FARHATAL-QALB

FARHATAL-QALB 7

PG:7

        ××××.      ××××.     ××××.   

Gaishe ta suka shigaa yi dukkanin su ukun. . Ita din kuma ta dinga amsa su da fara’a da tsantsar farin cikin zuwan su .

“Hajia ga… Wadda zata kama muku aikin.” Ta karasa tana nuna mata Umma Hadiza.

“Ah masha Allah! Ya sunan ki baiwar Allah?”

“Sunana Hadiza.”

“Khadija.. Mai babban suna. Toh ni sunana Hameedah Muhannad. Ni mata ce ta biyu ga mijin mu professor Adams Nasser. Ma’aikaciyar lapia ce ni ina aiki da asibitoci da dama a garin nan domin bangaren aiki na ya shafi surgery. Inada yara hudu. Zayn da Nadra, Nassem sai auta Muhammad muna ce da shi Moha… Muna fatan zaki ji dadin aiki tare damu. Allah ya saka alkhairi a tsakanin mu Amin.. “

Umma Hadiza tayi murmushi tana fadin,

“Aamin …” A hankali kafin ta shigaa cewa,

“A kusa da ku bayan unguwar ku muke. Inada yara 3. Kamal da Waheedah sai Najeebu. Da fari na haifi biyu basu yi rai ba. Nima mu 2 ne awajen me gidan mu . …Mun koma gode da yadda kika karbe mu hannu biyu. Allah ya bani ikon yi muku dede ya kauda fitina a tsakani Amin.”

“Allahumma Aamin” suka hada baki wajen amsawa.

Dr. Hameedah tace,

“Daman zuwan ku nake jira .. Fara aikinnan sai zuwa wani satin nanda kamar kwanaki 10 dai da yardar Allah. Yara sun kammala karatu acan waje. Da bazamu jeba sai da me gidan ya dawo yake sheda mana cewa an samu visa kuma zamu tashi ta Abuja insha Allah. Amman ba zamu dade ba, Sati daya zamuyi. So kafin mu dawo Kano haka dai nasan mayi kwanaki biyu a Abuja don acan ma munada gidah. “

“Allah sarki… Babu komai hajia. Allah ya bada saa kan abunda aka karanta. Allah kuma ya dawo da ku lapia “

“Aamin Yaa rabbi.”

“Bari mu tafi Hajia. Idan kun dawo ma yi waya.”

“Ku tsaya ina zuwa Indo. ” Mikewa tayi ta haura sama. Ba dadewa ta dawo da ledoji bakake manya manyan guda 3 ta shige cikin kitchen ta zuzzuba abunda zata zuba ta fito.

“Gashi Indo wannan ledar kowa dai dai. Sai wannan kudin takalma kuke cewa ko?”

Najan Isubu ta shigaa daria ahankali.

“Laa kuyi dariyar ku. Wai a haka ma fa nayi kokari. Tunda ba yare na bane. Amman de kusan nafi iya hausa akan yare na ma. Amman da da muke Spain hausa ta wallahi tafiya ta dinga yi. Saboda yaren da akeyi acan “

“Kinma yi kokari hajia. Yadda kike hausa wallahi ba wanda zai ce ba yaren ki bane, Sai idan an kalli hasken fatar ki da yanayin ki an san kin sirka da larabawa. ” Cewar Indo ta fada karshen gaskiyar ta.

Ita dai Dr. Hameedah dariya kawai tayi. Ta sake zaro wasu kudin ta bawa Indo tare da doriyar,

“Wannan kuma ki basu Hadiza da yama sunan ta.?”

“Naja’atu.”

“Kwarai Najan ishaq ko?”

“Eh Najan Isubu. “

“Allah sarki. To godia nake. Indo da Najan Isubu. Da Hadiza Allah yabar zumunci. Laa na mance shaf bari na kawo muku ruwa.”

“Aamin Aamin. Ai da kin barshi hajia “

“A’a ba za’ai haka ba…” Miqewa ta sake yi ta bude freezer ta dakko ruwan roba guda 3 da lemuka guda 3. Ta ajiye agaban su. Dan Allah ku tafi dasu. Kamar dai yadda na gaya miki Indo. Insha Allahu munyi magana da mai gidan kan kudin da zaa dinga bawa Hadiza idan ta fara aiki. Ya fadi yadda zai bayar ni kuma na kara dubu goma akai. Hadiza iya abunda zaki dinga yi dukda nasan Indo ta gaya miki yan kananan kayayyakin mu ne haka wanda ba zeyiwu mu saka a injin wanki ba. Bare kuma mu bayar can kamfani su wanke mana. Don ana kai mana wanki da guga. Don suke zuwa da kansu su karba. Ana kuma yi mana a gidah a injin wanki. So abubuwan da zaki dinga wankewa idan ya taso sune su dusters haka na goge goge , Da undies din auta Moha shekarar sa 5. Sai socks ina nufi safa da kuma wanke su mopping stick. Shikenan fannin wanki. Sai yan goge goge na parlorn baban su da kaude kaude na gyaran kitchen. Don munada masu aiki da ke kwana da kuma wanda suke zuwa su tafi. Dubu 30 yayi a wata? Sannan na tsayar miki kwanon abinci safe, Rana, idan kin kai dare ma nanma zaki tafarwa da yara shi. Ina nufin bayan wanda kikaci anan zaki dinga tafiya da wani gidah ko ki aiko a karba miki. Kinji Hadiza. Hakan ya miki?”

Umma Hadiza ta kasa magana saboda tsabar farin ciki. Duk sai ta dubibi ce. Ta kuma kasa boye farin cikin ta. Nan da nan ta dubi gabas ta zuba sujjadar godia ga Allah. Hawaye daya na bin daya.

“Kuka kuma? Haba Hadiza?? Menene na kuka? Idan beyi ba ki fadi nawa kikeso.”

Ina Umma hadiza ta kara man kukanta. Yayinda Najan Isubu ta rungumeta tana lallashi , Kafin ta ce,

“Kukan farin ciki ne take hajia. Hakika hadiza abar tausayi ce. Tabbas Kedin haske ce acikin rayuwar hadiza. Lalle farin ciki marar misaltuwa zai fara wanzuwa a fuskar hadiza da ahalinta. Hajia mungode. Mungode Allah ya saka miki da mafificin alkhairin sa. “

“Ai Hajia wanda ya rab’i wani na ki ma yana cin albarkacin ki bare wanda ya samu kansa a tattare da ke. Dole ta zubar da hawaye hajia. Hawayen farin ciki ne, Hawayen yaye baqin ciki ne. Hawayen samun kanta cikin sabuwar rayuwa take. Hawaye ne mai tattare da labarai da ba zasu fada ba. Tabbas hawaye ne take zubar wa da kololuwar madaukakin farin ciki marar algus. Hajia angode. Angode . Allah ya saka miki da mafificin alkhairin sa. Allah kuma ya raya miki zuri’ah ya albarkance su. Allah kuma ya kara yaye miki dukkanin kuncin da ke cikin rayuwar ki ya lullube ki da lullubar rahamar sa. Da karamcin sa. Da buwayar sa. Da zatin sa. Domin Allah buwayi ne kuma gagara misali. Hajia na ari bakin hadiza nace Allah ya saki da ahalin ki da dik wani masoyi naki a aljannatul frdwas. Allah kuma ya kara wadata ki da wadatar sa Allahumma Amiin “

“Aamin Indo.. Amin “

Umma Hadiza ta sharce hawayenta da kasan rigar ta. Cikin rawar murya da tsagwaran farin cikin data samu kanta aciki tace,

“Hajia banda bakin godia agare ki . Kalmomi sunyi kadan wajen bayyana godia ta agareki.wallah baki ba zai iya fasalta yadda nake ji ba arai na da zuciyata dama gangar jiki na baki daya. Hajia ubangiji Allah ya cigaba da suturta ki. Allah ya wadata ki da ga wadattun bayin sa. Allah ya kara miki karama da karaamci. Ubangiji Allah ya biyaki da aljanna. Allah ya raya zuri’ah. Allah ya biya bukatu na alkhairi. Allah ya kara daukaka . Allah kuma yaja kwana da imanin sa. Allah ya jikan mahaifa idan sun rasu . Yasa aljanna ce makoma agare su. Idan suna raye Allah ya kara musu nisan kwana ya wadata su da lapia . Allah ya faranta miki ya kara arziki mai albarka. Ubangiji Allah ya rubanya miki fiye da yadda kike temako. Allah ya biya ki Hajia. Allah ya biya ki. Allah ya b…”

“Aamin, Ya isa hakanan Hadiza. Dan Allah kubar godiar nan. Wadannan addu’oi haka.” Dr. Hameedah na magana tana matse hawayen dake zubo mata.

“Nagode. Nagode. Wannan addu’oi haka? Jazakum Allah khairan “

Nan suka cigaba da godia. Har dai ta samu ta dakatar dasu. Suka danyi hira. Kafin daga bisani suyi mata sallama su tafi. Kowanne da ledar sa baka ciki da kayan miya da kaji guda biyu. Da taliya guda 5. Da kuma dubu 5 kyauta kowannen su.

“Wannan mata gaskia insha Allahu yar aljannah ce. Wannan abun arziki haka?” Cewar najan Isubu.

Haka dai suka tsaya suna ta mayda zance. Umma hadiza nata jera musu magiya kan su bar kudin ta dau kayan. Saboda hanyar arzikin da suka mata. Sai da Indo tayi jan Ido kafin hadiza ta riqe kudin. Ta kuma sake musu godia kwarai matuka .

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button