BABU SO 66

ɗacin hakan, amma taci alwashi komi zai faru
a yanzu ɗin bashi ne Anaam ɗin zataci itama
zata rama.
Aysha ta dire tray ɗin hanunta a gabansa,
fuskarta da murmushi ta gaida Fadwa da taƙi
kallonta saboda kar Aysha ta fahimci tayi
kuka. Kanta kawai ta jinjina mata. Ayshan
bata damu ba, dan tasan halin Fadwa wani
lokacin itama akwai yarfi. Hankalinta ta
maida akan Share!, “Yaya a zuba?”. Kai ya
girgiza mata alamar a’a, sai kawai tai musu
sallama ta fice a ranta tana ayyana akwai
matsala gaskiya, sai dai rashin ganin Anaam
yasa taji wani iri.
Kusa da shi ta taso ta dawo, “Soulmate……Hannu ya ɗaga mata a fusace. “Fadwa! leave
me alone. Tashi ki fita”.
Idanu ta tsura masa zuciyarta na mata
raɗaɗi, tasan a cikin fushi yake, kuma shi baya
son yanke ma mutum hukunci cikin fushi. Jiki
a saɓule ta tashi ta fice wasu hawaye masu
zafi da jin matuƙar tsanar Anaam na ƙaruwa a
ranta. Dan a ganin duk an mata hakane
saboda Anaam, ta kuma tabbatar ba haka
iyayen Anaam suka bar Share! ɗin ba kamar
yanda Mama ta sanar mata yanzun.
Ya jima zaune a wajen zuciyarsa na masa
raɗaɗi da ƙuna, baya son ɓacin rai da
damuwa, yama rasa ina zai kama da halin
matan nasa. Ya samu ita Anaam ɗin ta sakko
ya fara samun kwanciyar hankali ita kuma
Fadwar na neman rikita masa lissafi. dole ne
ya musu sabon shiri na zama da kowacce da
halinta. Yasan duk abinda Anaam zatai tana
yinsane a karan kanta sannan bata da ɓoye-
ɓoye. Fadwa kam ya fahimci akwai zugar
mutane baibaye da ita, dan tun zuwan Anaam
gidan ya fahimci ta ajiye wasu halayenta na
zahiri ta aro waɗansu daban, idan bai tashi
tsaye a kanta ba zasu iya laɓewa a bayanta su
tarwatsa masa farin cikin gidansa, shi kuma
harga ALLAH yana sonta itama. Ya furzar da
numfashi mai ɗaci, tunawa da Anaam dakecikin bedroom ya sashi miƙewa ya nufi
bedroom ɗin. Da mamaki yake kallonta
kwance a gado har tayi barci, ya tsugunna
saitin fuskarta yana sakin murmushi da kai
hannu ya shafa kanta. “Dama fitsarin ƙarya ne
kenan?”.
Idanu ta buɗe a hankali dan dama barcin
baiyi nisa ba, sai kuma ta maida zata lumshe
da ture masa hannu. Hannun nata ya riƙo
cikin nashi, fuskarsa gab da tata, “Tunda kin
tashi muje kisha fruit ɗin”.
“Ni na ƙoshi barci nakeji Yaya”.
“Ni kuma ban yarda ba idan kika sha sai kiyi
barcin”.
“Uhhum-uhhum”. Ta faɗa tana noƙe
kafaɗarta. Miƙewa yay yana murmushi, ya
ɗagata gaba ɗayanta. Watsal-watsal ta farayi
da ƙafafunta. “Wayyo Yaya! Wayyo Yaya ni ka
saukeni na ƙoshi”.
“Wayyo Aunty! Wayyo aunty ni bazan
saukeki ba sai kinsha”. Ya faɗa dai-dai suna
kaiwa falon………
✍