BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tafiyar awa hudu ce takawo su Garin, daddy banda haushi babu abinda yakeji aransa, yarasa me Abba yake nufi dashi

Iso yasa ayi musu wajan Malam hamani, Babu Bata lokaci yace su shigo

Su kadai suka shiga falon ko’ina kalau dashi fes fes, security kuwa wasu sun tsare motocin wasu Kuma sun tsaya abakin kofa

Baba hamani yana ganinsu yagane Abba, nan da nan yamiqawa Abba hannu suka gaisa

,daddy ne yaqura masa ido, daka ganshi kaga cikakken buzu, saboda rawanin dayayi akansa na buzaye, fuskarsa babu yabo babu fallasa ya tsugunna har qasa ya gaidashi
Sosai baba hamani yaji dadin hakan

Bayan sun zauna ne yace alhaji bari akawo muku ruwa

Yana shiga gida yace wa umma Samia, takawo musu ruwa

Ruwan pure water ta dauko masu Dan karan sanyi, tazuba aflate mai kyau
Tadoshi Dakin da Amal take tace tashi kikaiwa baban ki yayi baqi

Babu Bata lokaci tasaka zumbulelen hijabinta tadaura niqab dinta tadau ruwan tatafi

Cikin zazzaqar muryar ta tayi sallama adakin, kansa asunkuye yake bai dagoba bare yaga mamallakiyar wannan zazzaqar muryar

Saida tace Ina wuninku sannan yakai dubansa gareta, Abba ne ya amsa, shikuwa gogan idanu yazuba mata

Ikon Allah ga murya har murya Amma Kuma fuska a nakashe, ita kuma Tata kaddarar kenan, inajin matsalar a idonta take kokuma abakinta

Shi kadai yake zancan zucinsa

Tana basu ruwan tajuya tayi cikin gida

Abba ne ya karantawa baba hamani matsalar daddy, Babu Bata lokaci baba hamani yatashi dakansa yahada shayi, yazuba wani Garin magani aciki

Yamiqawa daddy yace gashi kasha

Kwarjini tsohon yayi masa Dan haka babu musu yakarba yashanye shayin duka

Baba hamani yadubi Abba yace alhaji karka damu insha Allah za’a samu waraka

Abba yace mungode Malam, Jim yayi yana wani tunani aransa Dan haka yadubi daddy yace jeka Mota kajirani, Babu musu yatashi yatafi

Abba yadubi baba hamani yace wato Malam wata buqata ce Dani danake nema awajanka babba

Baba hamani yace alhaji ku fadi buqatunku

Wato Malam wannan Yaron shine da awajena Nabiyu, kwanaki matarsa Allah yayi Mata cikawa a dalilin haihuwa, wanda in baka manta ba anan mu kazo nakarbi magani awajanka

Baba hamani yadauka girgiza kansa alamar gamsuwa

Abba yaci gaba da cewa to a halin yanzu an tsaidashi takarar gwamnan jihar damuke, to bashida aure babu wani mutum nagari dazai zabi shugaba marar iyali, da dattako

Shiyasa nakeso idan babu damuwa kuma baka yiwa yar wajanka Amal miji ba inaso kabawa dana aurenta

Baba hamani yace Allah yaji qanta da rahma, alhaji na tausaya wa danku mutuqa
Kuma Amal banyi mata miji ba

Dan haka nabashi ita duniya da lahira

(Allah yaji qanki salma, wallah karaam yasani qwallah lokacin typing din nan????????????)

Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

8

Murmushi ne abaiyane asaman fuskarsa, yamiqawa baba hamani hannu suka sake gaisawa
Yace nagode Malam nagode sosai
Insha Allah idan naje gida, magabatansa zasu zo ayi komai agama alokacin banasan kada aja lokacin
Baba hamani yace babu komai alhaji ai temako ne
Kudi ya ajiye masa dami guda, sannan yatashi ya fita

Yana shiga motar ya kalli gefensa daddy ne a zaune ya lumshe idonsa

Murmushi yasaki cikin ransa yace wannan halin de yakusa qarewa da iznin Allah

  ***     ***     ***

Samia kinji abinda na yanke, Amma Malam kasan de halin yaran zamani Shiba Santa yakeba, itama haka, sannan Malam yaran nan bataba haduwa sukai sukaga junaba
Hakane Samia, Amma abinda zaki duba Samia ceto mukayi, shi wannan Yaron abin atausayawa ne, matarsa ta rasu Samia, mutumin daya saba da iyali ace yau babu su dole zai shiga damuwa, sannan Yaron yakusa shekara bakwai yanasan haihuwa Amma Kuma Allah Bai bashi ba
, tunda Allah ya hore mana abinda zamu iya temakon sa ai abin yazo da sauqi, ita kuma Amal mune muke da ikon zaba mata miji ba ita ba

Abinda bazan dauka ba daya ne Samia, wulakanta Amal, muddin akai auren nan tacemin yana mata ba dadi takalmina zansa inje har gida inci ubansa nasako yata agaba mutaho

Umma tayi shiru, tasan Sarai zai aikata, fatanta daya Allah yasa abinda take tunani bashi bane tsakaninta da Shahid

Tace to Malam, yanzu kasanar wa yayanta ne?
A a Samia ban fada masaba, zande sanar dashi idan ansa lokacin bikin insha Allah
Umma tace to Malam Allah yakaimu

 ***     ***     ***

Amma alhaji wannan wacce irin magana ce ka nema masa aure batare daka sanar dako daya daga cikinmu ba
Kuma ma yarinyar yar Malam, haba alhaji, yanzu fisabilillahi azo ace za’a yiwa daddy aure ma atambayemu yar waye kawai saimu Bude baki muce yar Malam ce
Haba ai da kunya, kamarsa yarasa wa zai aura Sai wata yar Malam

Wato hajia Naga alama kina yawan mantawa da bayanmu, Toni muddin Naga talaka Naga me kudi, to Abu daya nake daukar su
Da talaka Dame kudi duk Allah ne yayisu, Kai kanajina ko?
Daddy da idonsa yakada yayi jajir yadago yazubawa mahaifin nasa ido, yace nariga nayi magana da mahaifin yarinyar
Sai ince ma ai kamar kaganta ko? Yarinyar data kawo mana ruwa mukasha jiya?
Kansa ya girgiza alamar eh
Yaci gaba da cewa to alhmdlh, anbaka ita, Dan haka kaje kafara shiri, kafin afara shirin Zabe za’a daura auren, da fatan babu matsala?

Matsala? Yanzu shi Abba yake tambaya matsala? Arasa wa za’a aura masa Sai wata yarinya da in yayi hasashe ma yasan ya haifeta, yarinyar ma nakasashshiya, inba nakasa ba meyasa zata dinga boye Fuskarta, Abba bazai ganeba Amma irin wannan yaran munafukai ne wallahi

Kayi shiru, kokuma kaima maganganun mahaifiyarka ne yashiga kunnanka yayi ma huduba?

A a Abba nagode, Allah yasaka da alkhairi, banda BURIN daya wuce inbi umarnin ku

To dade yafima, zaka iya tashi katafi

Tashi yayi yatafi, jikinsa sanyi kalau
Yana zuwa dakinsa yafada kan gadonsa gamida rufe idonsa

Allah Sarki salma, meyasa kika tafi, yau gashi za’a aura min yarinyar da ahaifema mun haifeta

Bade auren bane, to suyi, zata gaji da zama tatafi gidansu, toda yaushe ma Salman tatafi dahar za’a mata kishiya

 ***     ***     ***

Hi
Dago Kai yayi ya kalleta, tace magana nakeso muyi idan bazaka damuba
Okasha yace ok inajinki, wancan abokin naku
Tayi masa nuni da Shahid dayake nesa dasu, yace inajinki

Wallahi Sansa nake, meze Hana kahadani dashi, ok Tome kikeso daga gareni?
Number sa, yace ok, gashi, tana rubutawa ta tashi tace nagode sosai dan’uwa
Yace no karki damu

Next day
Da sassafe ta kirashi, kamar wasa yaji muryar mace, tace bawan Allah magana nakeso muyi, yace inajinki

Wallahi tun lokacin dana fara ganinka, naji ka kwanta min, idan bazaka damuba zanso mu qulla soyaiya atsakanin mu

Um duniya kenan, Lalle duniya tazo karshe, yanzu matane suke neman maza

Yace cigaba inajinki
Tace Dan Allah ka temaka kasoni, wallahi ban taba son wani da namiji ba kamar ka, idan bazaka damuba zanso muhadu gobe kaganni

Yace babu damuwa Allah yakaimu, daga haka yakashe wayarsa

Nikam shahida kina bani mamaki wallahi, kamar ki kina bibiyar wannan gayen
Jamcy bazaki gane bane wallahi Ina Sansa da gaske

Kafada jamcy ta daga alamar ko oho

  ***      ***      ***

To Malam kaji abinda yake tafe damu, Malam yace eh gaskya ne munyi magana dashi, kuma yakirani awaya yafadamin Kuna tafe
Sake sabuwar gaisuwa sukayi, yatashi yafara gabatar musu da abinci da Sha, sai Bayan komai ya lafa ne, suka gabatar masa da kudin gaisuwa dana Saka Rana, Babu Bata lokaci aka sa sati biyu masu zuwa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button