GOJE

GOJE 39 and 40

Ad

_____

Tabbas mahaifinta yana tsananin sonta irin son da bayayi wa sauran ‘ya’yansa amma ta sheda cewa shi din kaifi d’aya ne, a haka yake baya ta’ba yanke hukunci ya janye, ita a ganinta kamar hukuncin yayi tsauri da yawa, har yaushe ta dawo da za’a d’ibar mata sati biyu ace ta fito da mijin aure kamar akwai rashin adalci a cikin al’amarin.

Ta samu mahaifiyarta da maganar cewa sati biyu yai mata kad’an tayi masa magana ya ‘kara mata sati biyu ya zama wata daya, Gimbiya Aysha ta nuna sam babu ruwanta a cikin maganar dalili ta riga ta san abunda yake rufe wanda ita Zinat din bata san dashi ba……….da ta samu Safah da maganar itama cewa tayi babu ruwanta kawai dai tayi kokarin ganin ta fitar da miji kafin lokacin daka a bata ya cika, sosai ta shiga cikin wani irin hali mai wuyar fassaruwa tunani kaf ya ta’allaka a gurin neman mafita, babu yanda za’ayi tabi wani daga cikin samarinta nada tace yazo ya aureta wannan zubar da mutunci ne, tsintar kanta tayi da tashin tsakiyar dare domin neman zabin Allah, duk da bata da wani cikakken ilmin addini, a hakan take gabatar da nafila ta zauna saman dadduma tana salatin Annabi kafin ta mika kukanta ga mai kowa da komai.


To kamar yanda suka tattauna maganar commissioner of police da Asp abunda ya faru kenan, domin a daran ranar da ya dawo ya bukaci zama dashi………………Suka fara tattauna maganganu kamar gaske sai dai kuma tafiyar ba tayi tsayi ba suka samu sa’bani dalili bambacin ra’ayi, a take gurin ya nuna masa cewa shi din Jan wuya! ne tafiyar su ba zata zo daya ba, ya nusa masa cewa bashi yakewa aiki ba ‘kasar sa yakewa aiki don haka bai isa ya gindaya masa wasu sharud’a wanda suka sa’bawa dokar aiki ba. mutukar yana bukatar tafiyarsu tazo dai-dai to kowa ya zauna a matsayinsa.

Sosai commissioner din yayi mamakin yaron, koda yake tun yana can ya samu labarinsa da kuma irin alakar dake tsakaninsa da Asp Musa Baharu wanda ya zame masa kadangaran bakin tulu, babu shakka ya sake ya bar wannan ala’kar ta cigaba da gudana to akwai matsala, dole ya shiga ya fita ya raba tsakaninsu, domin samun cigaba da gudanar da al’amuransa hankali kwance.

Ganin cewa ba zai samu yanda yake so ba yasa yayi saurin b’oye manufarsa yayi saurin gyara kuskuransa, kwantar da kansa yayi ya nemi maslaha dashi, sannan ya sheda masa cewa ya shirya tafiya training a sati a mai zuwa zai turashi can Abeokuta ‘karo sani akan aikinsa.” Cike da kwarin gwiwa ya amsa masa ba tare da wata fargaba ba.


Yau ne ya kasance cikar kwanakin da aka d’iba mata, kwance take sai juyi take ta rasa yanda za tayi da rayuwarta, tabbas da kuka yana magani da tuni yayi mata, babu yanda ba tayi da mahaifiyarta kan cewa ta sa baki a cikin al’amarin ba amma fafur! tace babu ruwanta ta dinga kuka tana rokonta amma taki sauranata, sai ta shiga kiran wayoyin ‘yan uwanta tana sheda musu halin da take ciki, ‘yan uwanta mata ne kawai suka saurareta amma Magajin sarki kashe wayarsa ma yayi yace hakan shine daidai idan bata fito da miji ba to duk wanda ya dace a daura mata aure dashi.

Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta mike zaune tare da sauke kafafunta k’asa! kawai ta tsirawa kasan kafet ido kamar me neman wani abu.

Turo kofar dakin yaja hankalinta ta tsirawa kofar ido har sai da ta shigo tare da sallama a bakinta, ido kawai ta zuba mata har ta ‘karaso kusa da ita, ta zauna gefenta tare da ajiye ajakar dake hannunta, wani irin kallo take mata kafin tace.” Me zan gani haka ni Sakina ‘kawata haka ki zama kamar wata zautacciya shin wai bayan kin dawo jinyya kika kwanta dubeki don Allah kin rame kinyi wujiga-wujiga dake.”!

Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke kafin ta kalleta da fadin.” Sakina baki da kirki wallahi ace wai don wulakanci sai yau ki kaga damar zuwa duba ni bayan ta dalilinki na samu matsala, yau satina uku da dawowa amma saboda baki da mutunci sai yau ki kazo.”

‘Yar dariya tayi da fadin.” Ki bari kawai ‘kawata wallahi abubuwa ne sukayi min yawa kin san dai harkar siyasa sai a hankali kullum cikin uzuri muke wannan dalilin ya hana ni zuwa duba ki amma wallahi kina cikin raina.”

Tace.”Ban yarda ba Sakina ai na gane matsayina a gurinki kin nuna min kudi ya fini babu komai ai.” Da sauri tace.”Don Allah kada wannan ya janyo mana samun sa’bani ‘kawata kiyi min uzuri ki kuma yafe min, kina nan a zuciyata.”

Ta’be bakinta kawai tayi ba tace komai ba.

Tace.” Zinat kina da damuwa gaskiya ba haka na san ki ba, ko dai mutanan nan sun samu nasara akanki ina nufin sunyi keta miki haddi”?

Girgiza kai tayi da fadin.” Ko d’aya Sakina kawai ina cikin wani lamari ne wanda na garara fita a cikinsa na rasa yanda zanyi.”

Tace.”Menene yake damunki.”? Kallonta tayi ta girgiza kai kafin ta sheda mata abunda ke faruwa.

Taja tsaki da fadin.” To yanzu ke ya za kiyi ? tunda kince ke ba zaki nemi tsoffafin samarinki ba, hakan yana nufin cewa kin amince da zabin mahaifinki.”

Hawaye ta share da fadin.” Sakina kai tsaye ba zan saduda ba, na san tabbas yau zai kira ni domin jin ta bakina ni kuma anan zan sake rokar alfarma ya kara min kwanaki ina tunanin kafin lokacin na samu mafita.”

Ta’be bakinta tayi da fadin.” Shikkenan ai amma wallahi da nice kai tsaye zan bijire na nuna rashin yarda ta, haba ai tuntuni an daina yayin auran dole.”

Ad

_____

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button