BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

Duk su Baffa suka bisu da kallo yayin da zuciyar haj. Sailuba kamar zaiyi bindiga tsabar fitina da tsanar ganin Maryam daya Kuma mamaye ta Baffa yace “maman malam daga aike kuma sai najiki shiru?”

Rasa me zata cewa Baffa tayi sai ta d’ago ta dubeshi shima ita yake kallo, kafin ta lalubo abin fad’a yay saurin cewa “sanda taje ina wanka”

“To ku gama cin abincin akwai maganar da zamuyi daku duka”

“Nima Baffa akwai abinda nake son fad’a maka tun kafin kaje wajen Inna kuma naso binka sai bansan katafi ba”

Dafa kanta yay yace kar ki damu wannan zuwan ma sai da Inna tai fad’a sosai na rashin ganinki, laifin mamanki ne da tafiya ya tashi sai ta kawo uzurin da dole ake fasa tafiyan dake shiyasa Nassar kawai Inna tafi sani.

Yay maganar yana kallon haj. Sailuba da tayi wani kicin kicin da rai zuciyar ta nayi mata mugun sak’a.

Shima daga haka ya wuce falonsa Ammey ta tashi ta rufa masa baya dake yau ita ce da girki.

Suna barin wajen ta juyo da niyyar zuba abincin dan har ta k’agu taji neman da Baffa yake mata sai karaf idanun ta suka sauka cikin nasa ya wani yi tagumi ya kafe ta da ido, a ranta tace gaskiya wannan mutumin da bansan shi ba babu abinda da zai hana nace maye ne yadda yake da jarababbe kallon nan.

Azahiri Kuma abincin da zata ci ta d’iba a flat ta mik’e zata bar masa wajen, gane hakan da yayi ne yasa yayi saurin dafe hannunta yana binta da wani marai raitaccen kallo “dan Allah kar ki tafi ki barni”

Ya fad’a kamar zai mata kuka, binshi tayi da kallon mamaki, yayin da shi kuma ya k’ara wani marai raice mata sai ta samu kanta da kasa yi masa musu ta koma ta zauna, shima tsulum ya taso daga inda yake ya dawo kusa da ita “lafiya?”

Tace dashi tana kallon yadda yake wani faman shafa cikin sa d’an marairaice mata yayi yace”yunwa nakeji nima”

Abincin da ta zuba zata ci ta tura masa ta d’auki wani flat d’in yay saurin dafe hannunta yana girgiza mata kai ta d’an kafe shi da ido dan neman k’arin bayani “ki bani mana” ya fad’a yana kallonta ta d’an had’e rai shi kuma ya kafa mata naci sai da ta bashi haka kuma shima yabata suka ci suka k’oshi.

Da alama nacin MD ma kawai zai sa yasamu yadda yake so lol????????????????????

Maman Islam ce

بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
???? BA JININA BACE????

2021

          NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Godiya ta musamman gareku masoyan gaskiya hak’ik’a ina jin dad’in yanda kuke min ina ina sonku domin Allah musamman ma ku d’in nan
MAMAN Jani
Ammeyn Sadik
Antyn muhseen
Ya Rahman
Mare
Jidda
MAMAN Abul
Mom Irchad
Ummey Idris yakub
MAMAN sayyadi
Shamsan
Maman sultan
Umm nawaad
MAMAN Raees
Safiya Sopy
Aisha munir
MAMAN jabir
Xeeyyah
Rashida Muhammad
Afra
Fauzi
Ummukurthum
Aishatu k sani
Zainab autar mm
Jannat Aliyu
Barira Aminu
Hykarianeg 17
Ameenatu
Khadija Muhammad
Hafsat Bala kawu
Maman Arif
Ikilimatu D Baraya
Ummu Abul
Mr maimunatu
Aisha ibarahim ummi
Zainab Muhammad sambo
Juwairiyya Lawal
Maman twins
Mama
Khadija Isa Dari
Duk wanda bai ji sunan sa ba yamin afuwan mutara a text fage ina k’aunar ku nima son so fisabilillahi.

Page 33

Tusio tasa ta goge bakinta kafin ta mik’e ” ina zaki?”
Kallon yadda ya wani lafe jikin kujeran dining d’in tayi kafin ta wani tab’a baki tace “ina kaji Baffa yace yana son ganinmu?”

Kai ya d’an dafa alamun ya manta sai kuma ya tashi yace “muje” batareda tace komai ba ta mik’e ta wuce yabi bayanta suka nufi part d’in Baffa.

Tun kafin su shiga suke jiyo b’ab’atun haj. Sailuba sai faman bala i take zubawa Baffa wani mugun tsaki MD ya saki har ga Allah ya mugun tsanar matar nan haka nan, abinda ya dad’a d’aure musu kai shine yadda suka shiga suka tarar tana zuba ruwan tujara shi kuma Baffa yana lallab’a ta yana bata hak’uri, da dai yaga abin yak’i k’arewa ne ya dubi Ammey yace.

“Aminatu dan Allah na rok’eki ke ki hak’ura taje tunda ita ban isa da ita ba baza tayi min alfarma koda sau d’aya na sauke hak’k’in ki ba”

Cikin wani irin yanayin da bazaka tab’a iya fassara shiba Ammey tace “ai dama Baffa ni ba matar gida bace ‘yar zaman jiran gida bace da kula da gida ko ba haka ba?
Gaskiya Baffa wannan karon bazan yarda ba nima duk abinda zai faru sai dai ya faru amma nataji wallahi haba dan masifa da bala i shekara da shekaru abu yak’i k’arewa nima wannan karon bazan hak’ura ba Baffa sai dai duk abinda zai faru ya faru.

Nan fa Ammey itama ta bud’e wuta ta rik’a zubar da maganganu masu d’aci kunsan ance mai hak’uri bai iya fushi ba to haka ne yafaru ga haj. Amina yau duk irin yadda Baffa yaso rarrashin ta botsare masa tayi.

Dai dai shigowar su MD da suka gama sauraran komai MD ya kafe Baffa da ido kafin yace “Baffa mai yake faruwa ne nakejin abinda ban tab’a jiba game daku?” ya fad’a yana kallon Ammey cikin yanayin da bai tab’a ganinta aciki ba.

“Kamar yadda aka saba ne Muhammad yauma nayi magana ne akan kujeran hajji danake fitarwa duk shekara, Sailuba bata tab’a bari na bawa Amina tabawa wani nata ba sai sau d’aya kuma ni bansan me take da kujeru har guda goma ba tunda ko ta b’angaren mu nike biyama dangi, to itama mai hak’urin yau ta botsare min tace sam bata amince ba itama na rasa yadda zanyi yanzun”

“Kawai kabawa wanda kake ganin yafi cancanta”

“Baza abawa wanda yafi cancanta d’in ba wallahi ko zata mutu wannan kujeru nawa ne dan haka banga wanda ya isa hanani wannan kujeru ba ehe, idan kuma tak’ama ce naga ubanka ma acan k’auye raba kujerun nan yake kamar babu gobe”

“Ni bana harka da jahilai marasa ilimi dan haka bani da lokacin da k’ik’ancin ki*

“Uwar ka ta kabari itace dak’ik’iya baniba dan is………..kafin ta k’arasa taji wani irin fitinannen zafi ya karad’e fuskar ta ta d’ago a firgice dan ganin wanda yayi mata wannan d’anyen aikin sai da ta wuntsula daga kan kujeran ta ganin Baffa ya kafeta da kallo yana huci, yayin da MD ya mai da kansa k’asa cikin tsantsar b’acin rai da wani irin tsanar haj. Sailuba.

Da wani irin tashin hankali ta bar wajen domin wannan ne karon farko da hakan ya tab’a faruwa iya tarihin rayuwar su dan haka abinda yayi matan yai masifar gigitaya ta sani hakan yana nufin aikin ta yana rawa kenan ai kuwa ya zama dole ta sabunta shiri

Tana barin wajen Baffa ya dubi MD yace “Muhammad na fad’a maka ka fita hanyar Sailuba matar nan jahila ce amma bakaji” da mamaki MD yake duban Baffa to shi mai yace dan kawai yace Baffan yayi abinda yake ganin daidai shine ya shiga sangarta?
Da wani irin fushi MD ya bar wajen yayin da duk suka bishi da kallo sai Maryam ma ta rufa masa baya dan sam bataji dad’in abinda maman nata tayiba.

Ammey ma tashi tayi yayin da Baffa itama ya bita da kallo haka dai duk suka watse kowa zuciya babu dad’i Nassar ne kawai ya zauna ya ci ya koshi abimsa ya kama gabansa ya tafi gidansu boy abokansa.

Sanda Maryam ta isa part d’in MD har ya gark’ame k’ofar da key babu irin bugan da batayi ba yai banza da ita kamar baikita ba.

Haj. Sailuba kuwa tana shiga d’aki a gigice ta nemi wayar ta ta kira haj. Zakiyya kamar wata k’aramar yarinya haka take kuka wurjanjan cikin tsantsar tashin hankali ta kora mata duk abinda yafaru.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button