Labarai

Majalisa Ta Mika Wa Buhari Kasafin Kudin 2022

Majalisar Dokokin Tarayya ta mika wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kasafin kudin kasar na badi domin ya rattaba hannu a kai.

Wata majiya daga ofishin Magatakardan Majalisar da ta tabbatar da hakan, ta ce an mika wa shugaban kasar kasafin kudin ne tun a ranar Lahadi, 26 ga watan Disamban 2021.

A cewar majiyar, ana sa ran Shugaba Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudin kafin ranar 31 ga watan Disamban 2021, a yayin da za a yi bankwana na karshe da shekarar.

“Muna sa ran kafin 31 ga wata, za a sanya hannu a kan kasafin kudi,” a cewar majiyar.

“Tun a ranar Lahadi, 26 ga wata aka mika wa shugaban kasa kasafin kudin.

“An aika da kasafin kudin ne a ranar 24 ga watan kuma ya zuwa 25 ga wata da ta kasance ranar Kirsimeti, kasafin kudin ya kasance tare da shugaban kasa.”

Majiyar ta kuma karyata rade-radin da suka rika yaduwa a bayan nan cewa ba a aike wa shugaban kasa kasafin kudin ba yayin da ya rage kwanaki uku a yi bankwana da shekarar 2021.

Ana iya tuna cewa, a makon jiya ne zauren Majalisun Tarayya biyu da suka hada da na Wakilai da Dattawa suka amince da kasafin kudin na badi gabanin su tafi hutunsu na karshen shekara.

Daga @Aminiya

 

 

 


Post Views:
17

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button