BAKAR INUWA 80
Hummmm bari dai na tsaya daga nan kar bin ƙwaƙwƙwafin yay yawa kuma????.
ALHAMDULILLAHI! ALHAMDULILLAHI!! ALHAMDULILLAHI!!!
Godiya ta tabbata ga UBANGIJI daya bani dama da rai da lafiyar rubuta wannan ɗan littafi. Abinda na rubuta dai-dai ALLAH ya bamu ladan baki ɗaya. Wanda nai kuskure ALLAH ka yafemin ni da ku da kuka karanta.
*Kamar ko yaushe ina neman afuwan duk wanda na ɓatamawa a yayin rubuta wannan littafin. A yafemin, a yafemin, a yafemin. Nima duk wanda ya ɓatamin na yafe masa, sai dai banda wanda ya zalinceni akan ganganci ko son zuciyarsa. Shima inhar yazo ya roƙa gafarata ya sanarmin zan iya yafe masa da fatan zai kiyaye gaba. Zata iya yuwuwa wannan shine littafi na karshe da bilyn Abdull zata rubuta a duniyar rubutu???????????? babu ruwan mutuwa dauka take a duk sanda taso.
Bazamu gaji da godiya a garekuba masoyanmu, kun nuna mana halacci kamar yanda kuka saba. ALLAH ya saka muku da alkairi ya bar zuminci, alkairin ALLAH yakai gareku a duk duniyar da kuke. Zafafa biyar na muku son so irin trillions ɗin nan wlhy. ALLAH ya saka da alkairi musamman wanda ke tare da mu tun farkon zafafa har zuwa yau. Kai harma wanda suka fara binmu yanzu duka mun gode sosai????????
Kamar yanda na faɗa BAƘAR INUWA ƙirƙirarran labarine. Idan kaci karo da abinda yay kamanceceniya da rayuwarka kayi haƙuri bakai din ake nufi ba. Sannan bazan gaji da sanar da mai karatu cewar littafi nishadi ne, faɗakarwa ce, harma da ban haushi. Idan kaci karo da nishaɗi kayi badan dole saika samesa ba ko ka nema. Idan kaci karo da ilimi ka amfana gwargwadon fahimtarka. Idan abin haushine ka ɗauka adon labari ne. Rayuwar novel bawai babu ita a zahiri bane, sai dai ba lallai kowa ya sameta 100% kamar littafin ba, idan ma ka samu kasa a ranka akwai ƙaddara da jabawar da zata iya banbanta da hikayoyin marubuta.
Abinda kaso gani baka gani na rubuta ba amin afuwa ajizancine irin na ɗan adam da mantuwa. Wanda yazo ba’a yanda kaso ba shima kayi haƙuri ba komai ake samu a yanda ake son gani ba. ALLAH ya sadamu da alkairinsa a zafafa karo na 7 da zasu zo muku nan kusa insha ALLAH????????????????????????????????
Mallakin Bilkisu Ibrahim musa (Bilyn Abdull)
Yi ƙoƙari ka biya na kuɗi ne, kar kuci hakkin daba naku ba