GOJE

GOJE 39 and 40

Ad

_____

Duk cikin maganganunta wannan ce kadai ta dauki hankalinsa, hankalinsa ya tashi da jin maganar saboda ya san hakan na iya faruwa idan shad’en ya ratsa, to amma wannan maganar ba zata sanya ya janye manufarsa ta alkairi ba, kamar hakan ma shine rufin asirinsu, duk da hakan zai tuntubi yaran domin tabbatar da gaskiyar magana.

Washe gari da safe kafin ya zauna a fada ya nufi b’angaran matayen nasa domin dubasu, gabadaya ya samesu ba yanda ya saba ganinsu ba, Safah dai tayi kokarin kawar da damuwarta har ya dan zauna sukayi hira, bangaran Gimbiya Aysha kam rigima suka tafka irin wacce sukayi shekara da shekaru ba suyi irinta ba.

Cikin tsananin ‘bacin rai yace.”Aysha yau ni kike nunawa da yatsa akan wani dalili naki na banza da wofi shin wai me Maijidda tayi miki kika dauki karan tsana kika dora mata, baki da kawaici akan ‘ya’ya Aysha baki tausaya mata cewa ita bata dashi meye laifinta anan don ta nuna kauna akan zuriarki.”

Ido jawur! tace.” Bana bukatar ta a cikin al’amarina kuma ba tun yau ba na tabbatar da cewa kaine kake daure mata gindi take mana duk abunda takeso, shin itace ta haifar min ‘yar da zata nuna min iko a kanta! na haifi ‘yata ta lalata min ita duk hakan be isheta ba sai da ta san yanda tayi ta shiga tsakanina da ita da ‘yan uwanta! bayan dawowarta har yanzu bata tako kafarta nan ba ballanatana taje gurin ‘yar uwata, haka nan jiya ‘yan uwanta suka gaji suka tafi gidan auransu bata shigo ba, shin kai a ganinka hakan shine dai-dai? duk abunda yarinyar nan take aikatawa da sanya hannun Matarka a ciki amma kullum sai ka dinga nuna cewa baka gane ba, to ni gaskiya na gaji da wannan al’amari zan kuma dauki mataki.”!

Ganin yanda take numfarfashi! ya sanya shi sauke nasa fushin, hannunta ya rike ya jata suka zauna gefen gado a tare.

Cikin sigar rarrashi yace.”Yi hakuri ki samu nutsuwa muyi magana da fahimta.” ta kalleshi da fadin.” Wane irin nutsuwa zan samu a cikin irin wannan yanayin.”? hannun ya sake rikewa da fadin.” Na yarda da gaskiyarki, Aysha amma kada b’acin rai ya sanya k’ima da mutuncinki ya zube kada fa ki manta kece babba a gidanan kowa yana ganin darajarki kada kuma kiyi wani abun da zai sanya mutuncin ki ya zube a idanun jama’ar dake cikin gidan nan, kibi komai a sannu a hankali.”

A raunane tace.” To wai yanzu ya kake so nayi? kana so na bari Matarka ta samu nasara a kaina kenan.”

Ya girgiza kansa da fadin.” Maijidda baza ta samu nasara a kanki ba Aysha kin zama murucin kan dutse a ko’ina kece a gaba.”

Ta girgiza kai da fadin.” Ban da gurinka domin yanzu Maijidda ce ke tsara maka komai kuma idan ta fadi magana dai-dai ne a gurina.”

Murmushi yayi yana kallonta, ya san kawai ta fadi wannan maganar ne saboda kishi amma shi duk cikin matansa babu wacce ke tsara masa magana yayi amfani da ita gwanda ma ita takan bashi shawarwari yayi amfani dasu, amma don ya kwantar mata da hankali sai yace.” Na amince da maganarki kuma zanyi wa tufkar hanci banji dad’in abunda suka aikata ba, kuma da kaina zan samesu na nuna musu kuskuransu.”

Ajiyar zuciya ta sauke da fadin.” Shikkenan tunda kace haka amma dai duk da haka ina so kayi min tsakani da matarka babu abunda ya shafeta dani da kuma zuria’ta.”

Domin a zauna lafiya yace.”Kada ki damu zanyi mata magana ta kiyaye shikkenan kowa ya zauna a matsayinsa.” Ajiyar zuciya ta sauke da fadin.” Hakan shine abinda ya dace.

To atakaice dai bai samu damar zaman fada ba sai da ya tabbatar da cewa ya kashe wutar da take kokarin ruruwa, ya kuma yi namijin kokari gurin nunawa Maijidda kuskuranta duk irin hujjojin data kawo masa be saurareta ba, yace.”Idan ita ZINATU tayi aikin kuruciya ke ya kamata ki nuna mata hanyar dai-dai, cewa taje gurin mahaifiyarta da ‘yan uwanta da suka damu da rashinta, amma kema sai ki ka aikata aiki irin na k’ananun yara abunda ki kayi sam be dace ba.”

Kuka ta shiga yi tana fadin.” An nuna mata iyakarta akan abinda take ganin tana da iko dashi, kuma ba tayi hakan da wata manufa ba amma tunda sun juya al’amarin da wata siga daban shikkenan zata cire hannunta daga kan ‘ya’yansu.”

Maganganun da tayi besa yaji tausayinta ba domin idan da sabo ya riga ya saba da jin irinsu kawai dai shi ya nuna mata kuskuranta ne.

Da kanshi kuma ya shiga dakin ZINAT din tana bacci ya tasheta sosai ya rufeta da fad’a irin wannan be ta’ba yi mata irinsa ba, a take a lokacin ya bata umarnin kan cewa tayi maza taje ta nemi afuwa a gurin mahaifiyarta.

Tana share hawaye ta shirya, ya sanya ta a gaba sai da ya tabbatar da cewa ta shiga sashen sannan ya nufi fadarsa.

Da sallama a bakinta ta shiga, ta amsa tare da tsira mata ido har ta ‘karaso inda take ta zube k’asan kafet kawai sai ta rushe da kuka tana takure jikinta.

Zuba mata ido kawai tayi tana mugun takaicin sangartar da take sai kace yarinya k’ankanuwa!

Tsawa! ta buga mata da fadin.” Za kiyi min shuru ko kuwa shashashar banza shashashar wofi.”!

Kokarin hana kanta kukan take amma hakan ya gagara yi take ita kanta takasa tantance me dalilin yin sa.

Tace.” To tunda haka ki ka za’ba bani da magana dake ki tashi ki koma inda kika fito.”?

Kasa tashi tayi sai dai tayi kokarin rage sautin kukan ya cigaba da fita kasa-kasa.

Ad

_____

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button