Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 71

Episode 71*

………“K Su’adah wace maganar banza ce wannan kike haka?”.
     Fulani ta katseta a harzuƙe.
“Ammy karki wani rufe gaskiya da son zuciya. Dole ne sirrin ɓoye ya fito fili, ban taɓa zaton Asmah zata zamemin BAƘAR INUWA ba sai yau. Ashe gara ranar da nake gudu da ita. Asmah bazan taɓa yafe miki ba, kuma insha ALLAH haka zaki ƙare rayuwarki a rashin nasarar da kike gani kina ciki……”
     A harzuƙe Adda Asmah ta yunƙuro zatai magana Fulani ta ƙatseta, hakan yasa mai-martaba bama gimbiya Su’adah damar faɗar duk abinda ke faruwa. Bako ta ɓoye ba, dan tun daga lokacin da riƙon Ramadhan ya koma hanun su Anne hanyoyin da Adda Asmah ta dinga sakata ita da Fulani har zuwa aurensa na farko, da kuma aurensa da Raudha zuwa son haɗasa da Aynah a yanzu da abinda suka jiyo ita da Safina yanzun. Bugu da ƙari dan ma kar Addah Asmah ta musa haka Safina ta ajiye wayarta da tayo recording duk maganganinsu kowa yaji.
      Sallallami kowa ya shigayi a falon, yayinda Adda Asmah ta haukace musu akan ita ƙarya ake mata. Saharri ne kawai saboda gimbiya Su’adah na borin kunya ta hana ɗanta auren ƴarta. Idanma kuwa tayi wani abun ai tare sukayisa. Wannan magana ta Adda Asmah ta sake tada ƙura, dan ko ba kunya gimbiya Su’adah ta daddage ta yarfama Adda Asmah mari,
       “Su’adah ni kika mara?!”.
“An mareki Asmah, kaɗanma kika gani wlhy, na tsaneki, na tsani ganinki, nayi dana sanin saninki matsayin ƴar uwata ciki guda. Kuma insha ALLAH Ramadhan yafi ƙarfinki har abada yafi kuma ƙarfin ƴarki, sai dai ki mutu da baƙin cikina dana zuri’ata. Munafuka kita zugani akan su Anne da suka riƙemin yaro tsakani da ALLAH kina cemin macutane ashe kece azzaluma mai cin amanar zuminci. Da iznin ALLAH ƙarshenki bazai ƙyauba…..”
      “K ce ƙarshenki baizai ƙyauba su’adah”. Adda Asmah ta faɗa tana kaiwa Gimbiya Su’adah mari, amma saita riƙe hanun ta murɗesa dan ko dai gimbiya Su’ada tafita ƙiba dama zuciya.
      Idanu Ramadhan ya sake rumtsewa kansa na juya masa. Yayinda su Bappi keta faman musu magana amma sunƙi sauraren kowa. Dan wata irin hankaɗawa ma Gimbiya Su’adah taima Adda Asmah tai taga-taga zata daɗi Aynah dake kuka ta riƙota.
       Nuna gimbiya Su’adah tai a kausashe. “Su’adah bakici bulus ba wlhy, ina matsayin yayarki kikaimin wannan abubuwan saboda kina auren mai kuɗi. Ni Asma’u nayi alƙawarin saina sabautar da rayuwarki data ahalinki baki ɗaya, dan wlhy sai kinyi dana sanin sanina. Sai kinsan na haifu cikin uwata da ubana, sai kin gwammaci daban kasance jininki ba!!”.
     Tana gama faɗa ta juya zata fita cike da borin kunya. Ana dakatar da ita bata saurari kowa ba taja hanun Aynah suka bar falon tana mai jaddadama gimbiya Su’adah bazata yarda da ƙazafin da sukai mata ita da Safina ba da mari ta jiraci sakamako.. 
      Wannan Al’amari ya firgita kowa ya kuma bama kowa mamaki. Mai-martaba da tun ƙuruciyar yaran nasa ya fahimci halin kowa ya share ƙwallar da suka cika masa idanu.
            “Ni nasan wannan ranar zatazo. Bammayi tunanin sauƙinta zai kasance hakaba. Tabbas Su’adah nada halayen banza da takejin zata iya taka kowa da komai idan taso. Girman kai, ɗaukar kowa ba kowaba duk halayyartace. Sai dai abinda mutane da yawa basa saurin ganewa daga gareta shine, abin kowa bai dameta ba. Su’adah bazaka taɓa jinta ta zauna surutu akan damuwa da cigaban wani ba, sannan dan taga wani da abu bazakaga ɓacin rai daga gareta ba balle damuwar kishinsa. Itako Asma’u da kuke gani, tanada sauƙin kai da son mutane, sai dai tanada nunkufurci da hassadar bata yarda kowa ya fita ba. Waɗan nan halayen nasu sune suka banbantasu, dan ita Hassada na cinye ayyukan bayi, tana maida mai son yin nasara bayan wanda yake gani bai kai ya fisa ba. Sai kaga mutum da halayen banza. Kai kullum cikin ibada da sauransu amma yanata samun nasariri kai sun gagara zuwa gareka karasa yaya haka? Nafi wane komai a rayuwa mizaisa ya dinga bani tazara? Amsar itace hassada. Hassada na ƙwace nasarori, ga wanda baida ita tana bashi nasarori koda bai kaika ba. Wasu suna tunanin Hassada itace kawai naga wane da abu banji daɗi ba. Hassada na zuwa kashi-kashi a cikin ayyuka.
         Kaji kai kaɗai kake son kai nasara a rayuwa. Kaji kanajin zafin wanda kafi da komai na rayuwa ya samu wani abu kai baka samu ba. Ka dinga damuwa da yawan maganar cigaban wane. Mutum ya gina ƙyaƙyƙyawan abu ka ruguza masa. Misali mutanen da ke fidda mana littafi ko zuwa su saya dan su yaɗa hassada ce. Shiyyasa zasuga kullum suna wahalar banza da tunanin dakushemu mukuma munata nasara a rayuwarmu domin basu isa hanamu samun abinda ALLAH ya rubuto a ƙaddararmu ba.
      Hassada na shigowa cikin ayyukan mutane daban-daban ƙarama ko babba, ka sani ko baka sani ba. ALLAH ya rabamu da hassada. Ka tsarkake mana zukatanmu akoda yaushe. Ka wajabta mana tsoronka da soyayyar ANNABINMU (S.A.W).
     Nasiha sosai mai-martaba yayi a wajen harda Bappi, daga karshe aka sake rufe taron da addu’a kowa ya kama gabansa..
   
      A ranar aka miƙa amare ɗakunansu zukatan wasu duk babu daɗi. Musamman ma gimbiya Su’adah dake kwance babu lafiya, dan jininta ya hau matuƙa sai dai gyaran ALLAH. Amma Safina da Mardiyya na tsaye a kanta harma da Fulani.

    Raudha dai batasan mike faruwa ba. Dan koda Ramadhan ya dawo sukuku baice mata komai ba ita kuma bata tambayesa ba saboda ba daɗin jikin takejiba sam. Ko lokacin da aka kawo su Bilkisu har falonsa suyi sallama a taƙaice ya musu nasiha ya sallamesu. Bilkisu kuwa ta rungume Raudha suna kuka har abin ya bama wasu mamaki dan da’alama akwai shaƙuwa sosai a tattare da su. Ganin abun nasu bana wasa bane Ramadhan ya rabasu da ƙyar ya rungume matarsa duk da mutane dake wajen bai nuna ya san da su ba. Bayan wucewarsu ya jima yana lallashinta, daga ƙarshe ma yasata sukai kwanciyarsu.

      Dan hatta da Aynah ta tare nata gidan bisa tursasawar mai-martaba. Hasalima shi da kansa yay mata rakkiya har gidan mijin nata ya kuma tabbatar ma mijin ko da wasa yaji a ransa zai iya rabuwa da Aynah duk abinda zatai, to lallai sai ya hukuntashi shima bawai ita kaɗaiba.
    To Alhmdllh, mai-martaba ma dan bai san wanene Aminu ba, idan hatsabibanci Aynah takeji ya taketa ya shanye. Idan iskanci ne gidan ta taras.

__________
 
        Har biki ya tashi lafiya kowa ya kama gabansa babu wanda ya sake tada maganar. Sai dai gimbiya Su’adah da jikinta keta sake tsanani duk da kulawar da take samu. Hakama Raudha ciwo ta kwanta sosai hakan sai ya raba hankalin Ramadhan biyu. Ga kwanakin hutunsu ya ƙare dama sati ɗaya ne kacal. Yanda jikin Maah ɗin keta ƙara tsanani ya saka Pa yanke shawarar tafiya taga likitan ta, dan haka randa su Ramadhan zasu koma government house aranar suma sukai shirin wucewa duk da Anne da taƙi yarda Raudha ta koma can gidan sai da Bappi ya lallaɓata. Aka kuma haɗata da su Basma.
     Tasha kuka duk da ita shaidace a yanzu mijin nata ya dawo dai-dai, sai damuwar da take hange cikin idanunsa da bata san ta micece ba. Ba kuma ta matsa da tambayaba tanata masa addu’ar dacewa dai da warwarewar matsalar tasa…
        
          Abubuwa sun lafa sai dai bazamuce duka ba. Gimbiya Su’adah na can likita ya ɗorata a magani, yayinda anan NAYA Addah Asmah keta faman shigi da fici na son ganin an hakala mata rayuwar Ramadhan dama Gimbiya Su’adah kanta duk da ƴar uwartace uwa ɗaya uba ɗaya. Sai kuma auren Aynah da take son rabawa wadda kullum cikin kiranta take tana kuka da roƙon taimakonta tazo Aminu zai kasheta. Dan bashi da aiki sai na mata fyaɗe safe da yamma. Idan taƙi yarda ya naɗa mata ɗan karen duka yayi yanda yakeso kuma. Baijin nauyin shigowa gidan da ƴammata da abokansa susha giyarsu da cocaine. Ya kuma dinga basu labarin abinda tai a America a club, hasalima anan ya fara ganinta har yaji yana buƙatar kasancewa da ita amma ta maresa. Shine dalilinsa na ƙudira aurenta. Ya kuma ɗau alwashin sai ya gama morarta ya saki videon wa duniya.
      Jin wannan zance Aynah tayi kuka tayi roƙo amma sam yaƙi saurarenta. Ta tabbatar masa komi yake so zatai masa akan karya tona mata asiri. Kota kanta bayayi saima ya zauna yayta kwasar dariya shi da abokansa.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button