Ni da Dr. SadeeqNOVELS

NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 45-46

🅿️ 45&46

“”””Honorable lawal ya wani zare mata ido had’e da cewa”ke lafiya ,kona miki kama da wanda kika sanine??”
dr sadeeq da ammi kuwa sun kafe honorable lawal da ido suna son fahimtar yanayinsa dake nuna rashin gsky”

 Aysha jikinta na kirma batayi mgn ba ta mik'e tsaye da nufin ta fita"

my sholy zoki zauna ki sanarmun meke faruwa ne?”mekuwa zai faru sadeeq?”nasantane? ko kuwa kaida ita kuka had’a baki tazo ta mun sharri ko me?”

Uffan dr sadeeq bece masaba”saidai jikinsa nabashi akwai wata ak’asa”

 Aysha kuwa fita take k'ok'arin yi ammi tace". y'ata dawo kiyi zamanki kinjiko?"batayi musuba tadawo ta zauna tak'i kallon gefen da honorable lawal yake"tana tunanin kod'an uwan sune"tunda tasan mahaifin dr sadeeq yarasu....

kallon ammi honorable lawal yayi yana k'ok'arin mgn ammi tace".kinsan shine Aysha ?"

Honorable yabi Aysha da wani irin kallo”yyinda dr sadeeq ke lura dashi da yanayinsa….

 girgiza kanta Aysha tayi tace".ah ah yamun kamane da wani dana sani"wata ajiyar zuciya honorable yasaki"saidai dr sadeeq be yadda da abinda Aysha ta fad'a ba"sbd ya lura da yadda honorable yaji dad'i har a fuska"

Aysha kuwa sbd batasan waye shiba agidan tak’i fad’a”sannan kota fad’a abin ya wuce bbu amfanin fad’an”

tashi tsaye honorable lawal yayi yabar parlourn”
Ammi ita kanta bata yarda da zancen Aysha ba”amma sai tayi shiru ta kalli sadeeq daketa kallon Aysha tace”.kadawo ne?

Eh ammi”wanka zanyi nakoma ai”yafad’a yana tashi tsaye”Aysha nason ta tashi tanajin nauyi…shikansa dr sadeeq d’in nauyin yamata mgn yakeji”

hakan yasa yafice kawai da tunanin zai tsareta dole tasanar masa miye tasani game da honorable lawal”

Aysha kuwa fira ammi tayita janta da ita”har anty binta tashigo parlourn”Aysha nason ta tambayi ammi gidan hindatu”amma tanajin nauyi kar ace ta zak’e.

suna nan zaune khaleefa yayi sallama anutse yashigo cikin parlourn”

Atake yasaki murmushi sbd ganin Aysha dayayi ta masa girma”

ammi na murmushi ta amsa yagaishesu itada anty binta”kafin ya zauna agefen Aysha”

batare data kallesaba tace”.ina wuni?”lafiya qlau ya gida?”Alhmdllh ta fad’a tana tashi dg kusa dashi ta dawo k’asa kan carpet”

Atake khaleefa ya yarda da maganar hindatu na cemasa datayi Aysha bata sonsa”

Ammi kuwa na lura da abinda Aysha tayi”saima cemata tayi”jeki kitchen gun iya ki amso drinks ki kama khaleefa”

Dato ta amsa tana tashi tsaye ta wuce kitchen”ita kanta anty binta azatonta Aysha adangin mahaifin su sadeeq take”

Aysha na fitowa da tray ahannunta dr sadeeq nashigowa parlourn”

yaci wankan k’ananun kaya”har yagaji dayin kyau”jeans dark blue da fara k’ar d’in t shirt ce ajikinsa”da takalmi sawu ciki bak’i da agogon fata”itama bak’i”jikinsa na fitar da fitinannan k’amshin”yyi kyau masha Allah” sbd ga gyaran fuska da aka mishi”tabon sallayarsa dake tsakkiyar goshinsa yayi bak’i gwanin kyau.

Keys d’in motarsa dana office nashi da wayoyinsa a hannunsa”

Atake yawani had’e rai sbd ganin khaleefa zaune yanata kallon Aysha data duk’a ta ajiye masa tray d’in dake d’auke da ruwa da lemo.

ammi kuwa tamkar tayi dariya”tana mamakin sadeeq data hango kishin Aysha k’arara acikin k’wayar idanuwansa”

ta tuna da yadda y’an mata manya kecewa suna sonsa yana k’iyawa”amma ga k’aramar yarinya nan yafad’a acikin soyayyarta….tabishi da kallo sama da k’asa”aranta tace”.mutum har mutum amma bbu aure”Allah yasa Aysha alkhairi ce garesa ya aureta.

yaya sadeeq dama kana nan?”sannu da shigowa”cewar khaleefa”

Eh “amma yanzun zan koma”ya gida dasu hjy??”suna lafiya”

Aysha dake tsaye kanta ak’asa tace”.ammi na wuce gida”tun yanzun Aysha ?”murmushi kawai tayi batace komaiba”

To kigaida gida”hindatu tace”.tayi fushi dake ko sau d’aya baki kaimata ziyara ba”zanje insha Allah”to shikenan Allah yataimaka”sukayi sallama ta nufi k’ofa anutse”khaleefa yabita da kallo harta fita”

Dr sadeeq dake tsaye yace”.ammi anjima zamuzo da mlm muhammad d’in”to shikenan Allah yakaimu”nizan koma office”to Allah yatsare”itama anty binta ta masa fatan alkhairi”

ya amsa yana juyawa anutse yabar parlourn”

Aysha na tsaye gaban motarsa”tundaga nesa ya hangota”dama jikinsa yabashi zatajirashi”

my sholy nazata ai guduwa zakiyi ko?”bafa haka bane yaya sadeeq”to menene fad’amun??”

murmushi kawai tayi tak’i mgn”yabud’e k’ofar driver sit yashiga”itama ta zagaya baya ta shiga”hakan yafaru akan idon honorable lawal”

Bayan sun bar gidan sun hau saman titi dr sadeeq ya kalleta fuskarsa bbu wasa yace”.sholy!inaso kisanar mun miye alak’ark’i da mutumin nan dakika gani d’azun??”kinsan bansan musu ko k’arya ko?”sbd haka kifad’amun gsky pls”

Ajiyar zuciya tasaki tace”.to amma nima kagayamun meye matsayinsa agunku?”

bayan rasuwar daddynmu ammi nah ta auresa”banason ki b’oyemun komai kisanar mun.

Kanta ak’asa tashiga sanar masa shine mutum na farko da baffa idi yafara had’ata dashi”wai ta masa rakkiya”atime d’in batafi sati guda agidansa ba”anan tamasa bayanin komai…

shiru kawai dr sadeeq yayi”dama binciken dayayi akan honorable lawal anfad’a masa yana neman mata”abin yakai harda k’ananun yara yake b’atawa”sam dole yarabashi da amminsa.lokaci yayi bbu wani zancen d’aga k’afa”

Dan Allah yaya sadeeq karka sanar da kowa”kaga ammi bazata ji dad’i ba.

Karki damu my sholy kinjiko?”dato ta amsa tayi shiru”bbu me mgn kowa da abinda yake sak’awa azuciyarsa”da haka suka iso asibitin….

tana rik’e da keys nashi suka wuce ta bud’e office d’in suka shiga”dr sadeeq ya zauna kan kujera.

zama tayi tana cewa time d’in sallah yayi fa”zanje masjeed nadawo nima yanzun “dato ta amsa”my sholy”yakira sunanta”na’am yaya sadeeq”menene naga kamar bakida walwala??”lah bbu komai fa”d’ago ki kalleni kifad’amun bbu komai mana.

nok’e kafad’arta tayi batayi mgn ba” tashi tsaye yyi yace”.inma ganin mutumin nan yasaki damuwa karki koma damuwa kina jina?”uhmm!natafi to”nasan kedai bakyayin sallah”sbd gulma kike cewa time yayi ko?”kukan shagwab’a tasaka tana bubbuga k’afafuwanta k’asa”

Lumshe idanuwansa yyi yace”.to nadena sarkin rigima”yafad’a yana k’ok’arin fita”Allah yatsare saika dawo”juyowa yyi suka had’a ido”atare suka saki murmushi ya amsa da Ameen yafita.


da misalin k'arfe 5:30 pm"baffa idi ne da Alh nura"suna zaune kan resting chairs a get house d'in Alh nura"

Baffa idi yace”.nikaina abin nabani mamaki dana sakawa y’ar iskar yarinyar nan ido”

Amma tunda tak’i yarda ni aganina kawai zanfito da niyar na aureta”idan akayi auren na huta da ita na tsawon wata 1 saina sako maka ita”

sbd karka manta dodo baya baka kud’i saika bashi jini da wasu kud’in” saiya ninka maka kud’in”

Ai nima shiyasa nakeso kabani dubu dari biyar d’in”nasamu na had’a da waccan mutumin nabashi”amayarmun da manyan kud’ad’e.

nima dg nan nabi sahunku ku masu kud’i”

Hahahahaha”kud’in haram dai ko?”cewar Alh nura”baffa idi na dariya yace”.hakane amma kai naka da halak da haram ka had’asu ko?”

To ai dole sai ankai na halak zai cud’anyasu su zama masu yawa ko?”

Hakane kuma”amma yanzun zanfara sanarwa Aysha zan mata aure nanda sati2″sannan gobe ko jibi naje batsari gun danginmu” nasanar musu bikinta yakusa nanda sati 2″

kaga time d’in dazaka saketa nikuma nayi kud’i”bazasumin k’orafiba”sbd inada kud’i ko?”

Alh nura yace”.hakane kam”suka shek’e da dariyar mugunta….

Aysha na zaune d’akin datake kwana”tana lazimi bayan tagama sallar isha’i”

Tana tuna fad’an ta da dr sadeeq yau ,akan yasiya mata waya me tsada tak’i amsa”shine yayi fushi da ita….gaba d’aya batada walwala sau 3 tana kiransa yak’i d’agawa”amma tabari zuwa gobe tabashi hkri”kuma ta amshi wayar”

Ke kinutsu inason mgn dake”cewar baffa idi daya fad’o d’akin bbu ko sallama” ya jingina jikinsa da bango.

gaban Aysha nafad’uwa tace”.inajinka baffa”

Amatsayi na na k’anin mahaifinki na zab’a miki miji wanda yadace dake”ayau saura kwana 15 bikin”gobe saura sati2 “
Tunda kingama makaranta dole kiyi aure”dg yau na soke zuwanki gun wani aiki” shegen aikin da sai kinyi wata ake baki dubu 25……✍️

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button