BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ga mamakinta ta kuwa bud’ar bakin mama sai cewa tayi “ni dai duk abinda Zaki aikata kada kisake ki kwaso ciki ki rik’a amfani da matakan kariya”

A matuk’ar firgice Maryam take kalloan haj. Sailuba jikinta har rawa rawa ya soma dan tsabar mamaki kasa magana tayi saima tunanin da ta soma aranta na “anya wannan uwa tace kuwa?”

Da k’yar ta iya ce mata daman nazo ne dan Allah Mama ki barni naje garin da momma take Nassar yace kwana d’aya kacal zasuyi dan Allah……katseta Mama tayi cikin sauke ajiyar zuciyar samun mafita na kaucewa tafiyar ta da Baffa zuwa wajen wannan jarababbiyar tsohuwar tace “sai kun dawo” mik’ewa tayi k’udin da takawo mata sai da ya girgiza ta ta amsa yau ko godiyar batayi mata ba ta fice kai tsaye d’akin Ammey ta nufa har MD ma yana can ta mik’ewa Ammey k’udin ta fashe da kuka tace “wai mama ce take cemin duk abinda zanyi kada na d’auko mata ciki anya uwata ce kuwa dan Allah Ammey ki fad’a min itace ta haifeni?”

Ita kanta Ammeyn ba k’aramin girgiza tayi ba musaman da suka k’irga k’udin miliyan d’aya da dubu d’ari da hamsi itama Ammeyn fashewa tayi da kuka ta kasa magana ganin haka MD ya kasa cewa komai ya rungume maryam yana rarrashin ta ransa na masa wani irin suya sun jima a haka kafin Ammey ta janyo maryam daga jikin MD ta kasa magana saima sabon kuka daya kwace mata.

Muje zuwa

بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
???? BA JININA BACE????
2021
NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 39

“Innalillahi wainnailahi raji un” kawai Ammey take ta maimaitawa, ta kasa magana, hakanan kukanta yak’i tsayawa, jikinta har rawa yake, tsabar damuwa takasa cewa komai sai fad’a jan yar ta take cikin jikinta tana shafar ta.

Can kuma kamar wacce aka tsikara zumbur ta mik’e tayi b’angaren Baffa a mugun fusace, da k’yar ta iya yiwa Baffa sallama yanayin da yaji muryanta yasan cewa lallai akwai gagarumin matsala dan ba komai Ammey take d’aga hankalinta akai ba.

Da kallo ya bita tana takowa kamar me koyon tafiyar yayin da Baffa ya kafeta da ido gabansa na fad’uwa, har ta k’araso cikin rawan murya tace ” Baffa yau ina so abani ‘yata tunda ba kune kuka yimin nakudar taba”

Da kallon mamaki ya bita, me kuma ya faru take irin wannan maganar?
Ya sani sarai rashin kunya ba halinta bane tana da hak’uri da sanin ya kamata yau kuma me ya tab’ota har take irin wannan zancen?”

Ammey da ranta yai mugun b’aci akan abinda taji yau abakin ‘yar tata yasa ta rufe ido ta rik’a fad’awa Baffa magana Kuma maganar duniya tak’i sauraran sa ga wani irin kuka da take yi mai cin rai.

Tun bayan fitar Ammey MD yaji wani sanyi aransa ya sani cewa shi zai fasa kwan dubuce ta cika yau shi kad’an sa sai murmushi kawai yake saki da maryam ta juyo zata kalleshi zai basar.

Gajiya yay da kukan nata ya matsa kusa da ita yace “kinsan wani abu?”
Tsaida kukan tayi ba tareda tace komai ba, ta dai zuba masa ido shikuma gane cewa shi take jira yasa yace “akwai abinda in kika sanshi sai kinji dad’i ranki zai miki sanyi zakiji cewa babu d’an gata kamar ki amma ina so kidaina min asarar wannan tsadaddun hawayen naki ki adana min su sai ranan da aka mik’a min ke a matsayin matana”

Ya fad’a yana d’age mata gira tareda murmushin da bata gane ko na meye ba, hararan sa tayi ta maida kanta can gefe tana shashshek’a, kafin ya k’ara magana aka kira wayarsa da sauri ya d’aga harda d’an russuna wa kamar yana gabansa, bataji abinda akace masa tadai ga ya amsa da to ya fice da sauri.

Lokacin da zai shiga d’akin dan amsa kiran Baffa sannan kuma Ammey ta fito daga d’akin cikin tsantsar tashin hankali da b’acin rai taci alwashin koda hakan yana nufin rabuwarsu sai an maido mata yar ta wallahi, ko kulawa da MD batayi ba ta fice ta ta wuce d’akin ta ta zari mayafinta rabonta da kwatanta yaji tun akan bada Maryam sai gaahi yauma ta k’ara kwatawa.

Yanayin da MD yasami Baffa na b’acin rai yasa MD ya k’ara nutsuwa ya k’arasa kusa dashi ya zauna kansa a k’asa Saida ya nutsu Sosai ya gaida Baffa wanda tsabar damuwa yasa ya kasa amsawa saboda tsabar tashin hankalin data jefashi.

“Muhammadu zan tambayeka ka dubi girman Allah ka fad’amin tsakani da Allah nake so kafad’a min iya abinda ka sani’ karka min k’arya, kar ka min k’arya, karka min k’arya, Muhammadu kada ka duba halin da kuke ciki kai da Sailuba asalin gaskiyar nake buk’ata”

Shiru MD yayi na d’an wani lokaci yana son tuna komai ko abu guda baya son ya manta (????????) MD fa ka fad’i gaskiya banda heri????????

Kallonsa Baffa yake yana jiran amsa, dan haka ya kwashe iya abinda ya sani komai bai rage ba kafin ya k’arasa jikin Baffa yayi wani irin sanyi wata irin nadama ta saukar masa take ya hau zufa jijiyar kansa tayi wani irin tashi, waima me ya hau kanshi da har ya manta halin Sailuba ya d’auki tarbiyyan gudan JININSA ya bata matar da ita kanta tarbiyyar take buk’ata take ya kama hawaye abinda ya firgita MD kenan ya rik’a rarrashin sa tareda kwantar masa da hankali

Wasa ya fara

MAMAN ISLAM CE
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
???? BA JININA BACE????
2021
NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 39

“Innalillahi wainnailahi raji un” kawai Ammey take ta maimaitawa, ta kasa magana, hakanan kukanta yak’i tsayawa, jikinta har rawa yake, tsabar damuwa takasa cewa komai sai fad’a jan yar ta take cikin jikinta tana shafar ta.

Can kuma kamar wacce aka tsikara zumbur ta mik’e tayi b’angaren Baffa a mugun fusace, da k’yar ta iya yiwa Baffa sallama yanayin da yaji muryanta yasan cewa lallai akwai gagarumin matsala dan ba komai Ammey take d’aga hankalinta akai ba.

Da kallo ya bita tana takowa kamar me koyon tafiyar yayin da Baffa ya kafeta da ido gabansa na fad’uwa, har ta k’araso cikin rawan murya tace ” Baffa yau ina so abani ‘yata tunda ba kune kuka yimin nakudar taba”

Da kallon mamaki ya bita, me kuma ya faru take irin wannan maganar?
Ya sani sarai rashin kunya ba halinta bane tana da hak’uri da sanin ya kamata yau kuma me ya tab’ota har take irin wannan zancen?”

Ammey da ranta yai mugun b’aci akan abinda taji yau abakin ‘yar tata yasa ta rufe ido ta rik’a fad’awa Baffa magana Kuma maganar duniya tak’i sauraran sa ga wani irin kuka da take yi mai cin rai.

Tun bayan fitar Ammey MD yaji wani sanyi aransa ya sani cewa shi zai fasa kwan dubuce ta cika yau shi kad’an sa sai murmushi kawai yake saki da maryam ta juyo zata kalleshi zai basar.

Gajiya yay da kukan nata ya matsa kusa da ita yace “kinsan wani abu?”
Tsaida kukan tayi ba tareda tace komai ba, ta dai zuba masa ido shikuma gane cewa shi take jira yasa yace “akwai abinda in kika sanshi sai kinji dad’i ranki zai miki sanyi zakiji cewa babu d’an gata kamar ki amma ina so kidaina min asarar wannan tsadaddun hawayen naki ki adana min su sai ranan da aka mik’a min ke a matsayin matana”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button