AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 1-2

HILAL yasa hannu ya yashe mayafin dayake kan AMEELA, yana murmushi ya kura mata ido, Ameela ta mayar masa da amsar murmushinsa,
Hilal ya lumshe edo cike da godiyar yau dai Allah ya cika masa burinsa, ya mallaki Ameela a matsayin matarsa,
Bayan sun share sama ga shekara biyu suna soyayya cike da farin ciki da kuma kaunar juna,
Hilal yaja nunfashi yace “godiya ta tabbata ga Allah subahanahu wata ala, daya nuna mana wannan ranar mai cike da farin ciki a garen mu, kuma Ina kara gode masa daya mallakamun wacce a koda yaushe nake kiranta da cikar burina, hilal yayi ajiyar zuciya sannan ya kara duben Ameela yanai mata murmushi yace “bakice komaiba”
Murmushi Ameela tayi tana kallonsa tace “banda abinda zance a yanzu saidai inyiwa Allah godiya daya nunamin wannar ranar ta aurena, domin burin ko wace ‘ya macce shine taga ranar aurenta, toni yau naga tawa, tayi shiru suka jima suna kallon juna cike da farin ciki da kuma nishadi,
Ameela tayi gyaran murya, hakan yasa hilal yadawo hayyacinsa,
Ameela tayi murmushi tace ” yanzu nazama mallakinka, kuma nazamo matar ka, Dan Allah karikeni Amana karkaci AMANAR AURE”
Halal yaja nunfashi cike da jindadin kalaman amila yace “ki kwantar da hankalinki, Ameelata bazan taba cutar dake ba, kuma nayi miki alkawari kece kadai mata a nan duniya, kuma bana fatar wani sabani yashiga tsakaninmu” Ameela tace “nima haka, kuma Allah yabarmu tare har mutuwa”
Hilal ya amsa da ameen, sannan yatashi tsaye, yana kokarin cire babbar rigarsa ta anganci,
Ameela tabisa da kallon cike da farinciki,
Bayan hilal yakarasa cire rigarsa, sannan yacire agogon hannunsa, ya kalli amila yana murmushi,” kizo muje muyui alwala muyi sallah munawa Allah godiyarmu daya nuna mana wannan ranar ta cikar burinmu”
Ameela ta janye mayafin dayake kanta tana kallon hilal cike da kunya, yaune first time dataga yanai mata wani iri mayen kallon,
Ameela tayi saurin maida mayafin ta rufe jikinta tana murmushi cike da kunya ta shagwabe fuska “too kaje ina zuwa “
Hilal yayi murmushi yace “Toh!!! yau naga sabon sanabi, amila nikike kunya yanzufa nazamo mijinki” nidai kaje zanzo nasameka” Ameela tafada cike da shagwaba,
Hilal yasaka dariya sosai sanna yanufi hanyar bandaki,
Ameela ta bishi da kallon tana lekonsa kamar marar gaskiya harya karasa bakin kofar bandakin,
Sannan yajuyo yana murmushi ya kiftawa amila edo, sannan ya murza kofar yashiga bandakin,
Shigarsa bandaki keda wuya Ameela ta janyo jakarta datake gefen gado tabude tadauko wayarta kirar Samsung galaxy s5,
Danne danne tafarayi,

Ina nesa ina rubutu amma danaga bana ganin abinda takeyi da awayarta yasa natashi nakarasa gurinta ina lekon wayar,

Janyo gurin notification tayi naga ta saka hannu ta danne gurin da ake bude data,

Zare idanu nayi ina mamakin wannan wace irin jarabar charting ce ta kamata, bazatama iya hakura da yau kadaiba, tun da yau ranar auren tace kuma first night dinta,
Bro Abdul ne ya dan dakeni a hannu nadan firgita(nadauka hilal ne yafito daga ban daki yakamani ina lekon asirin matarsa) nan nadawo daga duniyar tunanin dana shiga,
Na daidai birona na kara leka wayar Amila,
Massages naga sun fara shigowa ta ko wane App dakasan yakasance ana chart a cikisa irin su Facebook, Whtsapp, BBM, Instgrm, dadai sauransu wasuma banma san sunan suba dana fada muku sunansu,

Whtsapp Ameela tafara shiga, tana kallon wayar tana lekon kofar ban dakin a akai2,

Danna wayar take tanayin Kasa tana dunduba messages dinda suka shigo

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button