BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 64


Tafiyar dai Aysha bata yuwu a yau ba, dan tuni Share” ya fice gidan tare da Khaleel yin godiya ga Abie, Anaam kuma sai ta ƙara samun sauƙin jikinta insha ALLAH zai kaita. Sai da suka fara biyawa ta o”ice yin wasu muhimman baƙi, ba wani dogon zama sukai ba sai zuwa monday idan ya dawo aiki.

Takardar da zai basu suje su duba kafin zaman ya nema ya rasa, cikin ɗan dafe kai ya dubu Khaleel da Fharhan. “Inaga fa nama bar file ɗin nan a gida wlhy, Khaleel saika koma
kenan dan dole ne mu basu suje su duba.” “Okay bara naje ai bawani nisa bane”.
“Okay ba damuwa, kafin ka isa zan kira su
ɗakko maka kawai”.
Kansa ya jinjina masa ya fice. Shi kuma ya
shiga ƙoƙarin kiran layin Fadwa. Harta tsinke ba’a ɗagaba, yay mata uzirin ko bata kusa ya sake kira, amma nan ma dai hakan, ya ƙara kira har sau uku sai aka koma danna masa number busy. Ransa ya sosu matuƙa, dan ya gane tana kan sani. Amma sai ya shanye kodan baƙin dake tare da shi ya maida akalar kiran ga Anaam. Gama wayarta da su Abie kenan kiran nashi ya shigo, bugu biyu ta ɗauka har yanzu muryarta cike da farin ciki tai masa sallama. A hankali ya sauke ajiyar
zuciya, ya amsa mata.
“Har yanzu murnar motar ce?”.
“Humm Yaya bazaka ganeba”.
Murmushi yayi, “Okay idan na dawo ai sai ki
ganar dani, yanzu nidai nutsu na saki aiki”. “Okay” ta faɗa kanta tsaye.
“Ki duba a study table ɗina, akwai wani file green a wajen ki ɗaukama Khaleel zai zo ya amsa yanzun”.

“Tom”.
Ta duba a kurkusa inda yace amma bataga
file ɗin ba, sai dai kuma hankalinta ne kawai
bai kaiba saboda ya dannesa da wani book.
Ta shiga bin komai daki-daki da kallo tana
ɗan ɗagawa harda buɗe drawers ɗin wajen.
Saukar idonta akan wani ɗan akwati ya sata
nutsuwa tana kallonsa, harta maida drawer
ɗin ta rufe sai kuma ta sake buɗewa ta ciro
akwatin. “Uhhm su Alhaji Yaya mm mi kuma
ake ɓoyewa anan? Koma dai miye zuciyata na
son gani”.
Tana ƙoƙarin buɗewa kira ya shigo wayarta,
shine dan haka ta ɗaga. Kafinma yay magana
tace “Yaya ban ganiba fa, inata nema kuma
tun ɗazun”.
“Kamarya? Bayan nasan yana nan akusa-
kusa. Ki ɗan ɗaga kayan wajen Khaleel na waje yana jiranki amfani zanyi da shi”.
“Oh sorry kamarma gashi anan ka ɗaura littafi akai”.
“Ok ki kai masa yana jiranki”.
Koda ta kaima Khaleel littafin sashen ta sake dawowa. Dan zuciyarta naga akwatin nan haka kawai batare data san dalili ba. Kiciniyar buɗewa ta shigayi, da ƙyar ta dace ya buɗu bayan ta haɗa da ƴan dabaru. Da

littafi ta fara cin karo, ta ɗan jujjuyashi tana taɓe baki ta ajiye. Sai envelope brown babba. buɗeta tai ta zaro albom na hotuna mai tudu sosai sai dai bai cika girma ba a tsaho. “Hotunan sirri ne kenan su Yaya aka ɓoy….” ta kasa ƙarasa abinda ta faro. Ko’a magagin barci aka tasheta babu gilashi a idonta aka nuna mata hoton babu gargada zata bada amsar itace. Hotone da taga irinsa yafi guda ashirin a gidansu. Hoton ne da aka ɗauketa a ranar haihuwarta tun a asibiti. Tana rungume a hanun Yaya Share” Abie da aunty Mimi sun sakashi tsakkiya suna leƙenta a hannunsa ya babbake ya hanasu gani. Da sauri ta koma na ƙasa, shi kuma a ranar sunanta ne ita da shi, na gaba itace da shi da Mamie da Abie da aunty Mimi. Ta cigaba da buɗe albom ɗin mamaki fal ranta dan ta kasa fahimtar ma’anarsa. Hotuna na gaba sun kasance a gurare daban-daban. Wani wajen ita kaɗai, wani ita da shi, wani har da su Abie. Ranar birthday ɗinta na cika shekara ɗaya. “Ya ALLAH” ta faɗa tana cigaba da kallonsu daki- daki. Jikinta ya ɗan fara rawa ganin hotunan da har tana a shekarar shiga primary, secondray, kai har jami’a ma akwai, bayan zuwa lokacin Share” baya tare da su. Duk wani hoton birthday ɗinta akwaisa, hakama

hotunan bikin salla kona wani taron makaranta kona islamiyya duk akwai. Hoton ƙarshe da yay matuƙar bata mamaki shine na ranar ɗaurin aurensa da Fadwa, itama kuma ranar nata ɗaurin auren da bata sani ba. Rubutun da yay a jikin hoton ya matuƙar firgitata……….
End of book

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button