BAKINA YA JAMIN

BAKINA YA JAMIN


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

بسم الله الرحمن الرحيم.

PAGE 8️⃣1️⃣ ↘️ 8️⃣5️⃣.

________Kinga wannan ba komai bane ki kwantar da hankalinki.

Kinga alaji yace na gayawa Baba yana son ya turo magaba tansa asa mamu rana da zaran ansa rana kinga biki ai ya gurguso idan yaso lokacin bikin ki samu kiyi wuff da wani alaji a cikin abokanan ango….

Shewa suka buga haɗi da taɓa hannu , kana eshart tace “kai gaskiya kanki naja ta hannun dama kinga lafiya launa..

Amman kinsan Allah¿

Wallahi naji ciwon rabuwa da Bala, a haƙiƙanin gaskiya bazan taɓa samun mesona irinsa ba, yanzu matsalar danake ciki itace “nasan muddin yaya yadawo saiya sassaɓani a cikin turmi dan mugun ji da Bala yakeyi.

Mtssssssssass wani dogon tsaki khady taja kana tace “ashe haryau da sauranki, ni nazaci kanki ya fara jaaaa ashe ba haka bane¿

Kinga kiyi watsi da wani waishi Bala kizo mu raƙashe mu wataye.

Kiran da aka kwala wa, eshart a waje ne ya datse firar da suke yi, miƙewa tayi sannu alaikum jikinta yayi sanyi murus domin kuwa ko tantama batayi yayanta ne ya dawo.

Kallonta takai gunda khady take zaune sai faman sarrafa wayarta takeyi.

“Khady jirani ina zuwa inajin yaya ya dawo.

Ɗago kai tayi takai kallonta kan eshart kana tace “okey ina jiran ki idan kuwa kika jima zan fece dan naji ya mama da baba suka kaya batun turo magabatan alajina.

Ba tare da tace mata komai ba tanufi hanyar fita daga cikin ɗakin.

Kira ne ya shigo cikin wayar dake hannun khady , ƙwalalo idanuwa waje tayi lokacin dataci karo dame kiran wayar…

Danna accepting…. tayi kana takara wayar a kunnenta , cike da shaƙiyan ci tafara faɗin “ohh kaga hajiya lawisa matar alaji ɗan tasalle ashe _ ashe anajin ɗuriyar ku, ɗan murmushi lawisa tayi daga can cikin wayar kana tace “haba khady wannan kirarin har ina¿, Ina zamukai wannan kirarin haka¿.

Ɗan ya mutsa fuska khady tayi kana tace “uhmmmm ai kun can _ can ci ko wanne kirari a gareni.

Don ta kawar da waccen maganar ta ɗauko wata tace “amm ba wannan ba khady kwana biyu naji labari a gari cewa aure zakiyi shine ba sanarwa¿.

A’a a’a a’a yanzu har labari yakai gunki kenan¿.

Eh ko aure zanyi insha Allah nan bada daɗewa ba nima zan shiga cikin manyan mata za’a kama da mawa dani ciki da wajen Nigeria.

To Allah yasanya alkheree idan aka tashi kar amanta damu a sanar mamu.

Ba tare da tajira me zata ceba ta katse wayarta don gudun ta jefo mata wata maganar.

★★★★★★★★★★★★★★

After three months later.

Abubuwa da yawa sun fara tsawon waƴannan watannin abu buwa da dama sun faru, ciki kuwa harda sanya ranar auren khady.

A fannin hameed kuwa shima a bubuwa da dama sun faru a fannin sa , ciki kuwa harda warkewar mahaifinsa sumul harya koma kan harkokinsa nayau da kullum shima ansanya ranar auren sa da wata ƴar uwan mamanshi rana ɗaya dana khady za’a sha shagali kenan..

taufar ???? ranar da muke jira yau gata tazo fa????????‍♀️.

Ina anty Ummu inte….

Anty Ummu Affan karki bari a barki a baya fa

Wowww harna tsinkayo anty hauwa tasha gwagwaro fa???? lox.

To pans ku biyoni sannu a hankali domin jin yadda shagalin bikin zai kasance????.

More comment more typing????????‍♀️.

~Alƙalamin doctor maryamah????️.~

~tabbas alƙalami????️ yafi takobi????.~

#Comment
#Vote
#Share

Plx????????.

~ƳAR MUTAN {BUBARE}CE✍????!.~

????????????‍♀️‍ BAKINA YA JAMIN????????????‍♀️.
{ƙalubale garemu mata}.

STORY & WRITING BY DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.

marubuciyar????????.

TAWA ƘADDARAR KENAN!!!.


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

AUTAR MATA
{tikitacciyar yarinya}.

And now????????.

BAKINA YA JAMIN
{ƙalubale garemu mata}.

بسم الله الرحمن الرحيم.

PAGE 8️⃣6️⃣ ↘️ 9️⃣0️⃣.

________Ayau jummu’a 7/8/2020 dubban juma’ar musulmi suka sheda daurin auren Alhaji rabi’u me daƙaulen kaji da amaryarsa nana Khadija a kan sadaki dubu ɗari cifff!.

     ★★★★★★★★★★★★

A can cikin gida kuwa , maƙil yake da mata, sai faman sha gul _ gula akeyi.

Shewa najiyo daga cikin wani ɗaki da sauri na nufi ɗakin domin dauko maku rahoto.

Ɗakin maƙil yake da ƴan mata da zawarawa haɗi da matan aure dan kunsan mutuniyar ta mutane ce.

Kinga matar alh me dakwalai , takawarki lafiya, yanzu nan da zuwa wata ɗaya bama ganeki daɗa , dan kuwa hutu idan yaratsa wannan fatar taki baza a gane kiba.

Kinga eshart bana son shaƙiyan cinnan naki miƙomin wayata na kira alaji naji muryasa.

Ai kuwa ɗakin ya dauki shewa da kuwa ce _ kuwa cen su , wata daga cikin zawarawan ce tace “oh ni hafsatu, khady me kikeci na baka na zuba¿, nace dai alajinnan yau dashi zaki kwana a ɗaki ɗaya a gado ɗaya, dan haka yanzu ki barshi cikin al’umman annabi da suka zo tayashi murnar mallakar mace kamarki.

Ki bari har dare yayi wannan kam domin kuwa daren shine lokacin ki, idan yaso saiki cinyesa ki lashe kayanki.

Kwashewa sukayi da dariya gaba ɗayansu ƴan ɗakin , kana eshart ta caɓe zance da cewa “ke hafsy aikinyi kure a maganarki ta ƙarshe , inda kike cewa ” ta canyeshi ta lasheshi, ai saidai ya cinyeta ya lasheta dan ingaya maki da ganin wannan alajin kinsan ba dama, yau mutuniya za a zama mace.

Waƴannan dama waƴansu magan ganun ne sukayi ta tashi a cikin ɗakin.

{nikam abin yayiwa kwanyata girma beyiman nauyi ba dana dauko maku rahoto Amman muje zuwa dai}.

Ƙarfe takwas dai_dai aka fara kwasar ƴan matan amarya da zawarawan amarya zuwa wajen dinner daga can za’a wuce da amarya gidan mijinta.

      ★★★

Kai tsaye meena event center aka zarce da ƙawayen amarya.

Masha Allah, wuri ya ƙayatu iya ƙayatuwa , dole ma ya burge duk wata halitta dake wajen.

Anan waje aka ajiye dukkanin mutanen da aka dauko daga can gidanna su, ana jiran amarya da ango domin girmamawa zuwa garesu.

 Few minutes later.

Wata hatsabibiyar mota ce, fara sol! ta ƙayatu da jajjayen furanni, hankalin jama’a gaba ki ɗaya saida ya karkata ya koma kan motar.

An dauki tsawon mintuna ƙalilan kamin a wangale murfin motar, kana daga bisani saiga amarya da ango sunfito , taku sukeyu a hankali hannayensu sakale dana juna, nan danan gurin yadauki shewa da taɓi raff_raff_raff kakeji.

Su hajiya khady kuwa kai yaƙara girma, tafiya takeyi cike da taƙama da gadara, domin kuwa anata ganin tafi kowace ƴa mace sa’ar samun miji wanda yatara dukkanin abinda alajinta ya mallaka.

Anci ansha ancashe, haka zalika naira tayi kuka a wajen, ƙarfe 12:00am taron ya tashi.

Kai tsaye gidan angonta aka wuce da’ita.

Gidane daya amsa sunan gida, a waje tubarakallah masha Allah an ƙayata komai da komai Yadda Yakamata a waje.

Cikin gidan aka wuce da amarya darect.

Birki ƴankai amarya su kaja a parlon, ina ganin hakan na kutsa kaina daga ciki domin ganin meke wakana ne¿.

Kujerune guda biyu dasu ƴan filla_fillah dasu a ajiye cikin parlourn, inada yaƙinin kuma ganin sune ya da ƙusar da ƴankai amaryar a parlon.

Ɗan yaƙe , ɗaya daga cikin ƴan dauko amarya tayi kana tace “ah lafiya kuka ja tunga anan kuwa¿.

Muje ciki mana domin sada amarya da ɗakinta mana.

Jiki a sanyaya suka kama hanyar bedroom ɗin , yayinda ga baki ɗaya hankali khady a tashe yake dan kuwa bata san, meke wakana ba, Cox fuskarta lulluɓe take a cikin mayafi.

Canma cikin bedroom ɗin gashinan ga kamar sane.

Ba tare da ɓata lokaci ba kowa yakama gabansa, sai faman tsegum_tsegum akeyi.

Buɗe mayafinta tayi haɗi da fara waige_waige domin ganin me dame, iyayenta sukayi mata¿.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Leave a Reply

Back to top button