BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ba’a dauki Dogon lokaci ba, akayi sallama falon da buhun goruba
Ba Amal kadai ba hatta momy saida tayi mamaki, tace Ina zamukai buhun goruba ni juwairah?
Daddy ne ya sallami ma’aikacin, yace momy ni nace akawo dayawa Sai Tai taci
Momy tace kuma daddy har buhu?
Yayi shiru yakasa magana
Amal kuwa tashi tayi, taje tabude ta dauki guda daya, tadawo ta zauna takaita Bakinta
Wani Tsalle daddy yayi yariqe hannun ta, yace yi hakuri, kawo naje na wanke miki
Hanashi tayi ta zuba masa ido, ya marairaice yace please
Sannan tasaki, yaje yaqaro wasu, yashiga kitchen da kansa ya wanke su, yakawo mata
Momy tana kallansu yanda suke birgeta
Amal kuwa yana Bata tafara ci kamar ba gobe
Daddy yazuba mata ido yana mata kallan tausayi, to duk wanda yake iya cin wannan abun ai abin tausayi ne
Ita kuwa Amal ko ajikinta, data gama da qwallo daya zata ajiye tasake daukar wani
Saida tagama, sannan tayi ajiyar zuciya, ta maida Kallanta ga tv
Shima daddy waje yanema ya zauna, tana wannan kallan bacci me nauyi yadauke ta, momy ta dubi daddy tace dauketa kakaita daki
Babu musu yadauke ta ya kwantar da ita sannan ya sumbaci goshinta yafuto
*** *** ***
Next day
To shahid har kun futo? Eh baba mun gama zamu tafi, baba yace to kaji de abinda nafadama, kariqe yarinyar nan Amana Shahid
Karka manta yar’uwarka tana gidansu, duk abinda kayi mata to haka za’a yiwa qanwarka, Dan haka Dan Allah ku riqe junanku Amana
Shahid yace baba insha Allah Babu matsala, zan riqe ta Kamar yanda zan riqe Amal, ba zanyi sakaci da ita ba
Umma dake gefe tace to Allah yayi muku albarka, idan kunje ku gaida su hajiyan da Amal
Shahid yace to umma zasu ji, shahida ce tafuto itama cikin shirinta, Bayan sun gaisa dasu umma ne, sukai musu sallama, Shahid yace to umma Sai weekend insha Allah
Umma tace nikam kuyi zamanku ma Shahid
Shahida ce tace a a umma gaskya zamu dawo banasan narabu dake
Murmushi umma tayi tace to yata Allah yakaiku lafiya
Dahaka suka fice daga gidan sukadau hanya
*** *** ***
After 2 week’s
Daddy ya maida hankalin sa sosai wajan aikinsa, Koda yaushe baya zama agida saide idan yadawo ne zai kebe da iyalinsa
Haka kuma duk tsawon wannan lokacin bai qara zuwa wajan Amal da wata buqatar sa ba, idan yaje ma kullum cikin bacci take, Koda ace yana burin su kasance tare Awannan Daren haka zai ganta tana aikin bacci saide ya hakura
Kullum dataci abinci Sai bacci kamar me cutar bacci
Haka ya daure yake hakuri
A yayinda su shahida suke zamansu lafiya, gwanin sha’awa da birgewa
*** *** ***
Karfe hudu na yamma yau agida tayi mishi,direct Dakin Amal ya wuce, yau yayi sa’ah tana gaban madubi tana kwalliya, yana zuwa yafada kan gadonta yace baby I miss you sosai wallahi
Juyowa tayi tace kaida ka share ni kullum kana office kamar bakada mata
Murmushi yasaki yace banasan rigima, Bayan kullum nadawo kina bacci
Nikuma banasan tashin ki a bacci shiyasa
Fari tayi da idonta tace to naji, tashi muje kayi wanka Kaci abinci saika huta
Cikin shagwaba yace baby nide anan zan shirya yau
Amal tace my dear karmuyi haka dakai Dan Allah tashi muje
Hannayensa ya miqo mata alamar ta dagashi, taje takama jansa takasa karshe de shine ya fuzgota tafada jikinsa
Kissing din wuyanta yayi sannan yace to muje
Hannunsu sarqe da juna suka futo sukai dakinsa
Dakanta tacire masa kayan sannan takaishi har toilet din tafuto
wardrob ta nufa ta dauko masa kayan shan iska, sannan ta kalli Dakin, yana Dan buqatar gyara, haka tafara tattare kayan Dakin
Ta gyara shi tsaf, yanata qamshi
Yana futowa ta karbi qaramin towel din dake hannun sa yana goge ruwan fuskar sa
Qarasa goge masa ruwan tayi, tajashi har gefen gadon suka zauna, ta dauko mai tafara shafa masa
Shikuwa Sai binta yake da kallan birgewa da tsananin so
Yana zaune tana shafa masa man, taushin Hannunta dayake yawo ajikinsa ne yahaifar masa dajin wani irin yanayi atare dashi
Man ya karba ya ajiye yana binta da wani irin Mayan kallo, nan da nan ta gane manufarsa
Batayi masa musu ba lokacin daya janyota jikinsa da niyyar yin abinda yake so, tunda ita kanta tasan cewa yayi Mata hakuri
Basu dau tsawon lokaci ba suka Lula duniyar ma’aurata
Sosai suka murji junansu, sannan sukai wanka suka sake shiryawa, daddy Sai nishadi yake,
Amal na fesa masa turare yaga tana yatsina fuska, da mamaki ya kalleta yace baby lafiya kike kuwa?
Saurin boye damuwar ta tayi tace my dear babu komai
Yace no idan kinajin wani muje asbiti
Tace karka damu babu komai, Hannunta yana cikin nasa suka futo daga Dakin
Suna Zuwa falo ta riqe cikinta, tace wayyo Allah na Yaya daddy ciki na
Lokaci daya Daddy ya hargitse, yarasa Yaya zaiyi, kamata yayi yace Amal!!
Takasa amsawa Sai murqususu take ta riqe cikinta
Cikin tsananin tashin hankali yace Amal!!!
Hakanne ya janyo hankalin Abba da momy dasuke daki, Aguje sukayo falon
Suna Zuwa momy tace subhanallah meyasa meta daddy?
Idanunsa jajir yace momy Wai cikinta ne yake ciwo
Jikin momy yayi mugun sanyi ta dubi Amal da Bata Motsin kirki, ta janyo ta jikinta ta dubi Abba tace alhaji mu tafi asbiti
Abba daya zama gunki yana tsoron Kar itama ta mutu cikin mutuwar jiki yayi waje
Momy ta cewa daddy dauketa muje, yana dagata sukaga jini awajan
Momy tace innalillahi wa inna ilaihir raju’un
Daddy kuwa yana ganin haka Sai kuka
Suna futowa harabar gidan sukayi kicibis da Abba doctor hauwa, wadda inde jinya ce ta mata agidan to ita ake turo musu saboda qwarewarta wajan aiki
Momy Gabanta yana faduwa tace alhaji yarinyar nan fa jini take zubarwa
Cikin tashin hankali Abba yadubi momy yace kinga abinda nake fada miki ko?
Daddy kuwa baya um bare um um, hawaye yake sharewa kawai
Cikin sauri doctor ta karbeta sukayi asbitin cikin gidan
Babu Bata lokaci likitoci suka shiga Bata temakon gaggawa
(comments dinku yanayin kadan fan’s)
Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
28
Momy Sai zirga zirga take agaban Dakin da aka shiga da Amal, cikin zuciyar ta tana tsoron Kar yar mutane ta mutu ahannun su, mezasu fadawa iyayen ta?
Abba ne me yar nutsuwa acikinsu, daddy kuwa yana zaune Idanu sunyi masa jajir
Shi tunda yaji maganar momy tana cewa Amal na zubar da jini yasan cewa kawai shikkenan bari zatayi, shikuma haka Allah yayi shi bazaiga jininsa aduniyaba
Suna wannan Zaman jiran har tsawon wani lokaci
Doctor tafuto, Gaba dayansu kamar hadin baki suka nufeta suna tambayar doctor ya ake ciki?
Ta dubi daddy da gaba daya kamanninsa suka sauya
Tace ranka yadade babu damuwa zamu iya qarasawa office
Babu musu suka bita, Bayan tagama rubuce rubuce tadago tace alhaji gaskiya Badan anyi kokarin kawo ta asbiti da wuri ba da tuni cikin dake jikinta ya zube, muma kanmu munyi mamakin rashin zubewarsa kasancewar ta zubda jini mai yawa, Amma Allah cikin ikonsa ya temaka,kuma muma munyi bakin kokarin mu wajan ganin cikin be fita ba
Daddy Kasa boye ajiyar zuciyar sa yayi, Dan har saida yadora hannun sa Akan Kirjinsa yasaki wata nannauyar ajiyar zuciya yana qara godewa Allah
Momy tace to alhamdulillah, Abba ma yace to Allah mungode Maka
Doctor tace saide alhaji wani hanzari ba gudu ba, gaskya yakamata abarta tahuta, ina nufin ta bangaren zamantakewar aure, aikata wannan abun shine dalilin faruwar wannan matsalar