GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 11-20

11_*
Arewabooks@Mamuhgee
Washe gari ba wani dogon walwala ta tashi
Saima guraren 9 ta tashi Dan tun asuba tayi sallarta,

Zare dukkanin kayanta tayi ta jefa kan kujera ta wuce toilet tashige tana kokarin daura towel jikinta.

Sosai ta jima tana wankan sbd tasaba Bata lokaci gurin kyalekyalen wankan,

Sai bayan mintuna ta fito daure da milk towel kanta Kuma nade da wani towel din mara girma.

Natsatsen Qamshin shower gel dinta na AESOP Mai sanyin Dadi ne ke tashi ajikinta ta kalla Inda qaramin bedside agogonta yake ta kalli time taga goma yakusa Dan haka Kai tsaye ta nufi gaban mirror tagara shiryawa.

Moisturizer kadan ta shafa na LA PRAIRIE sai oil na Neutrogena da kome Zata shafa saita shafasa takejin skin dinta daidai.

Dama kafin ta fito daga wanka zubbi tagama gyara mata dakin ta kunna humidifier dasu fresheners masu sanyin qamshi ta fice da kayan data cire zuwa laundry.

Elira kaftan dress ta saka dark brown da scarf sai Cassandra wedge sandal ta fito gabaki daya qamshinta na JO MALONE sea salt yana gauraya iskar hanyar datake biyowa.

Kai tsaye dakin umma yaganah ta nufa tasan lokacin umman bacci takeyi sbd a qaidarta haryanzu data fara tsufa Bata daina saka hannu akan aikin abincin A MAJEED matuqar yana gari tariga ta saba
Matuqar baka ganta kitchen ba A MAJEED baya gari Dan hakan Bata komawa bacci bayan asuba saita tabbatarda abincin breakfast yagama kammaluwa a dining saita koma ta kwanta sai 12 take tashi tayi wanka ta Kuma leqawa kitchen din sakawa zubbi hannu a abincin ranar.

Kaman yanda tasani bacci umman keyi Dan hakan fitowa tayi dakin Kai tsaye ta nufi hanyar dakin cin abincinsu tana shiga abbin na shigowa ta dago ta kallesa da fararen idanuwanta dasukaji tsadaddiyar fenty beauty mascara da eyeliner

Qamshinsa daya doke nata ta shaqa tareda dakatawa daga zaunawan da zatai cikin nutsuwa da girmamawa tareda tsananin kauna irin ta ‘da da mahaifi tace”

Good morning Abbi,
Barka da fitowa.

Saida ya kalleta cikin nutsuwa ya ja kujera ahankali ya zauna yana sake kallonta ganin yanayinta na sanyi jiki har lokacin
Basarwa yayi sbd karta samu damar fara Masa hawaye agurin yace”

Morning,
Kin tashi lfy?
Ya umma yaganah?
Tana bacci ne?

Zama tayi tana cewa”

Eh Takoma bacci.

Itace ta zuba Masa breakfast din kafin tazuba nata Takoma ta zauna tafara ci.

A natse yakecin brown past din da aka hada da soyayyan dankali da hanta sbd Sarai umma yagana tasan Baya wani cin kayan fulawa sosai yafison abinci Mai suna abinci bawai wani jagwalgwalon gayuba.

Satar kallonsa Inayah keyi tanason magana akan roqonsa maganarsu ta jiyan amma tana shakkar hukunci ko dokar ta qara tsanani akan iya ta jiyan.

Kasa daurewa tayi ta aje fork din hannunta tareda dagowa ta kallesa a marairaice tace”

Abbi….

Tissue ya dauka tareda goge bakinsa kafin ya dago ya kalleta da dukkanin fararen idanuwanta ya zuba mata yana jiran abinda takeso fada.

Ganin yanda ya zuba mata idanuwansa yasata sauke Kai tana qaqalo hawaye cikin idanuwanta ta dago ta kallesa hawayen na gangarowa kan kumatunta tace”

Abbi Dan Allah kayi hkr bazan sake tsallake zuwa school ba I promise
Amma Dan Allah kada ka hanani fita ko zuwa wani gurin.

Hawayenta dake gangarowa ya kalla tareda Dan sake wani gajeran murmushi dayayi Masa zuwan bazata sbd ganin qarfi da yaji wai ‘yarsa daya Rena da hannunsa keson yimasa dabara,

Duka duka Inayah nawa take?
Yaushe tayi girman da wayon datake ganin Zata iya Masa wani sisina da hawayenta tunda tasan bayaso..

Ita Bata tashi da mahaifiyaba bare ace takoya ko tagani agurinta Amma wai hartasan taringa Masa hawayen kirsa Dan yaringa barinta tana yanda takeso.

Sake fadada murmushinsa yayi kadan yana Kuma kallon hawayen nata datake tsiyaya da gaske Wanda badan yagama saninsu a yanzuba da tuni zuciyarsa zatayi ‘daci da ganinsu Amma yanzu mamaki yake sosai ta yanda take iya hakan.

Numfashi ya sauke ahankali tareda zaran tissue dake kan dining din ya miqa mata yana cewa”

Ya Isa idan kingama tashi muje nine zan aje school din yau kafin na wuce office.

Share hawayen tayi da tissue din daya Bata tana jin Dadi cikin ranta na yanda kwata kwata Abbinta baya juran hawayenta.

Miqewa tayi tabiyo bayansa tareda daukan LV hanbag dinta tafito tana duba wayarta dake ringing da sunan Zaid akai.

Bata wani dauki wayarba ta jefa jaka sbd tanason samu ta lallaba abbinta yabarta taringa zuwa duk Inda ta saba zuwanta itadai tanaso gskia.

Cikin black BMW 7 series suka fita shine da kansa yake tuqa motar tana gaba zaune,
gabaki daya Qamshin tsadaddun turarukansu yagama sauya numfashin motar Amma dayake motar tasace shine Wanda yafi shigarta sai nasa ya take natan sbd tuni akwai qamshinsa acikin motar.

har bakin makaranta ya ajiyeta batareda ya tankawa uban magiya ra rokon datake masaba,

Saida yayi parking ya juyo ya kalleta fuska a Dan sake cikeda kulawarsa da taushin murya yace”

Inayah.¿

Dagowa tayi ta kallesa tana kokarin qirqiro wasu hawayen dasuke son qin zuwa,
Ahankali tace”

Naam Abbi.

Wannan kukan na karya dagayau gabaki daya na sokesa Shima,
Meye amfanin hawaye Dan ki dagawa mahaifinki hankali?
Akwai wani Wanda yake Baki shawaran yin hakan ne sbd kawai kisa mahaifinki yamiki abinda kikeso?

Girgiza Mai tayi tana kallonsa da rauni tace”

No Abbi.

No Inayah fadamun gaskia sbd nasan banbawa ‘yata tarbiyar hakanba,
Meye amfanin hawaye kawai sbd dagawa iyaye hankali,
Wannan ne last time dazan Kuma ganin wannan hawayen ok?

Gyada Kai tayi tareda maida hawayen dama Kuma fama taketayi akan suzo din basu zoba sbd Allah yasani batada wani dalilin kuka a rayuwarta sbd alhmdllh Allah ya wadatar da mahaifinta abinda duk take buqata a rayuwa,
Mahaifiya kawai ta rasa wadda koda ganganci ko subutar Baki Bata taba ambatar ko sunan uwa agaban abbin harma da bayansa sbd tsananin fushi da bacin ran dayake nunawa sosai wadda kusan itama sai hakan ya samu shiga zuciyarta na fushi dajin bacin rai aduk lokacinda ta tuno da dole tanada uwa kodai tabarta da mahaifinta lokacin dayake cikin zafin talaucinsa kokuma ta tafi tabarsu sbd bazata iya hakuri da wani hali daga murdaddun halayensaba Dan kuwa tasani abbin nata murdadden mutum ne itada umma yagana ne kawai suke iya Zama da abinsu sbd sunsan komai dayakeso da Wanda bayaso.

Bata saba batawa Abbinta raiba ko tayi Bata iya hakurin dacin ransa akanta Dan haka ta kallesa tareda dafa hannunsa ahankali a marairaice tace”

Abbi kayi hkr nadaina daga yau.

Gyada mata Kai yayi tareda dafa kanta cikin kulawa yace”

Shikenan kije karkiyi latti,
Ki kula.

Murmushi tasake tana cewa”

Ok bye Abbi Allah yabada sa’an aiki.

Fita motar tayi tana daga Masa hannu daya kafin ta juya ta wuce.

Neesah dake jiran isowarta taqaraso suka nufi ciki suna maganar Abbinta daya soke zuwanta spas kwata kwata.

Saida suka shige ya juya yabar gurin sai alokacin ya dauki wayarsa dake ajiye ya kunna ya nufi hanyar office.

Yau daga makaranta gida ta wuto direct basu tsaya yawon dasuka sababa na gurare
Itama Neesah yau dole gida ta wuce Amma badan sunso hakanba sai Dan bata iya take umarni Abbinta dakuma Bata Masa rai.

Kwana biyu haka suka daina yawo suka maida hankali kan karatu musamman dama sunyi nisa sosai.

Kwana biyun ita kanta umma yagana Saida taringa jinjinawa sabon umarnin na A MAJEED sbd a duniya shi kadaine yakai yakuma Isa yakeda ikon Hana Inayah yawo,

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button