BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin tsantsar tashin hankali yabaro kamfaninsa wanda yake ziryata a irin ranan dan ganawa da manya da k’ananun ma aikatansa.


Wuya ita wuya Amina tacishi kafin tasan inda kanta yake sai da tayi kusan sati guda acikin asbitin kafin tasan inda kanta yake ciki dai Kam babu shi domin ya riga da ya zube tun aranar.

Sosai haj. Sailuba ta rik’a bawa Amina wata irin kulawa dan hatta Nanne wacce Sam bata yarda da Sailuba kuma tana nusar da Amina ta kula da takun matar dan dai sunk’i d’aukan abinda mahimmanci ne saida tazuba ido wannan karon ta k’yale sailuba da Amina amma duk wani takunta tana ankare gane hakan yasa Sailuba matuk’ar taka tsantsan.

Babu wanda yakai Inna takaicin rashin cikin sai dai tayi musu addu’ar Allah yabada na aike tareda yiwa Baffa nasiha mai kamar jirwaye cewa ya kula da matansa ya sanya ido akansu da takunsu, duk da cewa bai gane me take nufiba yayi mata godiya ya maidata har gida dan bai tab’a yarda Innarsa tahau motar haya.


Kusan sau hud’u hakan yana faruwa wanda hakan yasa Baffa ya rufe ido yanama Amina bala’i da tambayarta nufinta akanshi ya lura haihuwane batasonyi dashi daga baya har k’asa ya durk’usa mata yana rok’on data taimaka ta haifa masa koda d’a d’aya ne yamata alk’awarin duk abinda takeso zaiyi matashi amma dan Allah kada ta k’ara yimasa asaran gudan jininsa.

Hawaye hawaye fa take gani a idanunsa Baffa ne yake mata kuka da rok’on ta haifa masa ‘ya’ya yana nufin ita ke zubar masa da yara idan tasamu ciki.

Itama fashewa tayi da kuka mai k’arfin gaske zuciyar ta yana wani irin suya take kalaman anty shamsiyya suka shiga dawo mata akaro na hud’u data sake rasa cikin dayakai kimanin watanni biyar wanda har sunfara saka rai da shi tunda yafi sauran ukun jimawa.

“Amina nifa nafara zargin kishiyarki akan wannan b’arin dakike yi ajere ajere duk dana san cewa komi dayake faruwa daga Allah ne kuma dama can Allah ya hukunta wannan cikin da suka lalace bamasu taka k’asa bane amma akwai sula kuma Koda ba haka bama idan kin zauna kinyi tunani taya ita bata haihuba zata bar wata tazo da daga baya ta cika gidan aikinsan dole zatayi wani abun akai duk wannan soyayyar da kulawar datake baki duk na banzane ga uban bautar dake da take a siyansace tunda kikazo gidannan baki gaba baki baya kullum ak’are ya kud’in guzuri inzaki farka ki gane ki farka sannan maganar gaskiya Amina ta inda zaki gane cewa magana na gaskiya ne idan kin sake samun wani cikin ko Baffan kada ki sake ki fad’awa sai dai su ganshi tunda na lura ke ba mai girman ciki bane irin girman cikin bane irin cikin Umma ne dake wanda inda anganshi to bazai k’ara sati guda ba zai fito duniya dan haka duk irin wahalar da zakici ki daure ki cije ki raini abinki dan tun mahaifarki tana iya d’aukan ciki zata zo ta gaza kema azo ana samun wata matsalar kinga kunyi duro kenan burinta ya ciki ke babu ita kinga anyi one one kenan daman abinda take so kenan.

Ganin tayi tsaye ga hawaye na tafaman shatatowa daga idanunta yasa ya kamo hannayenta ya zaunar da ita asaman cinyar ta yana cigaba da hawayen tare da rok’on ta daure ta daina Yi Masa ganganci idan tasamu ciki, ganin cewa ko me zata ce ba fahimta zaiba yasa ta tsuke bakinta amma ranta banda suya babu abinda yake mata.


Wannan karon Saida tayi wajen wata hud’u kafin Allah yabata wani cikin mai d’an Karen laulayi dan haka kamar yadda ‘yar uwarta ta bata shawara ta rik’a daurewa tana shanyewa dan tanaso ta tabbatar da abinda ta fad’a mata akan wannan kareemar matar ma kula da ita da damuwa da al’a muranta

Hakan kuwa akayi duk yadda taso ganewa bata bata damar hakan ba haka ta rik’a daurewa tana nuna babu komai duk da kuwa irin bak’ar azabar datake sha wajen cimaka da kuma rashin son wani k’amshin haka ta dinga daurewa har zuwa lokacin da cikin shiga wata bakwai bai fitoba amma komai nata ya k’aru domin Amina macece mai matuk’ar kyau da diri gata fara tas babu ta inda ta baro mahaifiyar ta bafulatanar asali mazauna wani daji.

Bayan wata guda lokacin cikin ya shiga wata na bakwai Kuma cikin kariya da k’udura na Allahu S W T A daga Baffa har Sailuba babu wanda Allah yasa ya gane cewa Amina tana da ciki, yayin da Baffa yadamu sosai har yana cewa kodai wani abun tayi dan karta haihu dashi?

Tun bayan da cikin ya shiga wata na biyar ta daina duk wani laulayi sai dai dan banzan kwad’ayi kasancewar Koda yaushe itace a kicin tana bauta da aiyukan gidan hakan yasa duk abinda ranta yake so shi take dafawa taci son ranta kayan kwalam kuwa Baffa baya rabo da kawo musu dake ita Sailuba tafi ganewa ta narki abinci aci kaji da su kifi duk wannan abubuwan basu dameta ba haka Amina zatayi taci ta kuma bawa duk mai rabo dan itama mutum ce mai yawan kyauta kamar Baffa, sannan kuma duk wani irin kyau da shek’i data k’ara hakan baisa Sailuba ta ganeba kasancewar dama can ita d’in Mai kyaun ce, Baffa ne kad’ai ya kula da hakan saidai bai tankaba domin ya lura da ita a y’an kwanakin wani bin sai tayi ta k’unci irin dai abubuwan da ba a raba mai tsohon cikin dashi.

Ranan wata laraba Amina ta tashi da matsanan cin ciwon mara cikin dare Allah yasa Baffa ad’akin ta yake ganin irin murk’ususun wahalar datake yasa yayi tunanin ko wani cikin tasamu zai fita dan haka yadda take kuka tana fad’in ya taimaka mata haka shima yake rok’on dan Allah karta bari wannan karon ma yayi asaran cikin dakyar ta iya bud’an baki tace”dan Allah ka taimakamin Baffa ba bari bane wannan karon haihuwa zanyi d’a zan haifa Baffa da sam bai gane abinda take cewaba ya fita da gudu zuwa d’akin Sailuba dagashi sai gajeran wando ko riga babu ajikinsa haka ya fice yatasota tasha mamakin ganin yadda Amina take murk’ususun ciwo wani b’oyayyen murmushi ta saki tana fad’in aranta magani yabi jiki Kennan, ita ta taimakawa Baffa yasa kaya yasunkuci Amina da gudu yayi waje sam kasancewar sa na likita bai kamata ace har irin haka yafaru a gidansa ba matarsa da suke kwana su tashi tare har tasamu ciki ya kai tamakin haihuwa duk bai saniba, amma idan mukayi duba da cewa Allah shine me yadda yaso Kuma asanda yaso sai muga hakan ba abin mamaki bane.

Labarin yafara sauyawa ne daga lokacin dayagama dubata ya tabbatar da abinda ya gani bai k’ara tabbatarwa sai da yayi mata scainin, tashin hankali yatad’a a rud’e domin ganin dan mutum muraran yana neman hanyar isowa wannan duniya mai cike da abin al’abi da mamaki.

Kasa control d’in kansa yayi yafashe da wani k’arkarfan kukan dayasa Sailuba danno kai cikin d’akin da mugun gudu zuciyar ta kamar takarda tsabar haske tasani wannan kukan na Baffa yana nufin wannan karon ma sunyi messing babynsu saidai kuma abinda tagani ba k’aramin kad’uwa tayiba domin har lokacin bai kashe na’urar ba ga babyn nan wanda basu gane wane jinsi bane na ta wutsulniya sosai ta daskare a jikin k’ofa zuciyar ta yana wani irin masifaffen bugu.

Wani irin juyi Amina tayi gami da sakin wani k’arkarfan nishi da gudu Baffa yatarota dan saura kad’an ta fad’o daga gadon tarotan yayi daidai da sallamar babyn izuwa duniya wadda ta fad’o ita da mahaifar gaba d’aya rasa yadda zaiyi yayi sai kawai ya zube gwaiwoyinsa ak’asa yayi sujjada shukuriyya kafin yayi saurin Kiran ma aikata suka shigo dakayan karbar haihuwa shi ya gyara matarsa da ‘yarsu takafin ya rungumeta ajikinsa yana tofe ta da addu o I kala kala.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button