BAKINA YA JAMIN

BAKINA YA JAMIN

Ahto nidai bara na kamo wurin alajina karyayi fushi dani……

manage plx????????.

more comment more typing‍????????‍♀️.

ąƖƙ’ąƖąɱıŋ ɖơƈɬơཞ ɱąཞყąɱąɧ

tabbas alqalami????️ yafi takobi????.

#Commet
#Vote
#Share

PLX????????.

~Y’AR {BUBARE}CE!✍????…..~

????????????‍♀️BAKINA YA JAMIN????????????‍♀️
{ƙalubale garemu mata}.


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

STORY & WRITING BY DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.

Marubuciyar????????.

TAWA ƘADDARAR KENAN

AUTAR MATA
{rikitacciyar yarinya}.

And now????????.

BAKINA YA JAMIN
{ƙalubale garemu mata}.

Not edited❌.

بسم الله الرحمن الرحيم.

PAGE 7️⃣1️⃣ ↘️ 7️⃣5️⃣.

_____ci masa kwalar riga tayi kana tace “kaga malam wallahi Allah yau d’innan basai gobe ba saika sakeni kajiman mutumin banza….

Nanfa tahau surka masa zagi ta uwa ta uba,inda take shiga ba tanan take shiga ba……

Wata gigitacciyar tsawa ya buga mata kana yasa hannu ya 6an6areta a jikinsa kana yace “wai kinzata tsoronki nakeji ne¿

Ko kuwa a naki ganin bazan iya zama idan babuki a Cikin rayuwata ba¿..

To wallahi ko d’aya….

Idanma wannan kike gani to kije na yanke dukkanin igiyoyina dake kanki na haramtawa kaina zama dake ….

Duk da’ita ta nemi sakin saida dukkanin ilahirin jikinta ya’amsa ,hankakinta yayi bala’in tashi sai yanzu take data sani marar iyakaa….

Hannu biyu ta daura a saman kanta kana ta rusa wata gigitacciyae kuwa had’i da zubewa k’asa war waassss….

Ko kallon gunda take beyiba ya shige d’aki ya janyo biro da takaddah ya rubuta mata sakinta ukku rerasss!.

Fitowa yayi Had”i da wurga mata takardar a saman jikinta kana yace “billahil azim ki gaugauta barin gidannan kamin na dawo,idan ba haka bako!!!!…

Girgiza kai yayi had’i da ficewa daga cikin gidan gaba daya…

Bud’e baki da kyar tayi kana tace “Alhmdllh Allah mungode maka.

Ashe inada rabon sake rayuwa dakai habiby¿¿
Magana takeyi ita kad’e kamar zautacciya..

Sa hannu yayi ya janyeta daga jikin abba kana yace “mom kinsan jikinsa beda k’arfi fa…

Bara na hanzarta naje nazo da malam nata’ala…

Batare daya jira mezata ceba ya juya da hanzari yabar d’akin….

Komawa tayi gefen gadon takama hannayensa duka biyu ta riqe,bakinsa ne yaci gaba da motsawa alamun yana sonyi magana…

Kunnenta takai dai dai saitin bakin nasa domin jin meye yake cewa…

R…u…w….a jin meyake cewane ya sanyata sakin hannayensa tafice da sauri ta nufi d’akinta….

Ruwan zam zam ta dauka kana ta taufa masu ayatul kursum da falaqi da nasi ,jikinta har rawa yakeyi wurin kafa masa kofin a baki….

Saida ta tabbatar yasha sun ishesa kana tasauke kofin daga bakinsa …..

Komawa gefen gadon tayi tayi zaune, hawaye Sai tarara suke faman yimata….

Faɗowa sukayi cikin ɗakin kamar waƴanda aka Koro,kai tsaye gurinsa suka nufa, kama hannunsa malam nata’ala yayi ya rirriƙesa bakinsa saifaman mazari yakeyi……

Kinga beauty a gaskiya ni nashiryawa aurenki Dan haka ki gayawa su baba zan turo da magabatana idan yaso sai’ayi maganar komai d komai lokaci ɗaya…

Washe haƙora tayi kana tace……✍????✍????✍????✍????

More comment more typing????????‍♀️.

~Alƙalamin ????️Doctor MARYAMAH IBRAHEEM.~

~tabbas a’ƙalami????️yafi takobi????.~

Comment
Vote
Share

~ƳAR MUTAN {BUBARE} CE!✍????.~

????????????‍♀️BAKINA YA JIMIN????????????‍♀️
{ƙalubale garemu mata}.

STORY & WRITING BY DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.

Marubuciyar????????.

TAWA ƘADDARAR KENAN!

AUTAR MATA
{rikitacciyar yarinya}.

And now????????.

BAKINA YA JAMIN
{ƙalubale garemu mata}.


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

بسم الله الرحمن الرحيم.

PAGE 7️⃣6️⃣ ↘️ 8️⃣0️⃣.

__________Washe haƙora tayi kana tace “dagaske alajina¿

Jinjina mata kai yayi alamar tabbatarwa, ai kuwa nandanan jikinta yahau ɓari , ta matsu yawuce ta samu ta taka rawa kamar ita ace tamallaki wannan mutum da kuɗi suka zaunawa, ashe da rabon itama ta ɗanɗani zumar duniya…..¿

Sama sama aka idar da taɗin nayau domin kuwa gabaki ɗaya hankalin gimbiyar baya jikinta.

Cikin gida tashige kai tsaye ɗakin mahaifiyarta ta shige zaune ta tarar da’ita tana cin ɗumamen tuwo, zama tayi daf da mahaifiyarta kana tace “mama albishirinki.

“Goro , tabata amsa kai tsaye.

“Fari ko jaaah¿

“Ke dan Allah tashi bani guri bana son hauka kinji ko¿

“Shin ma na tambaye ki¿ ni sa’ar kice da zakizo ki sanyani gaba da wani albishirina¿

Zumɓuro baki gaba tayi kana tace “haba mama ki tsaya kiji dame nazo maki Mana.

Lomar tuwonta takai a baki kana tace “oya faɗi naji.

Gyara zama tayi kana tace “dama alajine yace nayiwa baba magana yanason ya turo magabatansa.

Riƙe baki mama tayi kana tace “anya dagaske kikeyi kuwa¿

“Allah da gaske nakeyi mama.

Tsame hannunta daga cikin tuwon tayi kana ta miƙe tace ahafffff, kice banga ta zama ba, Bara naje nagayawa baban naku, ta ƙarashe maganar tana nufar hanyar barin ɗakin.

★★★★★★★★★★★★★★★★

Tattare ƴan kayayyakinta tahauyi sai faman sharce hawaye takeyi domin kuwa ba ƙarya sakin ya girgizata.

Gidan yayanta tanufa kai tsaye janye da ɗan akwatinta gidan tashige sai faman sharce majina da hawaye takeyi.

Ƙwalala sallama tahauyi Muryarta sai faman creaking takeyi alamun tasha kuka harta gaji kenan.

Matar yayanta ce, tafito tsakar gidan sai faman harare harare takeyi, cinkaro da wacce ke tsaye a tsakar gidanne ya sanya fuskarta gaurayewa
Da murmushi, kana tayi haramar isa gunda take tana faman sharce hawayen dake ambaliya a saman fuskanta.

Rungumota tayi kana tace “lafiya kuwa A’ishah¿ Lafewa taƙarayi asaman jikinta kana ta buɗe baki da kƴar tace “Anty hafsat yasakeni wayyoni Allah bala ya cuceni yaci amanata.

Rufe mata baki tayi kana tace “ke lafiyarki kuwa¿ Kiketa faman kuka akan namiji ya sakeki , to miye a ciki¿ Dallah yiwa mutane shuru ai bakanki akafara sakin ƴa mace ba, dan haka share hawayennan kizo muje ki kintsa kamin yayan naki yadawo na sheda masa.

Cikin gida suka nufa , ɗakin yaran gidan ta nuna mata kana tace “ki ajiye jikarki a can kizo kiyi wanka kici abinci kamin ya dawo a san tayi.

Jiki a saɓule tanufi ɗakin , tana tafe uwa wacce bata da lakka.

Raɓen gado taje tayi zaune tana faman sharce hawayen dake ambaliya a saman fuskanta.

    Zabura tayi awa wacce aka tsikara ta janyo ƴar ƙaramar jikarta ta janyo wayarta tahau sarrafata .

Number khady ta janyo haɗi da danna mata calling.

Daga can ɓangaren khady kuwa Cikin zaƙuwa ta ɗaga wayar haɗi da karata a saman kunnenta kana tace “hello eshart , gyara zama tayi haɗi da sausauta murya kamar me raɗa tace “albishirinki ƙawata.

Goro mutuniyar kardai kiceman komai ya kankama¿

Wai waye _wai waye tafara ganin ba kowa a kusa yasanyata mayar da hankalinta a kan wayar Kinga khady bara zan shigo unguwarku yau ko gobe akwai story far..!

Daga can khady tace ” no mutuniyar just gaya min kina Ina, yanzunnan zaki ganni.

“Okey ina gidan yayana, kizo dan Allah da wuri _ wuri akwai story kinji.

“Okey bani 30minutes zaki ganni.

Ajiye wayar tayi a saman katifar da take
kana ta rafka uban tagumi ta lula duniyar tunani………..✍????

More comment more typing????????‍♀️.

~Alƙalamin????️ Doctor maryamah!.~

~tabbas Alƙalami????️yafi takobi????.~

#Comment
#Vote
#Share

Plx????????.

~ƳAR MUTAN {BUBARE}CE✍????!.~

????????????‍♀️BAKINA YA JAMIN????????????‍♀️.
{ƙalubale garemu mata}.

STORY & WRITING BY DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.

MARUBUCIYAR????????.

TAWA ƘADDARAR KENAN!.

AUTAR MATA.
{rikitacciyar yarinya}.

And now????????.

BAKINA YA JAMIN
{ƙalubale garemu mata}.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Leave a Reply

Back to top button