BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da yamma suna Dakin momy su yasu, momy tana sake yiwa shahida fada, Amal duk tana jinsu yayinda take warewa shahida kayan dazata saka wajan dinner anjima
anty mufy ce tahadawa shahida ruwan magani tabata tasha, sannan ta kalli Amal tace kema bari azubo miki
Cikin sauri tace a a anty wallahi kibarshi nagode

Har taso bawa anty mufy da shahida daria

Daddy ne yashigo Dakin da sallamar sa, yana neman Amal, saboda yaje Dakin nata Bata nan, kuma yaduba yaga baiga kowa acikinsu ba, Dan haka yayo nan Dakin

Da mamaki afuskar momy ta dube shi tace yanaga kana tafiya daqyar ne? Qeyarsa ya Sosa, yace momy wallahi nagaji ne dayawa

Tace hakane Toya za’ai

Qasa yayi da kansa yace momy dama sallama zamuyi muku, mu zamu wuce

Tace Ina kenan?
Yace dama saboda hayaniya tayi yawa anan din, shine nace zamu koma gidan mu

Kallansa tayi, Sarai tasan inda maganar Tasa ta dosa, sai tace a a daddy dama kunada wani gida ne Bayan nan? Jinake Kaine yadace ka zauna anan gidan ba muba
Amma kana cewa zaku koma gidanku?

Anty mufy tace kuma yanzu qanina Ana wannan hidimar zaka dauketa ku tafi?

Momy ce ta kalli mufy sannan tace tace babu inda zataje

Ta maida kallanta ga daddy tace tashi katafi saida safe

Babu musu yace to momy nagode

Haka yatafi dakinsa yana tunanin yanda zai samu kebewa shida matarsa

Da daddare kuwa kowa yayi shirin tafiya dinner, Amal ko mayafi babu, duk inda tayi kowa Kallanta yake, motoci ne sukazo zasu dauki amarya da sauran qawaye awuce wajan, gidan Takoma za’a sake gyara Zaman kwalliya

Tana yin hanyar Dakinta, taji an fuzgota
Qara zata saki, yayi saurin toshe mata baki da hannun sa yace shiiii

Kamar marar gaskya yafara waigawa dayaga babu kowa yajuyo ya fuskanceta yace muje
Tace Ina zamu Yaya daddy wajan din….kafin ta qarasa yace gidanmu

Gidanmu zamuje, magana kawai zamuyi mu dawo
Cikin rashin damuwa tace to idan muka gama Sai muje wajan dinner ko?
Dayaga batada wayo sai yace daga can ma kawai saimu wuce

Tace to Bari insake gyara kwalliya ta, yace toyi sauri Kar afara muna gida

Haka tashiga daki, cikin sauri tagama komai harda sake fesa turare, sannan tafuto, tace muje

Hannunta yakama suka futo harabar gidan, duk mutane har anfara kaisu, sun shiga cikin motar suka zauna abaya shida Ida
Driver yafara ja, daddy ya hango Malam iliya

Umarni yabada akirashi, yana zuwa yace iliya daga yau ka koma bakin aikinka nada

Cikin rissinawa yace to yallabai, angama, yanzu kuwa zan tafi

Glass din motar tinte ya sauke suka tafi

Suna tafiya Amal ta dube shi tace aida kabarshi anan din, nisai Ina Bude gate din

Yasan sarai magana ta fada masa

Amma zai wanke kansa awajanta insha Allah

Ta restaurant suka biya, suna cikin motar akayi musu ordering abinci, sannan suka kama hanyar gidan

Suna Zuwa kuwa suka tadda iliya har yaje, dayake kusa gidan yake babu Nisa

Gidan suka shiga, da ledojin abincin ahannunsa

Direct dakinsa suka tafi, suna Zuwa Amal aka harde a kujera, tace Yaya daddy kayi sauri Dan Allah muyi muyi mu tafi

Shima yace karki damu yanzu kuwa

Babbar rigar sa yacire, yacire rigar jikinsa, sannan yacire dogon wandon
Kan Amal aqasa bataga abinda yakeba, saida taji alamun zai shiga toilet sannan ta dago da kanta tace, Yaya daddy ai wanka?

Shima yace to tayaya zamu tafi ni ban shirya ba? Ke kinci kwalliya nikuma ko oho

Tace shikkenan jeka, yi sauri

Tana zaune Zaman jiransa ta nayi tana duba agogo hannun ta

Yafuto, ya wuce yaje wajan kayansa

Yana duba qananan kayan dazai saka, yaga sabbin kaya aciki,daukosu yayi, yakalli Amal
Allah Sarki ashe shi ta saiwa wannan kayan lokacin da sukaje Germany
Murmushi yasaki yadauka yasaka

Yadawo Gabanta yadauki abincin yace taso kici abinci, banaso kije kinacin wani Abu agaban mutane

Babu musu tasauko qasa idonta akansa, tana kallan yanda kayan yayi masa kyau

Shida kansa yaciyar da ita, sannan yace Shima tabashi, spoon din tadauka zata bashi yace no da hannun ki nakeso
Haka tasaka Hannunta cikin abincin tafara bashi
Ahankali take bashi abincin yanaci har wani lumshe ido yake
Tana gama bashi ta tashi zataje ta wanke Hannunta, ya dakatar da ita ta hanyar riqe hannun ta yace bari kiga yanda ake qarasa aikin lada

Maida hannun yayi cikin bakinsa yana yana sudewa, saida yagama sudewa sannan yakama Dan ya tsanta daya yafara tsotsa ahankali

Gaba daya yafara kashe mata jiki da wannan salon nasa

Cikin rashin kuzari tace baka gama bane, sai a sannan yadawo hankalin sa
Yacika mata hannun taje ta wanke tadawo Dakin

Kamota yayi yace muje muyi maganar mu tafi

Zama sukai agefen gadon yakama hannayenta ya riqe, yace baby kiyi hakuri Akan abubuwan dasuka faru abaya, naji dazu ma kina fadamin maganar gate, ban kori iliya Dan yamin komai ba, saidan Ina kishin ki, banasan abinda zaisa wani Abu yahadaki da maza, bazan yafewa kainaba
Kiyi hakuri kinji? Banayin komai saida dalili

Sim card ya miqo mata yace wannan sabon layin dazakici gaba da amfani dashi ne, anbude miki account dashi, da sauran kudinki aciki, zaki dinga tura musu wanda na ciyar da yaran nan da kikai alqawari, Bayan wata biyar, saboda ancire na wata shida

Wannan kuma ATM dinane idan kina buqatar kudi Sai kije kicire yanda yimiki

Sannan maganar koya miki Mota, bansan Yaya za’ai ba, shahida tayi aure dasai takoya miki
Amma kiyi hakuri zuwa lokacin da zamu samu fita zuwa wata qasar Sai na koya miki

Amal mamaki yakashe ta zaune, ta dube shi tace Amma Yaya daddy yazaka bani atm dinka? Mezan yi da wani kudi kuma Bayan nawa na wajena?
Yace incase, wasu zasu iya neman temako awajanki saiki dauka aciki kibasu, karki damu, dukiyata Dani kaina nakine Amal
Mun Riga da munzama mallakinki, daddy naki ne halak Malak

Ajiyar zuciya tasauke tace Yaya daddy ni banida wanda zan temaka wa Sai mutum daya dayake Raina

Yace waye?
Tace wanine hamza, daya temakamin lokacin dazan tafi jigawa

Yace ok kice shine ya nuna miki hanyar guduwa ko? Amal tace Yaya daddy ba abinda kake tunani bane, nide kawai Ina San temaka masa ne

Kafada yadago yace saide kisa ayi masa komai Sai afada masa daga kene
Amma banasan ku sake haduwa dashi, tace to Yaya daddy nagode

Agogo ta kalla tace Yaya daddy mu tafi ko? Kallan ta yayi yace wai kina nufin wajan dinner? Tace emana

Yace haba baby tayaya zan barki kije da wannan uwar kwalliyar? Wallahi inkika fita mutuwa zanyi, Wai kinsan yanda nake sanki kuwa?
Dadi yakama Amal sosai acikin ranta
Matsota yayi yana shakar qanshin dake tashi ajikinta yace wanne irin turare kika saka ne? Inshaqa Nima?
Daga masa Kai tayi
Haka yafara bin jikinta lungu da saqo yana shaqar qamshin jikinta, daga nan labari yafara sauyawa, inda tace batasan zancan ba, haka de yabi ya kalallameta saida yasamu abinda yake so

Bayan komai yalafa ne, ya qaqumeta ajikinsa, yanasa mata albarka,cikin rada yace Mata kinji zafin yanzu?
Kanta ta girgiza, wanda azahiri taji zafin Amma ba kamar wancan Karon ba, Amma danta nuna masa dauriyar ta yasa tace bataji komai ba

Daukanta yayi cancak suka shiga toilet zasuyi wanka, inda sukayi suka gama Amma idon Amal a kulle

Saida suka dade suna fira wajan Sha biyu na dare sannan suka koma wancan gidan

Lafiya tashiga Dakinta cikin walwala da farin ciki Shima haka, Babu wanda ya lura dasu, kasancewar akwai sauran mutane yan biki

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button