NOVELSUncategorized

NAJEEB 46

Ibtisam wani irin dum taji,  na wani lokaci domin jin wannan Kalman daga bakin mutumin da kaf duniya shine wanda ya tsaneta, kai Anya??  Ban daiji abunda yace ba….  Duk tana manne a jikinsa take wannan tunanin…..


Najeeb yaci gaba da fad’in I love you so much ibtisam…..

Da karfi taja jikinta daga nashi tana kallonshi domin ta tabbatar shi dinne ko Waye

Ido ya kura mata yana kallonta, lokaci d’aya kuma ya k’ara matsawa kusa da ita tare da kamo hannunta yana fad’in ibtisam koda bakya so na ni Ina sonki, kin San mai yasa??  Just because you are my blood and you are my life……

Da sauri ta d’ago ta kalleshi cikin mamaki tare da tunanin kodai giyarshi yasha ne yasa yake fad’in wannan kalaman….. Lokaci d’aya kuma ta girgiza kai tunawa da tayi yan giya Idan suka sha giya gaskiya suke fad’a suna fad’in abunda ke cikin sune Wanda suka boye indai suka sha…..

Katse mata tunani yayi tare da fad’in ibtisam ban taba tunanin zanso any girl ba, coz I just take women only for fun, ban taba d’aukan mace a bakin komai ba saboda ina samun komai a wajansu Idan na rabu da wata anjima wata zata Kawo min kanta, sai wacce na zaba, and tunda nake samun mace ban taba tunanin inyi wani abu da mace y’ar Nigeria because Ina musu wani irin kallo na daban, which…… Sai kuma yayi shuru can yace ashe am wrong, ibtisam today I want to express my feelings to you……

Kukanta ne yasa yayi shuru yana kallonta cikin mamaki……

A hankali ya rungumota jikinshi tare da fad’in ibtisam nasan you will be shock idan kika ji na Fara sonki tun ban San miye so ba, at the time Ina d’aukan tsanar da nake cewa na miki ne yasa nake jin haushinki, na Fara nuna damuwa a kanki tun sanda naga kina tad’i keda wannan saurayin naki, at the time shima ban gane ina sonki ba, just abunda nake d’auka ina jin haushin guy dinne just kawai saboda bana shiri dake, tare da kafa hujjar yana zuwa zance wajan karamar yarinya wacce bata gama girma ba

Sanda akace an d’aura mana aure a lokacin ban so ba, but banda option face Nayi accepting d’inki as my wife, saboda Nasan bazan iya sakin macen dana aura ba coz inada kishin abunda nake so, ina zama dake duk da a lokacin zuciya ta tana nuna min tsanarki Wanda babu gaira babu dalili.

At the time da naji kina da ciki, wanda nayi miki ba tare dana Sani ba, lokacin na shiga damuwa Sosai, ban samu nutsuwa ba saida na tabbatar cikin nawa ne….. Ibtisam sai da na tafi na barki na gane duka tsanar dana miki ashe so ne, ban taba son wata mace ba sai a kanki, a lokacin na gane I can’t live without you….. 

Ibtisam tureshi tayi tana kuka tare da fad’in bana son jin komai daga gareka, domin ban yarda dakai ba, wlh najeeb ol wannan maganan da kakeyi is ol a lies, najeeb just like I see in your eyes, what you are telling me now is ol a lies…..   I don’t trust you

Najeeb zan zauna dakai just for the promise that I have make for granny, zanyi maka biyayya kaman yanda addini yace zan bika domin aljannata tana k’asan kafarka, zanyi maka duk wani abu da mace take ma mijinta, but karka k’ara cewa kana so na, domin bazan taba yarda dakai ba akan wannan Kalman har abada…….  Sai kuma tasa kuka Sosai

Najeeb wani miyau ya hadiye Mai zafi tare da d’aura hannunshi akan kafad’anta yace ibtisam trust me or not I don’t care but abunda ke raina na fad’a miki, and ban taba gayama ko wace mace wannan Kalman ba sai ke, just because you are special to me…..

Ibtisam tace najeeb basai ka yaudareni zan zauna dakai b…..

Yace bana yaudara tunda na taso, sannan bana fad’an abunda ba dai dai ba

D’ago mata da kanta yayi tare da fad’in just….  Sai kuma yayi shuru can yace plz ibtisam kalli ido na,….  You will see the love that I have for you…

Tace najeeb you never love me, inda kana so na Mai yasa aurena dakai saura igiya d’aya kace ka sakeni, wanda a lokacin inda inada tsarki da shikenan mun rabu har abada…..

Yace lokacin na furta Kalman saki ne just for your happiness, ibtisam bakya so na, kina zama danine kawai, I decide in rabu dake only for your happiness sannan nida kaina Nasan I don’t deserve you, domin ni mutun ne mashayi mazinaci, ol duka, inda duniya gaba d’aya kowa zaice min drinker womanizer, ban tunanin zan damu, but that word come from the person I love the must, ibtisam naji zafin wannan Kalman, wanda saboda maganan da kika fad’amin gashi yanzu Alhmdlh duk na daina, wanda a baya na aikata hakan ne bisa rashin sani,  hannunta Biyu ya kamo tare da matso mata su yana fad’in Kece kika canza min rayuwa kika sa na zama mutum banda abunda zan gode miki dashi, a rayuwa

Ibtisam ido ta lumshe wani hawaye mai zafi ya fito daga idon Nata, gaba d’aya ta rasa mai takeji, farin ciki ne ko dad’i ne gaba d’aya ta rasa mai takeji, ita gadai ta nan ne dai……

Najeeb yaci gaba da fad’in shigowarki cikin rayuwa ta, yasa gaba d’aya na canza daga yanda nake, which saida ga baya duka na gane am in love with you…..

Wani hawaye ne ya kuma silalo mata lokaci d’aya taja jikinta ta ruga da gudu tayi cikin Gida

Da ido ya bita harta bace mai sannan ya lumshe ido, lallai Allah mai iko, bai taba tunanin zaiso ibtisam ba a rayuwa sai gashi Allah ya jarabce shi, ashe wannan kiyayyar ta soyayya ce, shi a yanzu yanda yake ji zai iya zama da ita kota wani hali, amma Abu d’aya ne bazai jura ba shine ta dinga kira Mai sunan kabir, domin ya tsani kabir din

Ibtisam koda ta shiga dak’i ganin Zarah tayi tana waya, bata bi ta kanta ba ta kwanta tana kuka, gaba d’aya tana cikin rud’ani ta kasa yarda najeeb na Sonta, tabbas akwai wani abu…..  Lokaci d’aya kuma tayi shuru tana wani tunanin to in baya so na miye amfanin k’aryan??? 

Zarah ce ta kashe wayar da takeyi jin ibtisam na kuka, Zarah tace maiya faru kuma ibtisam?? Ko NAJEEB yayi miki wani abu ne??

Tashi tayi tare da kallon Zarah tace bai min komai ba, Zarah gaba d’aya Ina cikin rud’ani, Zarah kina tunanin najeeb zai so ni dagaske???

Zarah tace kwarai kuwa, domin a yanzu ma babu komai tare dashi sai soyayayrki Wanda nake gani a cikin idonsa…..  Shuru tayi tana kallon fuskan ibtisam din sannan tace Wlh najeeb yana sonki ibtisam, idan kika duba irin halinshi na da dana yanzu, gaba d’aya ya canza kaman ba najeeb din dana sani ba, in kika duba da kwata kwata baya sakar mana, musamman ma ke, amma kalla yanzu yanda ya sauya, wannan kad’ai ya isheki ki gane sonki ya kamashi  ….. Ibtisam ya kamata kema ki gane abunda najeeb ya gane, wanda gashi yanzu baya iya boye sonki, Kema ki fito ki nuna ma mijinki kauna da so, yanzu wayar nan da nakeyi bada kowa nake ba, saida Aysha domin hotanku dana d’auka a status nasa, tana gani ta kirani Wai dama ashe najeeb kika aura, nace mata eh, shine take fad’in shine bamu fad’a mata ba,??

Nace mata gashi yanzu ta sani, tace gaskiya kinyi Sa’a a rayuwa, domin samun mutum irin najeeb a matsayin miji, muna magana ne kika shigo kina kuka shine na kashe wayar

Zarah taci gaba da fad’in Wlh ibtisam bawai Ina goyan bayan najeeb bane, ya kamata ki ri’ke mijinki hannu bibbiyu, domin Idan kika tsaya wasa Zaki dana Sani nan gaba, najeeb Allah yayi shine mijinki, toh saiki ma Allah godiya, duk abunda Allah yaba mutum duk kyanshi duk muninshi a kullum ka dinga yima Allah godiya, domin Allah yasan abunda ya dace da kowa, kuma shine kad’ai yasan dai dai, kin amsan mijinki kaman kin karya abunda Granny take Fata ne, sannan kuma kaman kin nuna bakya son zabin da Allah yayi miki….. Ibtisam nasan ke ba kowa bane a ranki wanda zuciyarki ba komai take miki ba sai yaudara, abunda yasa nace yaudara domin kina tunanin kabir which tuni kin cireshi a tsarin ranki, Nasan ba komai kike tunani ba kar kici amanan shi right??? 

Ibtisam bata Bata amsa ba domin kuka takeyi

Zarah taci gaba da fad’in, karki manta KABIR ya daina d’aukan wayarki, tun tuni…..

Da sauri ta kalli Zarah cikin mamaki ya akai tasan tana kiran KABIR da a skul

Zarah taci gaba da fad’in nasan kina mamaki, ya akayi na sani, akwai wata rana sanda kuna waya kofar a bud’e take na dawo daga lecture na shigo naji kuna wayar, time din wayarki a speaker kika saka, gaba d’aya naji abunda ya fad’a,….

Kinga fah shi kabir namiji ne, wlh ibtisam In har namiji zai dake, mai yasa ke bazaki dake ba??  Sannan shi kabir din da kike tunani karki manta yana da mata yanzu, kuma na tabbata suna zaman lafiya, Kece ba zaki zauna da naki mijin lafiya ba??  Idan kika duba Allah yasa KABIR ba mijinki bane, domin Kinga anzo anyi mishi sharri, y’an uwanshi suka k’i yarda ai gwaji, duk wannan Abun dai dan Allah yasa dai shiba mijinki bane, najeeb dai shine mijinki, ya kamata ki farka daga baccin da kikeyi ki bud’e idonki ki gane gaskiya, kisan Mai kikeyi, wlh ibtisam Idan kika saki ranki na tabbata zaki dariya, Allah sarki granny burinta na karshe kenan……

Ibtisam cikin kuka ta katse Zarah tare da fad’in, insha Allah daga yau zan amsa mijina hannu bibbiyu, koda kuwa cewa da yayi yana sona k’arya ne……. Zan bashi kulawa tare da zuciyata…..  Sai ta kuma fashewa da kuka tare da rungume Zarah Tana fad’in nagode da kike kokarin d’aureni a hanya koda yaushe, Allah sarki granny bazan taba manta wannan maganar taki ba, da kike cemin inna rabu da najeeb wani zan aura, wanda zaki aura kin San halinsa ne??  Komin lalacewan wanda kake tare dashi gwara shi, akan kace zaka canza wani, domin in bakai wasa ba garin gudun gara saika fad’a ma gazo

Idan kika duba in mijinki yana neman mata, kika ce zaki rabu dashi kaza da kaza, idan kika rabu dashi kin San wa zaki kuma fad’a mawa?? 

Amsa shine baki Sani ba, a duniya babu abu mai zafi kaman mace ta samu miji mazinaci, wannan Abun yana da mugun ciwo Sosai, domin kullum hankalin ki ba’a kwance yake ba, kina tunanin zai iya kawo cuta ya manna miki….. Lallai zama da miji mazinaci ba k’aramin Tashin hankali bane, da yawa mata suna fad’a bazasu iya zama da miji Mai neman Mata ba, kuma gashi abun takaicin abun ba’a fuskansu yake ba balle ki gane yana neman mata ko bayayi, duk ba’a ganewa, wani namijin ma yanayi amma baki Sani ba, wani kuma kin kama sa, duk irin wannan Abun yana faruwa


2gnovel

4medicals

Smidris


Bawai Ina k’okarin in nuna ma mace ta zauna da mijin da yake zina bane, noo Ina k’okarin nuna muku Idan kin rabu dashi, kin San wa zaki kuma aura??  Duba da yanda duniya ta lalace yanzu maza a sashi d’ari wajan kashi 98 suna neman Mata, kuma dan suyi zina, wanda basa yin zina kalilan ne, domin yanzu duniya ta lalace wanda bakai tsammani ba sai Kaga yana aikatawa, which duk alamomi ne na Tashin alkiyama…..

A duniya babu abunda yafi hakuri tare da addu’a, Allah yana amsan addu’an Wanda aka zalinta da gaggawa, Allah yana yafe laifin bawa tsakanin shi da bawa, amma baya yafe laifin da bawa yayi ma bawa face shi wannan bawan yace ya yafe Maka

Ibtisam jan jikinta tayi tare da share hawayenta, Kai tsaye tashi tayi ta fad’a toilet tayi wanka ta fito, tasa wata doguwar riga

Zarah dai na kallonta bata ce komai ba

Ibtisam ta kalli Zarah tare da fad’in fuskana ya kumbura koh??

Zarah tace kije ki tambayi najeeb ya baki amsa

Murmushi tayi tare da fad’in au haka kika ce?? 

Zarah tace eh, domin shine zai gane hakan bani ba

Uhm kawai ibtisam tace


Yau gaba d’aya Sun fito cikin shiri domin tafiya airport dan zuwa saudiya

Tun ranan da najeeb ya fad’ama ibtisam yana Sonta bata K’ara Bari Sun had’u ba sai yau

Ta fito cikin jallabiya ba’ka, yayi mata kyau Sosai, wanda yau ta tsinci kanta da shafa powder saita k’ara kyau

Tunda ta fito idonshi ke kanta yana kallonta, had’a ido sukayi tayi saurin juyar da kanta gefe

Nufanta yayi tare da kamo hannunta ya ri’ke yace kina ta boye boye gashi yanzu na ganki sai muje koh

Tace plz ka sakar min hannu kar Mum ta fito

Yace AI hannun matata na ri’ke bana wata ba

Ibtisam wani murmushi ta saki wanda ya k’ara Mata kyau tare da fad’in plz naj sai kuma tayi shuru tare da zare ido tace Mum…..

Da sauri ya sakar mata hannu tare da Waigawa yaga babu kowa

Dariya ta saki Sosai tare da d’aga mai gira tace I escape…..

Murmushi yayi tare da fad’in plz come and hug me I miss you…..

Ibtisam kallonshi tayi suka had’a ido gaba d’aya jinta tayi wani iri, wanda hakan yasa tayi saurin kawar da kanta gefe, ta rasa mai yasa muddin ta kalli idonshi take jin haka

Jinshi tayi a gabanta har yazo inda take bata Sani ba, da sauri ta d’ago ta kalleshi jin ya ri’keta

Murmushi yayi tare da fad’in na kamaki yanzu…..

Shuru tayi tana murmushi k’asa k’asa

Najeeb yace so hug me

Ibtisam tace plz……

Hannunshi yasa a bakinta tare da fad’in don’t say anything, just hug me

Wani irin Abu takeji a jikinta, gaba d’aya wani kasala takeji a jikinta

Najeeb yace bazan barki ba sai kinyi abunda nace.

Da sauri ta lumshe ido tare dayin hugging d’inshi…..

Mum ce ta fito ganin su haka yasa taji wani irin dad’i har cikin ranta….

Ibtisam bud’e idonta tayi taga Mum da sauri ta Fara Jan jikinta daga nashi amma ya ri’keta kam ta kasa, tace Mum

Najeeb yace koda Mum tazo bazan barki ba….

Mum tace really…..

Najeeb da sauri ya saki ibtisam tare da Sosa kai yayi waje da sauri

Ibtisam ma k’okarin komawa ciki takeyi Mum tace ibtisam ku mu tafi lokaci na tafiya

Ibtisam wani irin kunya taji kaman zata nitse k’asa Don kunya….

Mum tace ina Zarah kirata mu tafi

Tace toh, tare da nufa d’akin ta kira Zarah suka fita, kai tsaye Mota suka shiga najeeb da ibtisam da zarah Mota daya mum da Dad mota daya NAJEEB a gaba ya zauna inda Zarah da ibtisam ke baya driver na jansu

Kai tsaye airport suka nufa inda suka shiga jirgi, ibtisam da najeeb waje d’aya suka zauna inda Zarah ita da wata mata suka zauna, sai mum da dad waje d’aya jirgi ya d’aga

Najeeb kamo hannun ibtisam yayi tare da ri’kewa yana shafa mata hannun tare da fad’in muna dawowa gidan mu zamu tafi

Ibtisam tace a’a ba yanzu ba, saina kammala karatu

Dariya NAJEEB yayi tare da fad’in oh gwara da kika tuna min fah, wannan karatun ni ban yarda dashi ba, gaskiya domin bazan yarda ki tafi zaria ba ni Ina wani waje ba

Ibtisam ta kalleshi ta gefen ido tare da cewa tunda na Fara ya za’ayi??

Yace hakuri mana

Ido ta zaro tare da fad’in hakuri

Hancinta yaja tare da fad’in yeah hakuri coz bazan bari kiyi nesa Dani ba, daga yanzu duk inda zaki muna tare

Dariya itama tayi tare da fad’in duk inda zaka kaifa

Yace in zaki bini sai mu tafi tare

Tace oh really

Yace yeah, ibtisam shuru tayi tana mamakin yanda yau ta saki jiki tana fira dashi haka, Tana tunanin har bacci ya dauketa……

Koda ta farka har jirgin ya sauka ta ganta akan kafad’an najeeb, tashi tayi da sauri Tana kallonshi yanda yake sakar mata murmushi yasa itama ta sakar mai murmushin sannan yace let go tare da d’agota domin su fita

Koda suka fita hannunshi na ri’ke da nata, inda suna shiga mota

Kai tsaye basu tsaya ko ina ba sai a hotel, ibtisam tayi farin cikin ganinta a k’asa mai tsarki

Najeeb yaso su sauka d’aki d’aya da ibtisam amma Mum tace ibtisam da zarah dak’i daya NAJEEB d’aki d’aya, babu yanda ya iya dole ya hakura amma badan yaso ba, yaso a bashi matarshi, danshi yana bukatar kasancewa da ita, dan Allah kad’ai yasan irin dauriyar da yakeyi

Ibtisam itama ta lura da yaso ta bishi d’akinshi, taci dariya Sosai

Kwanansu daya suka nufi asibitin da aka kwantar da mahaifin malam din najeeb inda suka gaida Mara lafiya din, sannan malamin yace su nufi gidansa duk inda za kuga Najeen to hannunsa na ri’ke dana ibtisam, ita gaba d’aya kunyar su Mum take amma shi ko a jikinsa, domin Suma larabawan haka suke, ri’ke da hannun matan su

Katon gidan malamin suka nufa inda aka had’a musu abinci Kala Kala akan dining, nan najeeb ya gabatar da iyayenshi wajan malam din tare da nuna mishi ibtisam yace ga matarshi, Zarah kuma yace ga sister d’inshi

Najeeb yace Dad shine malami na wanda ya koyar dani ilimin addini tare da fad’amin abubuwa da dama

Dad yayi ma malamin godiya tare da fad’in ban San da wani kalma zan yi maka godiya ba, domin ka ceto d’ana daga duhu ya gane miye rayuwa

Malamin yace karka damu, wannan ba komai bane, sannan abunda ya burgeni dashi NAJEEB yanda yake da kwakwalwa da saurin d’auke Abu a kansa, gskya ka gode Allah, sannan ina kira da masu kud’i da suji tsoran Allah, kar dukiya ta rudesu su saka su, su manta addini, wlh babu abu mai dadi kaman kasan addini kayi aiki dashi, babu wani gata da mutum Zaima y’ay’ansa a duniya face ya basu ilimin addini, domin shine gaba da komai, shine zai taimaki mutum a ranan lahira, ilimin boko iya na duniya ne kawai, wasu yaran sai Sun Gama karatun bokon sai Kaga sun rasu gashi ba’a samu ilimin addini ba Allah yasa mu dace

Suka amsa da Ameen inda najeeb ya kawo maganan sakin da yayi cikin Maye, nan malamin ya k’ara nanata musu babu saki tare da basu hujjojinshi akai

Sunyi na’am da batun tare da tabbatarwa babu saki ko d’aya tsakanin najeeb da ibtisam

Sunci abinci inda suka tashi sukai sallama, domin su koma hotel din da suka sauka d’akin su Mum ne na Farko daina su ibtisam na biyu na najeeb na kallon nasu ibtisam, su Mum na shiga Zarah na kokarin bud’e kofar najeeb yaja hannun ibtisam yayi d’akinshi da ita……..

pls click

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button