BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL
Abangaren MD kuwa tunda ya fita daga d’akin ya koma part d’insa ya zauna cikin wani irin farin ciki duk shafukan sa na sada zumunci babu inda bai d’ora sanarwar auren su da Maryam ba yayin da itama maryam kwana tayi saman abin salla saboda halin da ta kasance ya k’azanta ba ita ta samu ta hutaba sai bayan anyi assalatu.
Rana baya k’arya sai dai uwar diya taji kunya yaune d’aurin auren Maryam da MD wanda yau tun safe ake shirye shirye wanda yasa duk damuwar da take ji tsayin kwanakin ta nemeshi ta rasa.
Ta bangaran Ammey ‘yan uwanta sunzo sosai sai hidima ake, haka b’angaren ango cike tab da abokansa ana ta zuba masa shakiyan ci, haka dai aka shiryawa auren abokin nasu wanda har lokacin ya karato, idan ka kalli MD kuwa wani irin annurin farin ciki ne kwance a saman fuskar shi yayi kwalliya cikin bluen shadda wacce akayiwa riga da wanda da babba riga kayan sun yi mugun amsar jikin sa yayin da ya dinkawa Maryam nata ita kuma ruwan hoda tayi wani irin fitinannen kyau itama ba k’arya.
Hum zo kaga Baffa uban amarya shima yasha wanka iya wanka duk da kasancewar yana cikin halin damuwa na rashin sanin inda Baffa ya tafi hakan bai hanashi sakin fuskar ta shi ba da farko yaso a d’aga auren a tunanin sa Sailuba b’ata tayi amma Inna wacce ta k’araso da tawagar ta mota kusan biyar tace babu abinda zasu fasa haka aka cigaba da shagalin batare da sanin uwar amarya ba????????????????
Haka haj. Sailuba tayi kwanan wahala kwanan tashin hankalin kwanan masifa, a yadda takejin k’asan ta da k’yar idan mutumin nan bai farkata ba, amma idan ta tuna cewa muradin ta ya kusa cika sai taga hakan ba komai bane, kafin ta baro wajen boka sai da ya shaida mata yau za adaura auren Maryam da MD dan haka ta yi k’ok’arin ganin ta isa gida kafin agama shafa fatiha domin idan an d’aura bazai kuntu ba, haka ta baro wajen sa hankali a tashe tana fatan ta tadda ba a d’aura ba.
Tana shigowa dakin wani butu butu da ita suka fara ido hudu da Baffa wanda shigowar sa kenan daga wajen daurin auren a fusace yayo kanta cikin bala’ i amma suna had’a ido ya nemi fushin nasa ya rasa sai ma washe baki da yayi yace “a a Sailuba, Sailuba, hajajjuna daga ina haka?”
Yai mata tambayar cikin sanyin jiki yayin dayake jin wani irin d’aci can k’asan ranshi.
Ganin yadda aikin yayi saurin tasiri yasa tace “ban sani ba daga inda ka aike ni”
“A a Allah ya baki hak’uri nifa badan na b’ata miki na tambaya ba ganin yadda hankali na ya tashi ne yasa na ke tam”””””‘ kai dan Allah karka cika min kunne da surutun ka na banza” sai kuma ta bi ‘yan falon da wani kallo kafin ta maida hankalin ta kanshi tace
” Me ake yine naga an wani cika mana gida da wannan kazaman k’auyawan?”
Washe baki Baffa ya sake yi da dariya yak’e yace “d’aurin auren yarki ake ” ‘yata kuma wacece hakan?”
Ta tambaya tana tamke fuska a hankali yace “Maryam nake nufi Mana”
Sai tayi wani shu’ umin murmushi tace auho ” cemin zaka kayi shegiyar da akayo cikin ta a waje aka halarta maka”
Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara Baffa ya kafe Sailuba da ido yayin da duka ‘yan taron bikin suka kewaye su da hayaniya da son jin kwakwaf wasu kuwa fad’i suke ji tsinanniya saboda bak’in cikin ke baki haihu ba shine zaka sheganta masa ‘ya shi kuwa Baffa ji yai kansa yayi wani masifaffen sara masa take jikinsa ya kama rawa, yay saurin dafe kannan nasa da yake wani jin kamar ana buga masa gudu da sauri yayi saurin durkushe wa a wajen, yayin da itama Sailuba tayi saurin durkushe wa a gabansa ta bud’e dukan muryar ta da mugun k’arfi tace “EH BAFFA ABUBAKAR BA K’ARYA NAKE BA CEWA MARYAM BA YARKA BACE BA JININ KA BACE AN KAWOTA NE KAWAI DAN A GURBATA MAKA ZURI A KATAMBAYI UWAR TA WANENE UBANTA?
Da k’arfin gaske Baffa ya dafe kansa dayake bara zanar rabuwa da gangar jikinsa, yayin da kalaman ta sukayi wa Maryam da Ammey wani irin duka wanda atare suka shigo babban fakon Maryam tare da k’awayen ta dan amsa kiran Inna yayin da Ammey kuma tazo kawowa su Inna abincin su.
Tab Cha kwakiyar fa kenan
To masu karatu shin an d’aura auren Maryam da MD?
Baffa yana yadda da da maganar Sailuba?
Wane hali MD yake shiga idan yaji wannan mummunan al’amarin?
Da gaske ne Maryam BA JININ Baffa bane ko makirci ne?
Sannan wane hali Ammey take shiga sakamakon jin wannan mummunan al’amarin?
Duka wannan amsoshin dama wanda baku nema ba suna cikin littafin BA JININA BACE kashi na biyu wanda zai zo muku nan bada jima wa ba insha Allah ga mai buk’atar cigaban sai ta nemeni a lamba ta kamar haka 09030311095
Daga taku insha Allah
MAMAN ISLAM CE maiyi muku fatan alkhairi a koda yaushe
Thank you so much Allah yabar zumuch