GOJE 39 and 40
LAST FREE PEGE
39&40
A takaice dai basu bar masarautar ba sai da duk suka gaisa da duk wanda ya kamata, sun tafi da mamakin mutumci da dattakon mutanan, hakika kaf famliy din yarinyar nagartattun mutane ne masu hankali da sanin ya kamata, ita kadai ce ta fita zakka a cikinsu, koda yake dama haka Allah yake ikonsa, amma duk da hakan itama ba za’a rasa wani abu mai kyau daga cikin dabi’unta ba.
Maimartaba ya basu kyautar dawakai lafiyyayu gami da kayan sarauta kwatankwacin irin wanda yake amfani dasu, mussaman yasa aka kawo masa kayan farauta daban-daban domin ya gwangwajeshi, aikuwa duk cikin kyautukan da yayi musu yafi farin ciki da kayan farautar domin dama yana da bukatarsu, a ganinsa koda zai cika d’aki guda da irinsu ba matsala bace a gurinsa.
Wannan karon gabad’aya a kujerar baya suka zauna, sai da sukayi nisa da tafiya sannan Asp ya fara maganar da tuntuni take cin zuciyarsa.
Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleshi da fadin.” Asp kwata-kwata fa ni wannan al’amari be kwanta min a rai ba, kawai dai na amsa masa ne amma bana jin zan kar’bi auran yarinyar nan.”
[indeed-social-locker sm_list=’fb’ sm_template=’ism_template_9′ sm_list_align=’horizontal’ sm_display_counts=’true’ sm_display_full_name=’true’ unlock_type=2 locker_template=8 sm_d_text=’
This content is locked
Share This Page To Unlock The Content!
‘ enable_timeout_lk=1 sm_timeout_locker=1200 reset_locker=1 locker_reset_after=1 locker_reset_type=’days’ ism_overlock=’default’ ]
Asp ya ‘bata fuska da fadin.” Kada ka zama k’aramin mutum mana, ko dai har ka manta da wanda kayi magana, ba fa gurin wasan yara mukeje ba, ya za’ayi ka amsa masa cewa ka kar’bi kyautarsa daga baya kuma ka shigo da wata magana”
Kallonsa yayi babu farin ciki a fuskarsa yace.” Kunyarsa ce ta sanya na amince na kar’bi kyautarsa amma kai kanka kasan tafiyarmu ba zata zo d’aya da yarinyar nan ba, naji takaici a lokaci da yayi maganar har kake cewa dashi bani da aure alhalin jiyan nan, na nuna maka yarinyar da zan aura a lokacin daka shigo gidana, tabbas ka shigo masa da maganarta ina ganin ba zai k’arfafa maganarsa ba.”
Yace.”UMARU mace hudu Allah ya halasta maka mutu’kar za kayi adalci a tsakaninsu, wannan dalilin yasa lokacin daya fadi maganar na k’arfafa masa gwiwa, haba mutumina ai da kunya a gabansa ka nuna k’yamarka akan jininsa, kayi hakuri da katsalandan din da nayi maka domin ni kaina nasan da cewa yarinyar akwai matsala a tattare da ita, bata da tarbiya ko kadan, to amma hakan ba zai hana a aureta ba tunda wannan matsalar kawai gareta ina ganin idan ta hadu da jajurtacce namiji kamarka to cikin sauki rayuwarta zata sauya.
Ya jima yana nazarin maganganun Asp din kafin yace.” Kasan Allah a tsarina bani da ra’ayi tara mata amma ina ganin hakan ba zai samu ba, Asp ina jin tsoron auran yarinyar nan ta hana ni kwanciyar hankali, wannan dalilin yasa gabadaya al’amarin be kwanta min a raina ba.
Ya dan doki kafadarsa da fadin.” Haba mutumina kai da saba gwagwarmaya da maza mai zai sanya lamarin mata ya dinga baka tsoro! wallahi babu wani abun fargaba da tsoro a cikin al’amarinsu daga zarar ka gane hallayarsu shikkenan zaka zauna dasu lafiya saboda ka cire shakku akan hakan mutumina ba tun yau ba nasha fada maka cewa mace hud’u ce ta dace da kai haba jan wuya kada ka bani kunya mana.”
Dariya ya d’anyi ya bashi hannu suka tafa kafin ya girgiza kanshi da fadin.” Asp ba zaka gane ba ne amma shikkenan kawai mu bar maganar Allah ya tabbatar da alkairi.”
Yace.” Yauwa abunda nakeso naji kace kenan abokina insha Allahu za kayi fari ciki da wannan al’amari.
To har bayan magariba ZINATU na tare da aunty Maijidda komai anan ta gabatar wanka cin abinci da sauransu, hankalinta da tunaninta gabadaya baya kan uwar da ta haifeta ba ballantana kuma wani, hakan yayiwa ita Maijiddan dadi dama babban burinta ta cusa bakin ciki a zuciyar Safah domin itace abokiyar gabarta tun sanda ta fahimci cewa gimbiya Ayshan tayi mata nisa, sai ta mayar bakin kishinta kan Safara’u wacce ita kuma ta mayar da ita shashasha domin duk abunda take na rashin hankali bata biye mata su taru su lalace gabadaya.
Ta dinga bugar cikinta tana bata labarin abubuwan da suka faru, da rayuwar ta a dajin gami da irin wahalhalun da tasha, da labarin zamanta a gidan Asp babu abunda ta rage, sai dai koda wasa bata fada mata irin namijin kokari da kulawar da yayi akanta ba, duk abinda zata a fad’a a kansa sharri ne, har da k’azafin fyad’e kamar yanda tayi masa a gurin Asp, gabad’aya suka had’u suna zaginsa, Aunty Maijiddan ita ke fadin.” Zata shedawa maimartaba komai domin abi mata hakkinta, hakan yayi mata dadi a ranta domin ta san mahaifin nata yana saurarar maganar auntyn nata.
B’angaran Gimbiya Aysha kuwa ganin har bayan isha’i yarinyar bata shigo ba, sai ta kalli sauran yaran nata dake zaune a gabanta tace.” Wannan zaman da kuke bashi da amfani domin dai kune kuka damu da yarinyar nan amma ita bata damu daku ba, da ta damu daku to da yanzu ta nemi inda kuke saboda haka ku tashi ku tafi gidajenku hakan shi yafi ku rabu da ita da mugun halinta, sannan kada wacce tayi yunkurin kiran wayarta ku ‘kyaleta taje tayi rayuwa da wacce ta za’ba a madadi na da kuma ku.”
Cikin rashin jin dadin abinda ‘yar uwar tasu tayi kowacce ta tafi gidanta da bacin ran abun a cikin ranta.
Da yake aunty Maijiddan ce da girki a daran ta zauna tana shirya masa k’arya da gaskiya har da cewa ya dauki mataki mai tsauri a kan yaron domin yarinyar ta sheda mata cewa a yayin zamansu a dajin ya keta mata haddi.”
Duk cikin maganganunta wannan ce kadai ta dauki hankalinsa, hankalinsa ya tashi da jin maganar saboda ya san hakan na iya faruwa idan shad’en ya ratsa, to amma wannan maganar ba zata sanya ya janye manufarsa ta alkairi ba, kamar hakan ma shine rufin asirinsu, duk da hakan zai tuntubi yaran domin tabbatar da gaskiyar magana.
Washe gari da safe kafin ya zauna a fada ya nufi b’angaran matayen nasa domin dubasu, gabadaya ya samesu ba yanda ya saba ganinsu ba, Safah dai tayi kokarin kawar da damuwarta har ya dan zauna sukayi hira, bangaran Gimbiya Aysha kam rigima suka tafka irin wacce sukayi shekara da shekaru ba suyi irinta ba.
Cikin tsananin ‘bacin rai yace.”Aysha yau ni kike nunawa da yatsa akan wani dalili naki na banza da wofi shin wai me Maijidda tayi miki kika dauki karan tsana kika dora mata, baki da kawaici akan ‘ya’ya Aysha baki tausaya mata cewa ita bata dashi meye laifinta anan don ta nuna kauna akan zuriarki.”
Ido jawur! tace.” Bana bukatar ta a cikin al’amarina kuma ba tun yau ba na tabbatar da cewa kaine kake daure mata gindi take mana duk abunda takeso, shin itace ta haifar min ‘yar da zata nuna min iko a kanta! na haifi ‘yata ta lalata min ita duk hakan be isheta ba sai da ta san yanda tayi ta shiga tsakanina da ita da ‘yan uwanta! bayan dawowarta har yanzu bata tako kafarta nan ba ballanatana taje gurin ‘yar uwata, haka nan jiya ‘yan uwanta suka gaji suka tafi gidan auransu bata shigo ba, shin kai a ganinka hakan shine dai-dai? duk abunda yarinyar nan take aikatawa da sanya hannun Matarka a ciki amma kullum sai ka dinga nuna cewa baka gane ba, to ni gaskiya na gaji da wannan al’amari zan kuma dauki mataki.”!
Ganin yanda take numfarfashi! ya sanya shi sauke nasa fushin, hannunta ya rike ya jata suka zauna gefen gado a tare.
Cikin sigar rarrashi yace.”Yi hakuri ki samu nutsuwa muyi magana da fahimta.” ta kalleshi da fadin.” Wane irin nutsuwa zan samu a cikin irin wannan yanayin.”? hannun ya sake rikewa da fadin.” Na yarda da gaskiyarki, Aysha amma kada b’acin rai ya sanya k’ima da mutuncinki ya zube kada fa ki manta kece babba a gidanan kowa yana ganin darajarki kada kuma kiyi wani abun da zai sanya mutuncin ki ya zube a idanun jama’ar dake cikin gidan nan, kibi komai a sannu a hankali.”