BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kamar wasa taji, alamar yana kuka

Dasauri tace Yaya kuka kake?
Cikin shashshekar kuka yace Amal Yaya zanyi da soyaiyarki?

Innalillahi karde zancan su umma da gasken ne

Cikin kuka nace nashiga uku yaya

Yace Amal, Babu yanda zanyi, dole in hakura dake
Tunda baba yariga yayanke hukunci
baba yayimin komai Amal, BURINAH inso abinda yake so Koda kuwa ba shine ra’ayina ba

Yaya kayafemin kula Yaya sham danayi
Insha Allah bazan sakeba Yaya nayi laifi
Amma Yaya wallahi banasan wannan mutumin
Banasan sa Yaya
Please Yaya kadawo baba yayi mana aure

Hawayen idonsa yagoge yace bazai iyuba Amal, bazai iyuba, karmu maida mahaifinmu mutumin banza

Wayar sa yakashe yana goge hawaye
Kamar wasa okasha yaji kuka, yana juyawa yaga Shahid yana goge hawaye
Subhanallah, Shahid meyake faruwa?
Kamar jira yake a tambayeshi nan yaci gaba da kuka haiqan, yana cewa shikkenan narasata okasha

Okasha narasa Amal, yarinyar nan da soyaiyarta na rayu acikin zuciya ta

Jikin okasha yayi sanyi,ya janyo shi jikinsa yana rarrashinsa

 ***     ***     ***

Ungo wannan karbi Kisha, umma menene wannan din? Bansaniba yarme tsinannan surutu
Bata qara maganaba takarbi maganin ta shanye
Umma zanje gidansu rumaisa, bazaki ba, kije nan gidan hauwa’u tana neman ki
Babu yanda ta iya haka zura hijabin ta tatafi, tunda bikin nan ya matso ake dirka mata wannan magungunan, tarasa na menene
Ko duk Dan wannan gunkin sukeyi oho

Tana zuwa gidan anty hauwan ma, magani tahada mata tasha, wani kuma tabata su aleda Wai tanasha kullum idan ankaita bauchin
Koba bauchi ba
Zasuga bauchi

 ***     ***     ***

Alhaji kaide kadage Akan auren nan, wallahi kuwa hajia, aure kamar anyi angama insha Allah

Yatsina fuska tayi, tayi shiru batare data qara cewa komai ba

Ina agogon nan nawa?
Wai agogon daka siyo a Qatar kaida president?
Eh shi bani shi,
Tana kawo masa yasaka, yagyara Zaman babbar rigar sa, ya kalleta yace Toni ke kin zauna ko yau bazan samu afesa min turaren ba?

Batace komai ba ta tashi tana cika tana batsewa, tafesa masa, yace yauwa kokefa

Angama saka akwatunan acikin motar?
Eh angama alhaji
Tosh mu muntafi saimun dawo, shi daddy yacemin yana jiran
Jabir, jirgin su zai sauka nanda 20 minutes
So zasu biyo mu daga baya

To alhaji Allah yakaiku lafiya, Allah yatsare Amin hajia
Yana fita suka shiga motoci shida tawagar yan daurin aure, basu zarce ko Inaba Sai jigawa state

 ***     ***     ***

Jb, Babu inda zani, Akan wannan qanqanuwar yarinyar zanje indebowa kaina gajia, wallahi bazaniba

Jirgin ku yasauka da niyya nace masa Kai nake jira

Haba daddy, Abba nefa, meyasa zakai masa qarya? To Jb ya zanyi? Wai kasan yarinyar dayake shirin aura min ne? Yaushe ma Salman ta rasu?
Yarinyar fa batafi shahida ba, haba me zan tsinta ajikin ta?
Daria Jb yasaka
Yace a a fa daddy karka zo kana qaramar murya daga baya

Kai yarinyar fa nakasashiya ce, wallahi batada lafiya, liqamin ita ake so ayi

Kafin Jabir yayi magana wayar daddy tadau qara

Gabansa ne yafadi dayaga sunan Abba baro baro ajikin screen din wayar

Ahankali ya amsa, acan kuwa Abba yanata Fama da jama’ah Ana jiran ango yazo a daura aure tunda yace zasuzo daga baya

Abba yace Ina kuka tsaya ne, har yanzu shiru babu ku

Sumar kansa yashafa yace Abba Mota ce ta lalace mana ahanya

A a Mota ta lalace muku bazaku tsaida wata ku taho ba, yanzu Yaya kukeso ayi?

Abba kawai a daura

Abba yanajin haka yashaidawa mutane ango Mota ta lalace musu

Dan haka a daura aure

Babu Bata lokaci aka daura auren
Amal da karaam, Akan sadaki nera dubu Dari biyu, lakadan ba ajalan ba

Comments ????

Mrs Usman ce ✍????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

10

Agida kuwa anata hidimar biki, yan’uwa daga Niger sunzo, sai kuma maqota da yan’unguwa dasuka yiwa umma Kara suka zazzo

Nikuwa muna daki nida rumaisa Sai qawaynmu yan islamiya dasuka zo mana

Ajima kadan in goge hawaye, naqiyin wata kwalliya, mutane kowa Sai magana yake in tashi in shirya, na zauna Ina kuka kamar Wanda akamin dole, maisah ce mai kareni da cewa kukan rabuwa da umma ne, dahaka take rufe musu bakinsu
Da mutane suka ragu maisah tace Amal banga angon namu ba, ai yakamata ace yazo kun gaisa ko
Idanuna jajir nace maisah basai yanaso ba zaki ganshi
Shimafa bayaso, ninarasa dalilin baba nayin wannan aure, tunda babu Wanda Yake so kawai a rabu damu,
A a Amal duk abinda babba yahango yaro bazai hangoba, kede kiyi biyayya da hakuri Dan Allah Amal

Nace to maisah ta

A kofar gida kuwa, Ana gama daurin aure aka shigo da kayan lefen akwatuna dozin biyu
Baba yace ai alhaji ku koma da wasu kawai, kayan sunyi yawa, Abba yace haba Malam Muda muke cewa sunyi kadan, Dan Allah kadena wannan maganar adauki kayanta abata, haka aka shiga dasu gida, jama’ah kowa yagani, yana tofa albarkacin bakinsa

Abinci kuwa Sai kawo shi ake baqi kowa yaci yakoshi babu laifi anyi musu karba ta mutunci

Bayan azahar aka fara shirin tafiya bauchi tare da amarya, baba hamani yace shi bazai jeba, tunda akwai yan’uwa dazasuje su Gano inda take, hannun ta yakama da kansa yace alhaji ga amanar Amal nan, batada kowa ku kadai tasani, alhaji bazamu lamunci aciwa Amal mutunci ba, ko waye tsaf zan hawo Mota inzo in dauki yata mu tafi

Abba yace haba Malam, ai Amal kamar ya take awajena, batada banbanci itada daddy, insha Allah baza’a samu ko wacce irin matsala ba

Haka iyayenta sukai mata fada, aka daukesu Sai bauchi, hannun ta yana cikin na rumaisa

 ***      ***       ***

Shahid Ana Kiran wayarka fa
Yana daga kwance yace inaji okasha, wannan Yarinyar ce, kabarta idan tagaji zata dena ai

Haka wayar taita ringing, karshe ma Sai ya kashe wayarsa baki daya

Shahid wannan tunanin fa babu inda zai kaika, ni a ganina tunda yarinyar nan anriga anyi auren ta, kawai ka hakura, ga wata anan yarinyar nan tana Mutuwar sanka, meyasa bazaka amince ba

Kallan okasha yayi da kyau, okasha? Kalau kake kuwa? Ni in auri wa? Yarinyar da batada aiki Sai tallar jikinta a titi

Tana ganin hakan shine wayewa, tayaya zan auri sauran kallan wasu

Hmm ajiyar zuciya nazy yasauke, daya gama Jin duk kalaman su, yace Lalle Shahid kana da aiki agabanka, to yanzu a Ina kake tunanin zaka samu irin yarinyar dakake so?
Kullum cikin hijab
Bafa zaka samu ba

Zan samu nazy, Amal, Amal dina haka take, dahaka nayi Mata tarbiya tun tana qarama

Amal Amal Amal, kaide komai Amal, to yanzu de matar wani ce, tunda tariga da Tafita daga hannunku
Lover boy kadau qaddararka kawai

  ***     ***     ***

Kema de shahida da tsinannan naci kike, kin kira yaqi yayi picking, kinsake kira yakashe wayarsa, Amma ahakan zaki debi jiki kibishi gidansu, wallahi ni DANA SANI ma daban fada miki inda gidan yakeba

Sunkuyo wa tayi daidai fuskar jamcy, tace inde naci yana bada soyaiya, to naci na zai bani soyaiyar sa
Tamiqe ta dauki jambaki ta shafa, Dan qaramin mayafi ta dauka tayi rolling, sosai tayi kyau, doguwar face dinta ta tsaru

Jakarta ta dauka, tace Shahid na shahida ne, Babu me shiga tsakanin mu

Jamcy batasan lokacin datasa daria ba, ta kwanta, tace Allah yadawo dake lafiya, ban fara shirya karbar dizgi awajan da namiji ba

Tana fita Bata zarce ko Inaba, sai gidansu Shahid
Nocking tayi, suka Bata damar shiga
Dukansu suna falo

Shahid yana ganinta ya lumshe idonsa, shikam yagamu data kansa, matar datake bin namiji har gida Wai ita ake kira ya aura

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button