BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kayan jikinta tacire tasaka kayan bacci, Wayarta ta dauka taga maisah ta kikkirata, Bata jiba, saita duba taga ta turo mata message tana fada Mata ansa mata Rana da sham nanda wata daya biki, haka Amal de taita farin ciki Awannan lokaci sannan tayi bacci

  ***      ***       ***

Washe gari aka tafi da shahida jigawa, inda su umma suka karbesu hannu bibbiyu

Ankaita Dakinta, abokan ango suka rakoshi, su nazy nede da okasha, sai tsiya suke musu Wai fada ya zarce soyaiya

Haka Shahid de yakasa tanka musu, shi ya matsu su tashi su tafi koya sake da gimbiyar Tasa
Aikuwa suna tafiya, yacire hula da babbar Riga, ya yaye mata lullubin kanta, yafara janta da fira harta Dan sake dashi, sannan yakawo mata kaji da sauran lemuka sukaci suka Sha, yace ta tashi su gabatar da sallah

Suna idarwa ya kwararo musu addu’ah, sannan yace zata Iya zuwa ta kwanta tahuta, haka kuwa akayi, tana kwanciya Shima yatashi yaje ya kwanta

Shahida tayi tunanin babu abinda zai faru,shiyasa tasaki jikinta tana jinsa yamatso jikinta ya rungumeta , murya kàsa kasa yace amaryata, ahankali shahida tace na’am yace kikwantar da hankalinki kinji ?tace to

Tanaji tana gani yafara lalubarta , duk tatakure ta cure waje daya, tana tunanin wahalar da amal tasha, cikin dabara yace mata duk abinda nayi miki kema kiyimin kinji?

Girgiza kai tayi, yasake cewa amma idan bakimin ba , to zanyi wani abu, tace to

Haka yayi tayi mata wayo har yasamu biyan buqatars

Shahida Idanu suka Raina fata, Amma haka ta daure tayi hakuri, duk da taji jiki sosai

Saida komai yagama wakana sannan yatemaka mata, suka gyara kansu, shahida Sai shagwaba take zubawa, shikuwa Shahid duk ya rikice, sai abinda tace

  ***         ***       ***

After 1 month
Bikin maisah biki yazo, Amal taso daddy yabarta taje tayi ko kwana uku ne, Amma yaqi yarda, dole Sai ranar bikin aka kaisu

Daddy dakansa yagana da mahaifin maisah suka gaisa dashi sosai, dazasu tafi gidan su umma yabashi gudunmawar biki naira miliyan biyu

Haka iyayen maisah sukaita godia

Gidan umma suka wuce, wanda suka dade da tarewa asabon gidansu, Amal da suka hadu da shahida ake ta zubawa juna labari dakyar suka rabu

Haka suka dauko hanyar dawowa saboda dare

   ***      ***      ***

Suna zaune afalo suna breakfast Abba da umma Sai daddy da Amal

Abba yace hajiya opper Shahid ta aiki tafuto, kowanne lokaci zai iya farawa, harma da gida da komai na ma’aikata akwai
Amal naji tace wayyo Abba Dan Allah kace musu su dawo nan gaba daya
Abba yace yata ai wannan ikon yana hannun Shahid, Amma kisani nan da jigawa duk daya
Duk inda suka so zasu iya zama

Tace to Abba, aranta kuwa fadi take Allah yasa Yaya Shahid yayarda su dawo nan

Momy tace to alhaji Babu abinda zamu ce mukam ai Sai godia

Abba yasaki murmushi yayi shiru

Amal ce ta tashi, daddy yabita da kallo

Momy tace bade Harkin qoshi ba?
Cikin yatsina fuska tace momy naqoshi ne wallahi, abincin bayamin tes abakina, qarni ma nakeji

Daddy de yabita da kallan mamaki yakasa magana, tunda shide yasan kalau take cin wannan abincin, Amma Kuma yau tace qarni

Momy tace to jeki kwanta, kokuma kisa adafa miki abinda kikeso ko?
Tace to momy

Ta kalli daddy, ta wuce zata tafi daki, taji Jiri yadebeta, kanta yasara

Nan tafara baya baya alamun faduwa

Daddy ne yatashi Dasauri yaje yatareta, yace lafiya kuwa?

Su Abba ma suka taso, suna fadin lafiya Amal?

Amai taji yataso mata, cikin sauri ta qwace daga hannun daddy, taje toilet taita kwara Amai

Tana futowa ta kwanta Akan gado Bata koma falon ba

Acan falo kuwa Abba ne yasa daddy yakira doctor,daya tashi Kiran saiyasa aturo masa mace, doctor na zuwa suka bita cikin Dakin

Tana kwance, a gado, tana ganin su ta tashi zaune, doctor ta duba ta, sannan tace ta kwanta tahuta

Tajuyo ta kallesu tace alhaji congratulations Her Excellency na dauke da juna biyu na Tsawon sati biyar

Comments

Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

26

Daddy najin haka yayi saurin tsugunna wa yayi sujud shukhur
Saida yagodewa ubangijinsa sannan yadago

Abba ya washe baki yadubi doctor din yace a a masha Allah, Wai likita abinda kika fada din hakanne da gaske?

Doctor hauwa tayi murmushi hakane alhaji, haka bincike ya nuna

Abba yace to ai likita kema baza’a barki hakaba, saboda haka kituromin da account number dinki, zakiga kyauta mai tsoka

Cikin farin ciki tace to alhaji insha Allah

Momy ma datake ta farin ciki, tace ai alhaji wannan kyauta Nima baza’a barni abaya ba, ta dubi doctor hauwa tace doctor ki shirya insha Allah dake za’ayi hajjin Bana

Doctor cikin daria tace gaskya hajiya nagode sosai, haqiqa zanso Naga wanne yaro kokuma yarinya za’a Haifa

Momy tace ai mukam duk abinda muka samu bamuda zabi doctor

Doctor hauwa ta gyara glass din idonta tace gaskya ne, yanzu zanje nahado mata magungunan dazata dinga Sha, zai taimaka mata sosai wajan Jin sauqin jikinta, sannan hajiya Dan Allah adena barinta tana ayyuka dayawa, abari Sai cikin yagama qwari tukunna

Momy tace a a karki damu doctor insha Allah za’a kiyaye

Bayan fitar doctor ne, Abba yanata fara’ah yace a a masha Allah Abu yayi kyau, yadubi Amal Yace Amal?

Cikin sauri ta rufe idonta da tafukan hannayenta, Abba yajuya yafice

Momy ta kalleta tace to me kikeso adafa miki ne yanzu Amal? Kanta aqasa cikin kunya tace babu komai momy, banajin yunwa

Momy tace Toshiknn ki kwanta ki huta kinji, itama tafice daga Dakin

Yana ganin fitar momy yahau gadon tare da rungume ta, itama tayi luf ajikinsa
Yashafa Bayanta yace baby nagode sosai

Itama cikin sigar kissa tace a a Yaya daddy Allah zaka yiwa godia

Yace shi nafara yiwa baby, abin kamar almara nine zan baba

Cikin farin ciki ta kalleshi tace kakusa zama daddy ba
Cikin farin ciki yace dama daddyn ne, Amma marar yara
Gaskya bansan wacce irin godia zanyi wa mahalicci naba, yau nine matata take dauke da ciki akaro na biyu

Shafa fuskar ta yayi yace Allah yarabaki dashi lafiya babynah

Amal tasan yatuna da salma ne, yana tsoron itama kada ta mutu shiyasa yayi wannan maganar

Gashin kansa ta shafa tace ka kwantar da hankalin ka, duk wanda kaga yarasu kwanan sane yaqare
Addu’ah zamuyi mata Allah yayi Mata rahma

Cikin sanyin jiki yace amin

Me kikeso asawa Yaron dazamu Haifa? Ina nufin wanne suna kike so?

Jim tayi alamar tunani, sannan tace Kasa sunan Abba idan namiji ne ai yayi ko?

Shima cikin alamar tunani yace eh yayi, Amma nida abinda nake tunani shine musa sunan Shahid
Cikin mamaki tace meyasa Yaya daddy?
Yace saboda yayi jinkirin fada miki yana qaunarki, Sanadin hakan nikuma nasameki

Murmushi tayi tace, Yaya daddy kenan, musa sunan Abba, idan Allah yabamu wani Yaron Sai Asa sunan Yaya Shahid din

Daddy yace Toshiknn, Amma Kuma idan mace ce wanne suna kike ganin yadace mu saka mata

Kai tsaye tace Salma

Kallan mamaki yayi Mata, tace gashi Nima Sanadin ta nasameka, nasamu mijin da bantaba tunanin samun kamarsa ba

Cikin farin ciki daddy yace um me kikace? Dan sake fada please

Babu kunya tace Yaya daddy nace nasamu mijin da ban taba tunanin samun kamar saba

Yace Dan Allah kidena cewa Yaya daddy dinnan haba baby

Tace Toshiknn my dear

Bakinsa yakai saitin wuyanta yayi kissing sannan yace I luv u, tace I love you too

Wayarsa yadauka yakira jb
Daga daya bangaren jb yace abokina ya akai?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button