa saboda gudun irin wannan matsalar yasa naki barinsa yayi karatu anan naija, nakaisa cen waje saboda karya taso ya bijirewa umarninmu, nifa nafada wannan auren shida Amal saifa anyisa domin wannan burin mune tun muna yara”

Kawu bello yace “a a yaya karka yiwa yaron nan abinda bayaso, yanzu dai abarshi yaje yayi shawara, kawu bello yajuya gurin afham yace ” tashi kaje kayi shawara zamu nemeka” Afham yatashi ransa abace, shiba macceba amma ace za’ai masa auren dole, shifa baya son Amal dinnan,
Haka dai yashiga dakinsa zuciyarsa cike da wasi2 kala2,
Ya zauna gefen gado yayi jim yana tunanin wani abu saikuma yatashi yafito, yanufi dakin kanwarsa ANISA wadda akoda yaushe itace abokiyar shawararsa,

Akwance yasameta saman gado, Tana dannar waya, yayi sallama sannan yashigo dakin,

Dago kanta tayi tana murmushi ta amsa masa sannan yanemi gure a gefen gado yazauna yadan saka murmushi ” chart kike koh, bakida aiki sai chart,.sai ciwon chart yakamaki”

Anisa tayi dariya sosai “la yaya harda wani ciwon chart akwai ne”

Afham yace “sosai ma idan mutum ya nace akan chart to chart zaibi jikinsa mutukar baiyi saba to bazaiji dadi ba”

Anisa tace “toh wannan likitancin kane yaya, anisa tatashi zaune tace “ai nama gama chart din daman wata sabuwar kawace nasamu wallahi yaya karka ganta ta hadu kamar ita tayi kanta,

Anisa tashiga gallery cikin Whtsapp prfil pc takai ga photon ameela tatsaya “kaganta yaya, sunanta ameela, kamar baindiya” tamikawa afham wayar, yakarba, dam yaji gabansa yafadi a lokacin dayayi tozali da kyankywar fuska ameela, sak irin yadda yake neman macce dakyau da diri da kuma kyakkawar surar jiki,
Anisa tana gefe tana dariya ganin yadda afham yakurawa photon ido,
Kamar daga sama taji muryar ummanta tana kiranta, dasauri anisa ta karasa bakin gado tasaka takalminta, tayiwa afham alama da hannu “ina zuwa yaya,.bari nazo musa labule idan yarinyar taimaka,” takarasa maganar cike da zolaya dakuma dariya,

Afham gabaki daya pic din yatafi da imaninsa, lumshe ido yayi sannan yasake budewa, tabbas yasamu irin maccen daya jima yana nema, wadda tajima tana zomasa a mafarki,

baimasan da fitar anisa ba yajuyo yayi yana waige waige ganin bata cikin dakin yasa yayi saurin fitowa da wayarsa yashiga xender yatura pic din, sannan yashiga Whtsapp yaga number da aka rubutawa ameela, da sauri yadauki number yayi save a wayarsa ya ruba mata ZABINA,
Sannan yajiyewa anisa wayarta a kan gado yafita yakoma dakinsa,
Akan kado yakwanta yakamo pic din ameela yana kallo yana maimaita sunan a bakinsa, yaa lumshe ido sunan da surar jikinta duk sun masa, tabbas ya yayi gamu da katar kuma yanzunne zai samu damar tunkarar su kawu bello da abbansa yafada musu cewa yasamu wadda yakeso, matukar wadda yake gani a pic dinnan ta aminta dashi, duk azuci yake fadan wadan nan maganganun, a fili kuwa tambayar kansa yake, to ta ina zaifara….

Hmm akwai chakwakiya kenan.. muje zuwa

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button