BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai da taci kukanta ta gaji sannan ta mik’e ta shiga wanka fasa amsar d’inkin da tai kenan, bayan ta fito a wankan ta zauna ta d’and’asa kwalliyar ta tai matuk’ar kyau dan dama maryam mayyar kwalli yace duk da tsantsar kyawun da Allah yai mata akwaita da son kwalliya.

A can b’angaren Halima kuwa ad’ari d’ari take komai domin ba ta da tabbacin fitowar Maryam tunda wannan mayen bros d’in nasu mai fad’an tsiya ya dawo.

Sosai masu docuration d’in suka k’ayata wajen sai kace wani bikin aure ba walima ba.

Maryam kuwa duk da tsamin da jikinta yai mata saboda azabar dukan datasha bata fasa shirye shiryenta ba dan bata tsoron bros ko kad’an acewar ta ai dukane kawai guda zai daka kuma guda zai bari.

Bata samu damar karb’o kayan ba sai wajen k’arfe hud’u da sauri tazo ta shirya cikin wani d’anbanzan swess mai azabar kyau da tsada ita da kanta tasan cewa babu k’arya tayi masifar kyau ba na wasa ba.

Tana shirin fita suka kicib’us damama tana shirin shigowa galala tayi da baki tana kaonta da irin kyaun da tayi rumgume maman tayi tace “mamana na shirya, nayi kyau kuwa?”

” fad’a ma ai b’ata bakine ‘yata kyawun da kikayi bazai fad’uba fatana dai ki kula da kanki kinji ko karki bari wani abin yasamar min ke in hakan yafaru bazan yafe ma kainaba?”

Wani lallausan murmushi ta sakar mata tareda manna mata kiss a goshi tace karki damu mamana insha Allahu babu abinda zai faru, yauwa ansaka min duk abubuwan da nace amitar?”

” komai ya kammala kije driver ke yake jira kar ku b’ata lokaci”
Had’e rai tayi tayi kicin kicin da fuska, take naga hankalin maman ya tashi tajawo ta jikinta tace “me kuma ya faru baby? muna maganar mu lafiya yanzun kin canja?”

Cikin shagwab’a tace “mama nafa ce miki da kaina yau zanja shine zakima driver magana gaskiya nidai ni da kaina zanje” murmushi maman ta saki tace “yanzun ke da wannan shine zaki b’atamin ranki abanza gashi” ta fad’a tana mik’a mata mukullin ta amshe tare da kuma rumgumeta ta sakar mata kiss a kumatu tace “ina k’aunar ki mamana sai na dawo” ta fad’a tare da yin waje aguje.

A d’an farfajiyar gidan ta tarar da Ammey tana kiranta amma ko kallon banza bata isheta ba balantana na arzik’i, tun kafin ta tada motar ta saki wani d’an banza hom ai baba mai gadi yanajin haka yataso aguje ya bud’e mata k’ofa dan yasan order ta ya fita daban dana kowa acikin gidan.

Ammey na tsaye har tafice sannan ta girgiza kai aranta tana mata addu ar sauka lafiya.

Ba d’an k’aramin gudu maryam take ba domin acewar ta wai ta b’ata lokaci abokanta na cen suna jiranta ga wani uban kid’a data k’ure wanda zai sa Sam bazata fuskanci ko gane abinda zai fad’a mata ba, wannan tabi ar tace sam maryam bata da mutunci ko kad’an bata sami tarbiyar kwarai daga maman tata ba ta nuna mata kudi sune komai na rayuwa dan haka tayi komai babu komai kud’ad’en mahaifinta zasuyi mata maganin duk wata damuwa.

Cikin k’ank’anin lokaci ta isa wajen, tasami gu tayi parking saida ta fara manna arnan glass d’in daya dace da kwalliyar tata kafin ta zuro kyakyawar farar k’afar ta waje ahankali take takawa, yayin zuciyar ta ya falfala da gudu cikin wajen saboda kid’an data ke jiyowa awajen da maryam gwana ce wajen rawa gata mayyar rawar ce biki ko batasan maishiba taje sai ta taka.

Tunda ga sanda ta faka motar yakafe wajen da ido har zuwa lokacin data fito cikin yauk’inta datakun ta mai tafiyar da hankalin ‘yan maza kai har ma da matan bak’aramin mummunar fad’uwa gabansa yaiba ganita gashi babu damar shiga wajen domin lokacin shiga meeting d’in da zasuyi yayi dole ya wuce amma aransa yana fatan har sugama bata bar wajen ba tunda yaga wajen data shiga yasan cewa wani bikinne tazo.

Ita ko maryam tana ganin ta shiga wajen har ta fara wata irin rawa da juyi karab idanunta suka sauka akansa, take ta aro wata irin nutsuwa ta arawa kanta dan tana masifar gudun abinda zai b’arar da ajinta wajen masoyin nata kuma abin k’aunarta Muhseen.

Abokanta na hangota suka saki shewa da ihun murnan ganin ta da sauri suka k’araso wajen wasu na d’aukar ta pic yayin da wasu ke suka take mata baya har suka k’arasa cikin wajen.

Kujerar da aka tanada mata wacce ta kasance kusa da Muhseen ta zauna kamar wasu amarya da ango tunda shigo wajen akan idanunsa har rawa data soma amma sam bai nuna ya gantaba domin maryam ba k’aramar ‘yar disgi bace shi yasa yake masifar kame kansa agabanta.

Ba tare da b’ata lokaci ba aka fara gudanar da abinda ya Tara su awajen sukaci suka sha sannan ta rarraba kyautukan data tanada domin abokanta duk Halima ce ta kula da wannan yayin da maryam ta masifar kame kanta agaban Muhseen sai da za ayanka cak ne ma ta d’an dubeshi k’asa k’asa ta gaida shi murmushi ya sakar mata ba tare da ya amsaba ya tashi suka k’ara wajen, wa ashe na murnan zagayowar haihuwar muhseen abin ya k’ayatar dashi yadda ya kamata yadda maryam take ‘yar bidiri to shi har ya dameta ya shanye bayan gama yanka cak ne aka bud’e musu filin rawa suka shiga suna wani irin taku mai ban shi’ awa da burgewa, juyowar da zatayi kawai idanunta suka sauka hakansa yana tsaye sanye cikin kakinsa dayake masifar yi masa kyau ya hard’e hannayensa a k’irjinsa ya kafeta da fitinannen kallonsa, take gabanta yai masifar fad’uwa hankalin ta yai mugun tashi ba dan komai ba sai dan gudun kar ya disga ta agaban saurayinta da abokanta musamman da ta kalli idanunsa taga sunyi wani irin rinewa sabo da b’acin rai, amma dan k’arfin hali irin nata kawai sai ta basar taci gaba da rawarta, abinda yai masifar k’ona masa rai yafara takawa cikin tafiyar sa na ingarman namiji batasan ya isota ba sai dayayi mata wani mugun damk’a kamar zai karyata saida ta saki k’arar wahala Muhseen kuwa yana ganin haka ya cika wandon da iska dan yasan sojoji ba imanine dasu ba yanzun sai suyi masa walmakalifatu.

K’ok’arin kwacewa ta soma ai kuwa yana juyowa ya d’auketa da wani azababben mari wanda a take hancinta ya balle da jinitayi luuuu zata fad’i saboda tsabar gigita ya fisgota ta fad’o jikinsa ya dad’a d’auketa da wani marin har guda biyu tsabar wahala da azaba bai barta ta gane inda take ba ya fincike ta daga jikinsa ya hau janta har jikin motar sa ya wullata ciki har Sai da ta gwaru da murfin motar saura kad’an ya had’e da hannunta wajen rufewar mukullinta ya jefawa driver da ya kira shi kuma ya tada tasa yabar wajen da masifaffen gudu yayin da yabar k’awayen ta da abokanta da jimami da tausayinta Allah ya had’ata da jarababben d’an uwa mara mutunci d’an hana ruwa gudu.

Daga yanayin order dayake ma mai gadi yasan cewa babu lafiya wannan jarababbiyar yarinyar ta tab’oshi, da sauri ya bud’e masa get yai saurin matsa gefe dan yasan cewa ba shigowar dad’in rai zaiyi ba ilai kuwa saida yayi wani irin masifaffen cin taya sannan ya danna hancin motar ciki, Nassar da dawowar sa kenan daga masallaci ya kwasa da gudu yai cikin gida domin yasan indai yayan nasa yana cikin zafi to kan mai uwa da wabi yake duk wanda yasamu bi yake ta kansa.

Maryam kuwa zuwa lokacin ta gama shiga wani hali tsabar wahalan dukan data sha haka ya kuma fincikota yajata ciki keeee ya gwara da kujera yana huci sai kace mayunwacin zaki a idanun haj. Luba ya watsar mata da ‘ya kamar kayan wanki nan kuwa ta hau jaraba tana tsine masa ko kallon ta baiyi ba yayin da sai da ya kuma lallasata sannan ya d’ago yana huci ya kalli Ammey dake karatu cikin wayar ta bata ko kalli inda suke ba yace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button