BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

” Ammey yakama ta ace kinsa ido akan yarinyar nan domin kuwa kema ‘yar mijinki ce dan haka kina da hakki akanta bai kamata ace kinsa ido ana watsa tarbiyyar yarinya ba idan ba haka ba idan Baffa ya dawo zan fad’a nasa irin rashin d’ar da yake faruwa agidan kamilin mutum kamar sa”

“Uaban Kane ya koya mana bad’alar nace uban kane bad’alalle d’anb iska mara mutunci kai dan ubanka tarbiyyab’ace da kai kai dazaka zauna kana gayan magana d’an iska mara zuciya dakana da zuciya da tuna ka fita harkana da ‘yata amma dake kai zuc………………take ta had’iye sauran maganar saboda wani matsiyacin kallo daya watsa mata duk bala inta tana tsiron Muhammad domin ba shi da mutunci idan ransa ya b’aci MD kenan kamar yadda abokansa suke masa lak’abi.

Sai data yi jinyar jikin ta na kwanaki biyu kafin ta samu ta warware har ta iya shiryawa ta fice gidan su Ammey ta nufa wajen malam Babba mahaifin Ammey hakanan Allah ya nufeta da son tsohon saboda shi mutum ne dayasan kansa ya iya zama da mutane abinda ya kamata ace uwa zatayiwa d’anta shine malam Babba yake ma maryam cikin hikima da dabarun su irin na tsofaffi domin ya kula Luba banzar Uwa ce irin iyayyen nannan da basu son b’acin ran ‘ya’yan su dan haka komai yaro zai basa tsawatar wa.

Tun daga nesa ya ta hango wani kamar bros a kusa da malam d’in take kuwa tai bala in had’e rai da k’yar ta iya yin sallama ta k’arasa kusa da MALAM d’in ta durk’usa har k’asa ta gaida malam sai wani ciccin magani take murmushi malam yasaki yace.

Idan naga zan iya zan dinga yin posting safe da dare idan na Gama daukiin Kuma sai abinda Allah yayi ????????????????????????????????

Maman Islam ce
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
????BA JININA BACE????
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 3

“Maryamu kenan maryamu sarauniyar mata me ya faru ne naga maryam d’in tawa tana wani ciccin magani?”
Murmushi ta d’an saki batare da ta shirya wa hakan ba yadda yai maganar ne dole abin yabaka dariya cikin shagwab’a yace “har ga Allah bazan yafe abinda ake minba malam kawai dan anga ubana baya gari shine ake neman kasheni ko akassaramin rayuwa nidai nabar mututm da Allah gaskiya”

Ta k,are maganar tare da zubowar hawaye.

“Subhanallahi wake neman kassara min rayuwar uwa ina raye a duniya da lafiyana?”

Had”e rai ta k’arayi tana hararan MD k’asa k’asa sarai ya ganta ya basar yayin da malam ya d’an kalleshi yace “kodai kaine muhammadi kake takurawa uwata?”

Murmushi kawai yayi yana shafa kansa yayin da malam yace “ashe kuwa kaine gaskiya muhammadu karka k’ara dukar min uwata shifa duka baya shirya mutum sai daima ya dad’a kangara shi dan haka naaiha itace kawai zatasa mutum ya rusuna ba wai dukana kaji ko muhammadu”

“Shikenan malam yafad’a cikin sanyin sa” yayin da maryam ta tsagal tace “tab waye zaimin nasihar ai wallahi sai dai yaiwa kansa mutanen da suke zama cikin bariki suna k’arewa matan abokan aikinsu kallo har su kyasa ne zaimin wata nasiha” ta k’arasa tana manna masa wata shegiyar harara dan har ga Allah ta tsanesa saboda gana mata azabar da yake.

Murmushi malam yayi yace “haba uwata shid’infa yayanki ne bai kamata ace kina masa raahin kunyaba”

“Tab’ ai wallahi sai dai ya nemi k’anwar sa ni babu abinda na had’a dashi’

Malam yace “gidanku nace gidanku ai ko ke kika had’a hanya da shi kuma alak’arku ba mai yankewa bace har k’arshen rayuwar ku”

“Ai kuwa ni zan Malku wannan bak’ar alak’ar kuma zakace na fad’a maka malam babu ni babu shi wallahi yadda baya sona baya k’auna ta nima haka”

Ta k’arasa maganar yayin da idonta yake nuna gaskiyar abinda yake kenan har k’asan ranta, malam yace “uwata idan zakiyi so kiyi so dan Allah haka idan zakiyi k’i kiyi domin Allah domin bakisan me gobe zai haifarba dan haka nake so ki cire duk abinda kika sanya aranki game da d’an uwanki”

“Malam alkhairi goben zai haifar ta fad’a idanunta yana cikowa da kwalla taci gaba da cewa malam dukanfa dayaimin ne yasa kayi kwanaki baka ganni ba ina can ina jinyar jikina, ni bama dukan ne ya fi b’atamin rai ba irin yadda ya disgani a gaban saurayina da k’awaye na dan haka wallahi ni babu ruwana da shi”

Malam yace “saurayi kuma maryamu shi Baffan naki bai sanar dake yayi miki miji bane?”

Da mamaki Maryam tace miji kuma malam? Ni bai fad’amin ba yadai ce na kasance mai kula da kaine kuma bai amince na saurari kowa ba har sai ya bani izini iya abinda na sani kenan”

“Yanzun bai isaba kenan shiyasa har kika fara kula wani batare da izinin saba”malam ya tambaya babu alamar wasa atare dashi, tace” bafa haka bane malam shid’in fa yayan k’awata ne wallahi yana da nutsuwa”

“Ke zaki fad’a mana hakan ko kuma mu zamu gano da kanmu?”
“Kune malam ta fad’a asanyaye ganin babu alamar wasa atare daahi.

Ranan dai hiran da malam batayi armashi ba ta sallame shi ta wuce, tana barin wajen malam ya dubi MD yace “akwai matsalafa muhammadu MD ya kafe malam da manyan idanunsa batareda ya furta komai ba, gane me yake nufi ne yasa malam cigaba da cewa kamata yaifa ace kaja maryam ajiki ba wai kadasa mata tsanarka a zuciyar taba kasanfa meke faruwa tsakanin ku dan haka nake neman alfarmar ka rik’a janta a jiki ba wai ka rik’a tsan gwamar taba hakan zai iya haifar da Marsala”

“Insha Allahu zanyi yadda kace malam cewar MD cikin sanyin jiki dana murya sannan ya d’ora da cewa ” yarinyar ce batajin magana ko kad’an malam”

“Tunda haka Allah yayi ta dolene mu rik’a hak’uri da ita my bita da addu a.

Ita ko maryam bayan tabar wajen malam gida ta dawo ranta babu dad’i domin ko a hanya tak’i jinin su had’u bare su had’a inuwa guda da shi, abakin get tayi kicib’us da Nassar ya rugo da gudu yace “Adda maryam albushir” tace “sweet” hannu ya mik’a mata yace to bani?”

Tace “ai kasan tunda nace zan baka ko” yace Baffa yayo waya aje a d’aukoshi inaji Ammey tana Kiran bros tace yaje ya d’aukoshi” manyan idanun ta ta wara akanshi tace na fara wasa da kaine ABDUL Nassar?”

“Allah da gaske nake kuma idan nayi k’arya kimin duka” hannu ta bashi suka tafa sannan ta kama hannunshi tace “muje nabaka sweet kai yau har wannan ball d’in da ka nunamin jiya kace na sai maka to yau insha Allahu yanzuma zanje na siyo maka wani tsalle ya doka ya rungumeta yace na” gode Adda maryam wallahi wata ran kina da kirki, dan Allah ki daina zagin Ammey na kinga nima bana zagar miki mama” kallonsa ta d’an yi sannan ta shafa kansa har ga Allah ta na son d’an uwanta mama ce bata son mu amalarta dashi wanda duk iya nacinta ta kasa gano dalilin.

Maman islam ce
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
????BA JININA BACE????
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 4

Tana rik’e da hannunsa suka shiga cikin gidan lokacin mama tayi shirin fita ganinsu tare da Nassar mama tayi kicin kicin da ranta tace”bana hanaki hurd’a da wad’annan annobar ba?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button