BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Alhaji sidi yace ainine da godia Malam, okasha shi kadai na mallaka, ta Sanadin ka dakuma temakon Allah Yarona yazama cikakken mutum

Ai babu abinda zance dakai Malam Sai godia

Sannan shikuma Shahid kafada masa yazama ready, banaso su qara one week a qasar nan

Mrs Usman ce ✍????????????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

5

Alhaji sidi bai Bata lokaci ba wajan karbar takardun shahid yatafi dasu gida wato Kanon Dabo, inda yafara cuku cukun nema musu school shida dansa

Baba hamani yana shiga gida yafadawa samiya wannan labarin, bakinta har kunne saboda tsabar murna
Amal ce ta futo daga daki Jin umma Sai hamdala take tun dazu
Tace umma me a kayi ne yau?
Nan umma tabata labari, Amma abin mamaki maimakon tayi murna kawai saita juya daki, iyayan babu Wanda ya lura da halin datake ciki, kasancewar suna cikin farin ciki

Tana shiga daki tafada kan yar madedeciyar katifarta tadinga kuka, Yaya Shahid zai tafi karatu, to dawa akeso taci gaba da rayuwa?
Kafin zuwa magrib zazzabi mai zafi yarufeta

 ***     ***     ***

Yauwa hajia maimuna kawai kowanne kikawo dozin daidai mugansu, eh namaza dozin daya na matan ma haka, tunda bamusan me za’a Haifa ba
Abba yayi sakare yana kallanta da mamaki

Tana ajiye wayar datake tajuyo tace alhaji barka da dawowa
Wai hajiya, mezakiyi da kayan yara ne naji kina cewa akawo miki dozin dozin
A a haba alhaji, ya zakace me zamuyi da kayan yara
Ai gara mufara tarawa tun yanzu,
Abba yace wai kina nufin cikin sati biyun za’a fara yiwa siyaiya?
A a to alhaji so kake Sai an haifeshi sannan mufara siya

Dariya yasaki yace gaskya wannan jika naki zaiga gata
Tace ai alhaji kaide kawai Allah yakawo shi lafiya
Abba yace amin hajiya
Daga daki ta futo taci Riga da wando, kayan sun kama mata jikinta sosai, kasancewar batada jiki sosai Sai kayan sukai mata Das ajikin ta, tayi fakin gashin kanta dayasha gyara, tana zuwa tafada Jikin momy juwairah, cikin shagwaba tace momy Dan Allah kifada masa kinji

Hajiya tajuya tace to alhaji kaji, Wai yar lelen nawa tace adan daga mata kafa zuwa next week saita koma hutu

Abba yace hajiya yarinyar nan kina sangartata dayawa, mezatayi inta zauna agidan? Banasan sakarci ta tattara yanata yanata Takoma school jibi, already sun fara lecture, daga kanta tayi daga Jikin momy juwairah tace Allah Abba basa farawa da wuri, yace banasan Jin komai, tunma kafin daddy yasamu labari ki shirya kibi flight din dazai tashi jibi, banda yawo da qawaye babu abinda kika iya, Dan haka karna sakejin maganar cewa Wai bazaki school ba

 ***     ***       ***

Yana dawowa daga filin ball, wanka yashiga, yaje masallaci sallah, sai Bayan an idar ne ya hadu da baba hamani, baba hamani bai Bata lokaci ba wajan fada masa yanda sukai da alhajin dayazo dazu, yace to baba Allah yasa hakane yafi alkhairi, daga haka bai qaracewa komai ba, suna shiga gida yayi cikin dakinsa, yarasa me yake masa dadi, Anya kuwa zai iya rayuwa batare da Amal ba? Yarinyar daya reni qaunarta acikin zuciyar sa tun batasan kanta ba, Rana daya kwatsam ace yaje yayi wata rayuwa batare da ita ba? Anya yayiwa zuciyar sa adalci kuwa?
Zumbur yamiqe tsaye yayi dakinta, gara yaje yaga halin datake ciki, duk da yar tsamar dasuke da ita Akan wasiqar Malam nura

Yana zuwa kofar Dakin yace in shigo? Yaji shiru yasake fada second time, still yaji shiru, Dan haka yasa kansa ciki

Yana shiga kuwa yaganta akwance, Dasauri ya qarasa gareta, yace qanwata
Dakyar ta Bude lumsassun idanunta ta kallashi, hakan datayi shiya haddasa masa shiga cikin wani Hali

Matsawa yayi ya zauna a gefe daya daga kan katifar Tata yace ki tashi zamuyi magana
Tana tashi data ganshi Sai maganar ummah ta Fado mata arai, aikuwa batayi wata wata ba ta fada jikinsa tasaki wani kasalallan kuka

Yasalam!

Abinda yafada aransa kenan, wannan yarinyar karta hauka tashi

Bayanta yake bubbugawa alamar rarrashi, tayi luf acikin kirjinsa, idanunsa a lumshe, yace kiyi shiru mana
Koso kike Nima kisani kuka? Bata iya maganaba illa girgiza Kai datayi

Yace meyasa kika shigo daki ke kadai kikabar umma afalo?
Cikin sigar shagwaba tace Yaya Wai tafiya zakai nanda sati daya? Yaya please karka tafi kabarni, dago da kanta yayi still tana kwance ajikinsa
Suka qurawa juna ido
Kenan taji maganar tafiyarsa shiyasa itama tashiga wannan halin

Ahankali yabude kyakkyawan lips dinsa, ya matso da bakinsa daidai nata, tamkar zai hade bakinsu waje daya

Cikin kasala yace bakyaso intafi?

Lumshe idonta tayi ta Bude alamar hakane

Yace to kiyi hakuri kinji qanwata, insha Allah duk inda naje zaki kasance anan dina

Yafadi haka yana yi Mata nuni da kirjinsa gefen da zuciyar sa take

Amal BURINAH akoda yaushe shine inkasan ce tare dake, infaranta miki, insaki walwala

Amal
Tace na’am Yaya
Yace kiyimin alqawarin har in dawo bazaki saurari kowaba, har yanzu ke yarinya ce, baki Kai matsayin dazakiyi soyaiya ba
Dakaina zan nema miki mijin daya dace dake kinji?

Jikinta ne yayi sanyi Jin kalaman sa, dayaji tana kula Yaya sham to inajin da saiya daketa

Yaya nayima alqawari babu Wanda zan saurara, Nima BURINAH shine in yima abinda ranka yakeso

Kinyi alqawari? Nayi ma yayanah

To muje inbaki abinci, Kisha magani
To yayanah, Sarai ta ware suka fita daga Dakin

 ***     ***     ***

After 2 weeks
Tafiyar su Shahid ta tabbata, inda aka gama musu komai da komai shida okasha
Umma da baba da Amal ne suka rakashi har airport
Okasha yana kallansu, shiko ajikinsa, asalima Bluetooth ne akunnansa yanajin waqa
Lokacin da aka kirasu shiga jirgi Amal kuka Shahid kuka

Umma cikin ranta tanajin tsoron wannan al’amari na Shahid da Amal

Amma Allah yasa ba abinda take tunani bane

Suna shiga jirgi, Babu Bata lokaci suka Lula Indonesia, saida su Amal sukaga tashinsu sannan suma suka dau hanyar dawowa gida, suna shiga Mota ta riqe kanta da hannun ta dayake barazanar tsagewa,
Bayan sun dawo gida saida umma tayi da gaske sannan Amal tadan saki jikinta kadan, shikkenan babu Yaya Shahid, Babu meyi mata wasa, Babu me rarrashinta, Babu me tsokanar ta, sai hawaye
, Allah ya kyauta, abinda umma tace kenan taci gaba da abin gabanta, duk da itama taji ajikinta wannan Tafiyar ta Shahid

    ***     ***     ***

Suna sauka suka hau taxi ta kaisu gidan dazasu zauna kusa yake da school, kasancewar okasha kansa awaye yake basa shan wahalar komai, darana suka sauka Dan haka suka shirya zasuje makaranta su qarasa registration daga nan kuma suje su siyo Sim card domin Kiran yan gida

Bayan sunyi wanka, okasha yashirya dawuri ya zauna yana jiran Shahid, yayi kyau cikin qananun kaya

Yana Zaman jiransa Sai gashi yafuto da yadi ajikinsa Riga da wando rigar tsawon ta har qasa, ko hula babu yace masa muje

Okasha baisan lokacin daya tuntsure da daria ba, yafara nuna shi da hannu, haba gaye, ya za’ai Kasa wannan kayan Dan Allah

Shahid dayakejin wani daci aransa saboda rabuwarsa da Amal yace okasha please tashi mu tafi Dan Allah

Okasha yace to kaga Ina zuwa, dakinsu yaje yabude jakarsa yadauko wasu arnun kaya qanana, jar Riga, baqin wando, yace gashi Kasa wannan kafin muhuta zuwa gobe muje shopping Dan Nima banzo da wasu kayaba

Shahid yace kagani babu wani kaya dazansa Malam kawai muje

Dakyar okasha yasa Shahid yasaka kayan, sannan yabashi wani agogo yasa qirar Gucci, saiga Shahid harta taje lallausar sumar kansa ta buzaye mai kama da ta yan hindi
Dasauri suka futo saboda basaso suyi latti basu tsaya ko Inaba Sai University of Indonesia

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button