Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 71

      GOVERNMENT HOUSE

      Sukam matsalolin nasu da sauƙi Alhmdllhi, dan Raudha ma ta ɗanji ƙarfi harta koma zuwa makaranta ma. Idan akwai abinda ke damunsu a yanzu bai wuce ciwon gimbiya Su’adah ba. Sai dai kullum Pa na kwantar musu da hankali akan da sauƙi sosai. Hakan naɗan saka musu nutsuwa, har ma yake bama Ramadhan damar shan sharafin soyayyarsa. Duk da kuwa randa ya nuna buƙatar kasancewa da Ustazah ɗin nasa ansha daru. Kuka ta dinga masa da tsalle-tsalle dan ta kasa manta azabar data sha ta ƙarshe. Tunda suka dawo gidan daya tunkareta sai tace wajen bai warke ba ai. Ranar dai ya gaji da yawo da hankalin da take masa ganin zai cutu ya matseta ta ƙarfi ya duba.
    Tuni ta warke abinta zaren ɗinkin ma ya warware da kansa saboda kulawar data dinga samu wajen Anne. Azabar data sha ne kawai yasa take gudunsa. To ranar dai kam duk kukanta bai saurareta ba sai da ya sauke nauyi. Sai dai ya bita a hankali matuƙa yanda har taji nutsuwa tsoronsa ya ragu a ranta bakamar kwanakin baya ba.
     Daga ranar kuma suka sake dunƙulewa waje guda. Dan takai ma ita da kanta tana nuna so saboda cikinta yazo mata da wannan yanayin sosai. Cikin ƙanƙanin lokaci ta sake kara buɗewa tai ƙiba sosai da haske. Shi kansa har baya gajiya da kallonta da kiranta ƴar lukutarsa.
     Da yace ƴar lukuta zata fara masa kukan shagwaɓa ita bata yardaba. Shiko yayta dariya da tsokanarta. Sukanyi waya da Bilkisu kullum, tana kuma cigaba da sake ɗorata akan abubuwa na musamman har gashi yanzu Raudha ta ɗauka sabbin ma’aikata. Mai mata kwalliya da kula da duk wani ado da zatayi musamman idan hakan ta kama akan wata fita ta musamman duk da har yanzu Ramadhan bai taɓa yarda yaje da ita wani taro ba. Sai mai mata gyaran jiki itama. Ramadhan bai hanaba tunda ya san duk abinda zai ƙaru da sune shima ai, to shinema mai ƙaruwar tun school dai kawai Raudha ke zuwa, sannan koda yaushe komanta a rufe.

         Zuwa yanzu cikin Raudha ya shiga watanni na huɗu, ya fito mata ɗan duk da bawani ƙato can ba, wanda ma baida fahimta zai ɗauka tumbi ta fara ajiyewa saboda ƙibar da tayi. A kuma lokacinne gimbiya Su’adah ta dawo NAYA dan likitan riketa yay ta huta sosai acan.
      Ita da shi sukaje mata sannu da zuwa a wani dare cikin fitar sirri. Har yanzu bazamuce Gimbiya Su’adah na ra’ayin Raudha ba. Sai dai akwai sassauci matuƙa a yanayin data amsheta. Harda tambayarta tana lafiya kuwa wannan ƙiba tata lokaci guda haka?. Ita dai Raudha komai batace ba sai ɗan murmushi kanta a kasa. Hakama Ramadhan bai saka musu bakiba dan a ganinsa bai kamata yacema Maah ɗin Raudha nada ciki ba taga rashin kunyarsa a fili. Sai bilkisu ce ta sanar mata Raudha nada ciki ai. Duk da gimbiya Su’adah ta danne yanayin data shiga na farin ciki ƴaƴanta sai da suka fahimta har shi Ramadhan ɗin da Pa, sai dai babu wanda yace mata komai akan hakan.
      Raudha taji daɗin haɗuwa da Bilkisu da itama mijinta ya kawota duba Maah ɗin. Dan tanata son zuwa ma taga gidajen amaren laulayi ya hanata, Ramadhan kuma yace bazatajeba sai taji ƙarfi sosai. Makaranta ma yana barintane dan kar tai asarar abubuwa.
     Sosai Anne ta bata dabarun rainon ciki da shawarwari, tare da mata addu’ar fatan sauka lafiya. Basu baro gidan ba sai kusan ɗaya na dare………✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button