BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shikuwa yana futowa, kujerar da Amal ta zauna yaje Bayan kujerar ya tsaya, hannayensa cikin aljihun wandonsa

Yana kallansu, yarasa meyasa yakeji aransa yaran nan suyi suyi sutafi

Amal cikin dar dar tace momy ga yayanah Yaya Shahid, momy tace Allah Sarki, aikuwa ga kama nan, ta dubi Shahid din tace yasu umman naku?

Amal tacika da tsananin mamaki
Shahid yace suna nan lafiya, sunce agaida ku

Daddy kuwa kallansa yake, cikin ransa yace babu laifi Yaron yahadu ba qarya
Ganin yanda gaba daya hankalin Shahid yana kan Amal ne yasa ahankali yadawo kujerar da Amal take zaune yazauna dab da ita, cinyarsu na gogar tajuna, ta Bayanta yakai hannun sa ya rungumota kadan zuwa jikinsa

Gabanta ne yake faduwa, me Yaya daddy yake shirin yi ne haka?

Kallansa take yayinda Shima yazuba mata ido kamar yau ne Karo na farko dasuka taba ganin juna
Cikin murmushin daya mutuqar saka Amal mamaki yadubeta yace

“kinata surutu baki kawo musu ruwa ba? “

Kallansa tasake yi sosai, takasa magana, yau daddy ne yariqeta haka Kamar wani masoyin da za’a qwace masa budurwa?

Tashi zanyi momy cikin sauri tace a a Amal yi zamanki, nan tafara qwalawa me aikinsu kira
Raliya!
Raliya!!
Dasauri Raliya ta futo tare da rissinawa,
momy tace Raliya me kike haka kika bar baqi babu ruwa babu drinks?
Yi hakuri hajiya, bari akawo
Tana juyawa shahida tafuto, fuskar ta babu yabo babu fallasa, ta zauna kusa da momy

Kallan su Shahida tayi kamar ba itace tashiga da kuka ba, sannun ku da zuwa, Shahid kamar bai santaba agajarce yace yauwa
Cikin ransa yace
Meyasa meta duk ta rame haka?

Nazy kuwa daya Kasa boye mamakinsa yace shahida ashe anan kike?
Da murmushi afuskar ta tace nazy anan nake

Amal da aka yiwa dabaibayi cikin mamaki ta dubi Shahid tace yayanah? Dama kunsan juna ne?

Murmushi yasaki yace nasanta a school dinmu

Amal tace ok,Allah Sarki ai ban taba saniba
Shahid qara kallan daddy yayi yanda yawani qanqame Amal, kana kallan qwayar idonsa zaka hango kishi qarara, baisan cewa shi yariga yadau qaddarar saba tarashin Amal, kawai de qanwar tasace bayaso, kuma shi soyaiyar nan de ba ayi dole

Raliya ce tafara jera kayan motsa baki, Babu Bata lokaci gabansu Shahid yacika da sinadarin sanyaya maqoshi

Zata fara zuba musu shahida tace barshi Raliya
Ahankali tataka har inda suke ta miqawa nazy, yace thanks shahida

Shahid ta zubawa ta miqa masa, yazuba mata ido, kamar bazai karba ba saikuma ya basar ya karba baice mata uffan ba
Suna Sha momy tace Shahid Amma ai anan zaku kwana ko?

Gaban daddy ne yafadi, kwana? Kuma anan gidan? Ko dayake aiba damuwa tunda su sunada wani gidan

Shahid yace a a hajiya yau nakesan komawa jigawa insha Allah, tace Toshiknn Amma kashirya next time idan kadawo anan zaka kwana, Shahid baice komai ba Sai murmushi

Amal tace yayanah, Ya baba yake? Dafatan de yanzu Yadena rigimarsa ko?
Shahid yace a a yana Nan ai saide in ba’a taba Kiba
Gaba daya sukasa daria,shida ita
shahida kuwa wani irin dadi takeji yau Shahid a gidansu

Saqonta yabata yace gashi mu zamu wuce, Dasauri ta tashi, Dan dama amatse take da wannan Zaman na daddy agefenta

Momy ce tayi ciki Dasauri, shahida ma tabita

Amal tace Yaya muje na rakaka,hannu suka miqawa daddy dukansu sannan suka fita

suna fita daga falon yatashi yakoma Jikin labulen window yanda zai dinga kallansu

Momy tabawa ma’aikatan kaya masu yawa tace abawa su Shahid, kayaiyaki ne su atamfa da less masu tsadar gaske, na umma Sai kuma turare na baba
Sai nashi agogo mai shegen tsada da shadda

Da farko Qin karba yayi, saida Amal tace ya karba, tace yayanah Dan Allah ka gaida su ummatah, Kallanta yake da murmushi yace zasu ji, but Bama Lalle na samesu ba Dan sunce zasuje kano gidansu okasha su yiwa mahaifinsu godia, Amal ta eh gaskya Kam yakamata, Nima ai nakusa zuwa Yaya

Daria yasa yace ke kina cikin wannan sojojin inake Ina fita, yauwa namanta acikin saqon ki umma tace akwai wani magani kidinga Sha da daddare kafin ki kwanta, bansan kona mene ba na tambayeta taqi fadamin, but inaga de na tsari ne baba yayi miki
Dan Naga alama wannan gidan naku saida neman tsari, idan aka sako mutum a gaba da naci

Kallan rashin fahimta tayi masa, tace Yayanah, me kake nufi?
Da murmushi afuskar sa yace nida masu gadin can nake
Sakin Fuskarta tayi tace ok, juyowar dazatayi tayi ido biyu da daddy dayake tsaye ajikin window, da kansa yayi Mata alama data dawo ciki

Allah yaso Shahid bai lura ba, Dan haka sukai sallama cikin sanyin jiki tadawo ciki
Tana zuwa falon anan taganshi yana aikin zageye falon, Kallansa tayi fuskar sa tadawo kamar da atamke

Tashare shi tashige dakinta

Saida yaga shigarta daki sannan Shima yakoma dakinsa

Da daddare Amal tafuto zataje kitchen tasamawa kanta abinda zataji, tafuto da flate din ahannun ta, saiga shahida, cikin ranta tace shahida ganinki ba alkhairi ba, Shahid ta zauna dab da Amal, Amal kuwa ta dauke abincin ta zata tafi daki,
Riqeta tayi tace Amal, magana zamuyi

Cikin dakiya Amal tace inajinki
Amal Dan girman Allah kiyafemin, haqiqa nasan nabata miki abaya, Amma kuskure ne da aikin shedan Dan Allah kiyi hakuri ki yafemin

Amal inasan yayanki tun muna school, Amma baya kulani, baya sona, kuma baya qaunar ganina Amal, Amma Naga tsantsar soyaiyar ki acikin Idanunsa, idan kikai masa magana nasan zai Soni

Amal kokin San a dalilin qaunar yayanki nashiga wannan halin? Nakamu da ciwon hawan jini

Riqo hannun Amal din tasakeyi cikin kuka tace Dan Allah Amal

Amal da mamaki yacika ta cikin haushi da takaici ta Fizge hannun ta, har hakan yayi Sanadin faduwar flate din Hannunta tace shahida me kike ce?

Yana dakinsa yaji qara Dan haka Dasauri yafuto, yanayin daya gansu aciki ne yasan cewa babu lafiya Dan haka yaja yatsaya yana kallansu daga nesa

Amal tace kin manta cin mutuncin da kikamin shahida? Har gida kika debo kawayanki kukazo kuka tozartani

Shahida cikin kuka tace Amal……
Itama Amal din kukan Tasa tace Dan Allah kimin shiru shahida bakida abinda zaki fadamin, tajuya dakinta da gudu tana kuka, yayinda shahida ta tsugunna awajan tana wani malalacin kuka

Yana gama kallansu yaja kofar dakinsa yarufe, yafada duniyar tunani
*** *** ***
Suna zaune adakin Abba momy tace alhaji yaufa baqi mukai bakanan yayan Amal yazo tareda abokinsa, Amma Kuma hajiya kukasa sanar Dani?
Kama hannayensa tayi tace alhaji kayi hakuri aikasan baka Gari, sannan banasan katse Maka ayyukan dasuke gabanka, Abba yace eto hakane kuma, to dafatan de babu damuwa sun koma kalau ko?
Tace alhmdlh sun koma lafiya, Amma Kuma saide akwai matsaloli guda biyu , cikin tashin hankali Abba yace subhanallah hajiya meyake faruwa kuma ?
Alhaji jinyar shahida fa wani yaro ne take so shikuma baya Santa, sannan yau yayan Amal yana zuwa shahida tana ganinsa tace shine Yaron da take so, Abba yace tofa
Shine nace alhaji meze Hana kayiwa mahaifinsa magana inyaso ayi tuwona maina?
Abba yace hajiya idan muka bashi ita, Bayan kuma bayasanta to bamu siya mata yanci awajansa ba, ta dage da kanta da dabarar ku ta mata tashawo kansa ya amince, inyaso saina yiwa mahaifinsa magana

Cikin sanyin jiki momy tace Toshiknn alhaji, Amma wlhy ni har yanzu nama Kasa yiwa yarinyar magana, Gaba daya kunyar ta nakeji
Abba yace hakane, to kinga abinda nake nusar dake akai tunba yauba, insha Allah komai zaiyi normal, BURINAH Inga kowa de acikinsu yana cikin kwanciyar hankali

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button