BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ahankali ya zare rigar daga jikinsa yakasan ce dagashi sai dogon wando da farar vest ajikin farar fatar sa
Toilet din yabita, yakamata ya riqeta saida ta gama sannan ya wanke mata Bakinta da fuskar ta, yariqota yanayi mata sannu suka dawo Cikin Dakin
Ajiyar zuciya take ita kadai?
Shahid yace sannu
Bata iya bashi amsaba illa daga masa Kai datayi
Yace meyake damun kine? Tace babu komai fiance

Yace no, tashi muje asbiti
Tace da gaske nake, Babu abinda nakeji, kawai qamshin wannan turaren daka fesa ne banaso
Kin tabbatar babu abinda yake damunki?

Babu komai fiance
Yace ok
Tashi yayi yacire wandon Jikin nasa yasauya wasu kayan, zuwa kalar brown manyan kaya, yabude cikin kayanta yadauko turaren data dauke
Yafesa sannan yaje kusa da ita yace wannan yayi ko?

Ahankali ta tashi ta rungume shi, tana shaqar qamshin turaren
Shide Shahid yana tsaye mamaki yana neman kashe shi
Ahankali yasa hannu ya rungume ta, suna tsaye ahaka har tsawon wani lokaci sannan yajata zuwa gadon yace ki kwanta ki huta to Nima zanje office

Riqeshi tayi tace ni inasan wannan qamshin please karka tafi
Babu yanda ya iya haka ya zauna agefenta, yana shafa Fuskarta
Ahankali bacci me nauyi yadauke ta
Tashi yayi ya kunna mata esi ya rufeta da blanket sannan yafice zuwa wajan aiki

  ***       ***       ***

Yau tunda safe tatashi tashirya, da kanta tashirya Dakinta, taci kwalliyar ta cikin doguwar Riga ta atamfa
Bawani daurin wahala tayi akanta ba, me sauqi tayi
Ta feshe jikinta da turare
Tafuto falo ta ganshi tsaf agyare

Abinci tazuba me mugun yawa, ta cinye shi tsaf
Zuwa yanzu harta saba da mugun cin abinci kamar yan kwallo
Kuma hakan bazai Hana anjima taci wani abincin ba

Tana gamawa ta dauki Wayarta zata kira daddy kawai kuma saita fasa
Takira maisah
Tana shiga maisah ta daga Kiran daga bangaren ta
Tace Allah Sarki yar’uwata yanzu nake cewa bari inkira me cikin nan inji Yaya take da cikin jikinta

Amal tace kede bari maisah wallahi nagaji da wannan Zaman
Jira nake wani yazo daga gida wallahi kafata kafarsa zan biyoshi mutaho gida
Nagaji
Maisah tace haba me ciki kwana nawa nema yarage

Cikin sauri Amal tace kede bazaki dena fadamin wannan sunan ba, kedinma kwana nawane kin samu naki

Ajiyar zuciya maisah tayi tace albishirinki, ai yanzu ma inada abina harna wata daya
Gani ya sham dina yana tattalina dana babynsa

Amal tace Karde ki fadamin magana wallahi, kinsan cewa Badan matsalar dana samu kwanaki Akan cikina ba, Babu abinda zai rabani da daddy nah

Kuma yanzu ma jira nake yazo, wallahi Dani zai koma

Maisah tace kinga ni wasa nake miki, garama de ki biyo abinki kudawo gida adora daga inda aka tsaya

Daria Amal Tasa tace kinga ni Sai anjima tun kafin ki fara shaqiyancin naki, Allah yarabamu da wannan abin lafiya, maisah tace to amin

   ***       ***       ***

Tun dazu yake tsaye a kofar kitchen din yana Kallanta tana aikinta cikin nutsuwa
Juyowar dazatai Sai ganin mutum tayi

Dasauri ta dora Hannunta Akan Kirjinta, tace oh wallahi harka tsorata ni
Shigowa cikin kitchen din yayi yana rungumota jikinsa yace sorry fiancee

Jug ta meqo masa cike kunun madara da kwakwa tace ungo kaimin wannan dining

Babu musu ya karba yakai, yadawo kitchen din yace Dame zan tayaki?
Albasa ta bashi da wuqa tace ungo yankamin wannan qanana

Karba yayi yafara yankawa, yanayi Idanu yana cikowa da hawaye

Qanshin albasar dataji ne yasa nan take wani irin Amai yataso mata, cikin sauri tayi waje da gudu

Kallan mamaki yabita dashi, sannan ya ajiye wuqar hannun sa ya wanke hannun yabi bayanta

Lokacin daya shiga Dakin harta gama tafuto daga toilet tana goge Fuskarta da towel

Baice mata komai ba, yadauko mata after dress ta dora Akan kayan jikinta yabata dankwalin abayar tayi rolling, suka kama hanyar fita waje

Suna Zuwa harabar gidan, yayi saurin Bude mata gaban motar tashiga, yazagayo yashiga yajasu Sai hospital

    ***      ***      ***

To babana harka shirya ne haka da wuri?karfe takwas fa yanzu

Kansa ya Sosa, yayi masifar kyau cikin farin yadin da aka yiwa ado da ash din zare
Babbar rigar ta karbi jikinsa
Hular kansa kala daya da takalmin kafarsa, sai tashin qamshi yake kamar wanda zaije wajan daurin aurensa

Yace momy ai gara inbi flight din dazai tashi da wuri

Tace to ai ka tsaya kayi break ko

Agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa ya kalla
Yace ai momy babu damuwa idan naje can sainaci

Kallan mamaki momy tayi masa tace, kace baka sanar da ita zakaje ba, tayaya zakayi maganar zakaci abinci idan kaje
Kaga muje Kaci abinci saika wuce

Babu yanda ya iya haka ya wuce dining yaci abincin kadan, momy tatashi ta dauko masa wata Leda tace gashi to saika Kai mata

Ai bazaku wuce sati biyu ba zaku dawo gaba dayanku ko?
Fuskar sa yashafa yace eto gamu nande momy, da inaso mu wuce Saudia ne daga can

Momy tace banasan shirme daddy, yarinyar da tsohon ciki zaka Diba kuyita tafiya yawo? Kabari idan Allah yadauke ta lafiya saikuje

Yace to momy saikun ganmu, kifadawa Abba idan yafuto nawuce

Cikin ranta tace yauga zumudi lale

Afili tace to zaiji, Allah yakaiku lafiya

   ***       ***      ***

Doctor ya dubesu yace inajin ku meke tafe daku?
Shahid yace wallahi narasa gane kanta ne doctor, yau tace batasan qamshin wannan Abu, gobe tace batasan qamshin wannan
Hartakai yau Albasa wannan da ake abinci da ita dagajin qamshin ta tafara Amai
Nace mata muje asbiti tace a a lafiya kalau take, shine nace yau de bari nakawo ta aduba ta agani ko batada lafiya ne?

Murmushi doctor din yayi yace Toshiknn bari Akira nurse tazo suje ayi mata text

Babu Bata lokaci nurse din tazo, sukaje akayi mata gwajin fitsari dana jini
Basufi minti talatin ba, likita ya baiyana musu cewa tana dauke da ciki tsawon wata biyu

Nan take farin ciki yakamasu gaba dayansu
Shahid yadaga hannu sama yana zubawa Allah godia
Haka suka taho gida cikin tsananin murna

Suna qarasawa gida shahida tayi hanyar kitchen, cikin sauri yace fiancee me zakiyi?
Tace abincin zan qarasa, yace inaaaa ai daga yau wannan aikin yadawo nawa, zauna kede kawai ki huta
Wayarsa yadauka yakira umma yafada mata ko kunya babu, sannan aka turawa momy text

Yakira number daddy taqi shiga alokacin suna cikin jirgi yakashe wayar, saiya kira Amal yafada mata yayarta tana daukeda juna biyu na wata biyu

Amal farin ciki kamar tayi me, qawa ciki, ga kuma anty shahida ma ta samu nata, Allah Sarki rayuwa

  ***       ***      ***

Da yamma Bayan tagama motsa jikinta, suna dawowa gida tayi wanka tasaka doguwar Rigar material medan fadi
Ta tattara gashin kanta ta daure da dankwalin rigar
Sai tashin qamshi take
Ta zauna afalo tana kallo, tanata sakin tsaki ita kadai wato yau Kiran wayar daya saba yima bazai nemeta ba, saide ita idan ta matsu ta kirashi kenan
Aikuwa bazata kirashi ba itama

Ita kadai de tana kallo dataga tunanin nasa bazai qareba saita dau wayar ta kirashi, Amma Kuma saitaji wayar a kashe

Afili tace to lafiya kuma yau yakashe wayar?

Sake gwadawa tayi still wayar a kashe, dole Sai hakuri tayi ta gumi tareda zubawa TV din Gabanta ido, Bawai Dan tana fahimtar komai ba

  ***      ***       ***

Jirgin su na sauka yahau Mota aka kawo shi har kofar gidan, tareda ambassador nigeria dayake qasar dakuma wasu tsiraran mutane, yana futowa suka sake gaisuwa dasu sannan yashiga cikin gidan cikin farin ciki

Da maigadi suka fara gaisawa sannan yanufi falon cikin takunsa na qasaita

Tana Nan a zaune tana aikin tunanin sa taji anturo kofar falon
Qin kallan kofar tayi, tasan bazai wuce doctor ko me aiki ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button