AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 67-68

  ??67 and 68??

Via OHW???? w

Ana gama azahar hilal yadawo gida, rike da jakar aikinsa a hannunsa,

Dakin ameelah yakarasa yasameta tana bacci, yaja tsaki a zuci yace “yanzu haka batayi sallar azahar ba”

Afili kuwa sunanta yafara kira yana dukan kafarta,

A hankali tafarka sukayi ido hudu ciki muryar bacci tace “harka dawo “

Hilal ya tsuke fuska yace ” eh nadawo, kinyi sallar azahar”

Ameelah tadafe kai "au har lokaci  yayi ne"

hilal yace “aa ki kwanta lokaci yajiraki”

Tagane bakar maganar yamata hakan yasa tayi murmushi tatashi tanufi bandaki tayi alwala,

Hilal yana tsaye tafito, saiya tashi yace “idan kingama sallar kisameni a daki”

Ameelah tace “toh”

Sallaya tadauko tafara sallah, bata jimaba tagama, tayi addu a sannan tatashi tanufi dakin hilal,

A zaune tasamesa yana kallon wata sabuwar waya datake hannunsa,

Sallama tayi yadago kai ya kalleta, takaraso kusa dashi tazauna,
Wayar ya mika mata yace “ga wayar kinan” tasa hannu takarba, iphone ce… Jita keyi kamar ta burma ihu,

Hilal yakatse mata jindadi dacewa “sim dinki na nan kona siyo miki sabo,

Cike da jindadi ameelah tace “yana nan bari nadauko “

Tatashi cike da zumudi tanufi dakinta dauko sim

Inda ta ajiyesa yana gurin, daukowa tayi tadawo dakin hilal,

Tamika masa sim din yayi off din wayar yacire murfi ya saka sim din sannan yamayar da marfin ya rufe ya kunna wayar,
Ameelah ta matsu wayar bata budeba,

Cas wayar ta bude, text massage suka fara shigowa barkatai, wadansu na mtn ne wasu kuma nawasu bakin numbers ne,

Hilal ya mika mata wayar, ganin sakonni na shigowa yace ” kiduba sakon kigani mana”

Ta razana sosai tayi murmushin rashin gaskiya tace ” toh jira nake sugama shigowa tukunna”

Kar kar kar sukaji wayar tadau kara,
Hilal yayi saurin duba wayar number HMM ce ,
HMM yakira, mummunan faduwar gaba ameelah taji…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button