Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 71

Ad

_____

Episode 71*

………“K Su’adah wace maganar banza ce wannan kike haka?”.
     Fulani ta katseta a harzuƙe.
“Ammy karki wani rufe gaskiya da son zuciya. Dole ne sirrin ɓoye ya fito fili, ban taɓa zaton Asmah zata zamemin BAƘAR INUWA ba sai yau. Ashe gara ranar da nake gudu da ita. Asmah bazan taɓa yafe miki ba, kuma insha ALLAH haka zaki ƙare rayuwarki a rashin nasarar da kike gani kina ciki……”
     A harzuƙe Adda Asmah ta yunƙuro zatai magana Fulani ta ƙatseta, hakan yasa mai-martaba bama gimbiya Su’adah damar faɗar duk abinda ke faruwa. Bako ta ɓoye ba, dan tun daga lokacin da riƙon Ramadhan ya koma hanun su Anne hanyoyin da Adda Asmah ta dinga sakata ita da Fulani har zuwa aurensa na farko, da kuma aurensa da Raudha zuwa son haɗasa da Aynah a yanzu da abinda suka jiyo ita da Safina yanzun. Bugu da ƙari dan ma kar Addah Asmah ta musa haka Safina ta ajiye wayarta da tayo recording duk maganganinsu kowa yaji.
      Sallallami kowa ya shigayi a falon, yayinda Adda Asmah ta haukace musu akan ita ƙarya ake mata. Saharri ne kawai saboda gimbiya Su’adah na borin kunya ta hana ɗanta auren ƴarta. Idanma kuwa tayi wani abun ai tare sukayisa. Wannan magana ta Adda Asmah ta sake tada ƙura, dan ko ba kunya gimbiya Su’adah ta daddage ta yarfama Adda Asmah mari,
       “Su’adah ni kika mara?!”.
“An mareki Asmah, kaɗanma kika gani wlhy, na tsaneki, na tsani ganinki, nayi dana sanin saninki matsayin ƴar uwata ciki guda. Kuma insha ALLAH Ramadhan yafi ƙarfinki har abada yafi kuma ƙarfin ƴarki, sai dai ki mutu da baƙin cikina dana zuri’ata. Munafuka kita zugani akan su Anne da suka riƙemin yaro tsakani da ALLAH kina cemin macutane ashe kece azzaluma mai cin amanar zuminci. Da iznin ALLAH ƙarshenki bazai ƙyauba…..”
      “K ce ƙarshenki baizai ƙyauba su’adah”. Adda Asmah ta faɗa tana kaiwa Gimbiya Su’adah mari, amma saita riƙe hanun ta murɗesa dan ko dai gimbiya Su’ada tafita ƙiba dama zuciya.
      Idanu Ramadhan ya sake rumtsewa kansa na juya masa. Yayinda su Bappi keta faman musu magana amma sunƙi sauraren kowa. Dan wata irin hankaɗawa ma Gimbiya Su’adah taima Adda Asmah tai taga-taga zata daɗi Aynah dake kuka ta riƙota.
       Nuna gimbiya Su’adah tai a kausashe. “Su’adah bakici bulus ba wlhy, ina matsayin yayarki kikaimin wannan abubuwan saboda kina auren mai kuɗi. Ni Asma’u nayi alƙawarin saina sabautar da rayuwarki data ahalinki baki ɗaya, dan wlhy sai kinyi dana sanin sanina. Sai kinsan na haifu cikin uwata da ubana, sai kin gwammaci daban kasance jininki ba!!”.
     Tana gama faɗa ta juya zata fita cike da borin kunya. Ana dakatar da ita bata saurari kowa ba taja hanun Aynah suka bar falon tana mai jaddadama gimbiya Su’adah bazata yarda da ƙazafin da sukai mata ita da Safina ba da mari ta jiraci sakamako.. 
      Wannan Al’amari ya firgita kowa ya kuma bama kowa mamaki. Mai-martaba da tun ƙuruciyar yaran nasa ya fahimci halin kowa ya share ƙwallar da suka cika masa idanu.
            “Ni nasan wannan ranar zatazo. Bammayi tunanin sauƙinta zai kasance hakaba. Tabbas Su’adah nada halayen banza da takejin zata iya taka kowa da komai idan taso. Girman kai, ɗaukar kowa ba kowaba duk halayyartace. Sai dai abinda mutane da yawa basa saurin ganewa daga gareta shine, abin kowa bai dameta ba. Su’adah bazaka taɓa jinta ta zauna surutu akan damuwa da cigaban wani ba, sannan dan taga wani da abu bazakaga ɓacin rai daga gareta ba balle damuwar kishinsa. Itako Asma’u da kuke gani, tanada sauƙin kai da son mutane, sai dai tanada nunkufurci da hassadar bata yarda kowa ya fita ba. Waɗan nan halayen nasu sune suka banbantasu, dan ita Hassada na cinye ayyukan bayi, tana maida mai son yin nasara bayan wanda yake gani bai kai ya fisa ba. Sai kaga mutum da halayen banza. Kai kullum cikin ibada da sauransu amma yanata samun nasariri kai sun gagara zuwa gareka karasa yaya haka? Nafi wane komai a rayuwa mizaisa ya dinga bani tazara? Amsar itace hassada. Hassada na ƙwace nasarori, ga wanda baida ita tana bashi nasarori koda bai kaika ba. Wasu suna tunanin Hassada itace kawai naga wane da abu banji daɗi ba. Hassada na zuwa kashi-kashi a cikin ayyuka.
         Kaji kai kaɗai kake son kai nasara a rayuwa. Kaji kanajin zafin wanda kafi da komai na rayuwa ya samu wani abu kai baka samu ba. Ka dinga damuwa da yawan maganar cigaban wane. Mutum ya gina ƙyaƙyƙyawan abu ka ruguza masa. Misali mutanen da ke fidda mana littafi ko zuwa su saya dan su yaɗa hassada ce. Shiyyasa zasuga kullum suna wahalar banza da tunanin dakushemu mukuma munata nasara a rayuwarmu domin basu isa hanamu samun abinda ALLAH ya rubuto a ƙaddararmu ba.
      Hassada na shigowa cikin ayyukan mutane daban-daban ƙarama ko babba, ka sani ko baka sani ba. ALLAH ya rabamu da hassada. Ka tsarkake mana zukatanmu akoda yaushe. Ka wajabta mana tsoronka da soyayyar ANNABINMU (S.A.W).
     Nasiha sosai mai-martaba yayi a wajen harda Bappi, daga karshe aka sake rufe taron da addu’a kowa ya kama gabansa..
   
      A ranar aka miƙa amare ɗakunansu zukatan wasu duk babu daɗi. Musamman ma gimbiya Su’adah dake kwance babu lafiya, dan jininta ya hau matuƙa sai dai gyaran ALLAH. Amma Safina da Mardiyya na tsaye a kanta harma da Fulani.

Ad

_____

1 2Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button