GOJE

GOJE 39 and 40

A raunane tace.” To wai yanzu ya kake so nayi? kana so na bari Matarka ta samu nasara a kaina kenan.”

Ya girgiza kansa da fadin.” Maijidda baza ta samu nasara a kanki ba Aysha kin zama murucin kan dutse a ko’ina kece a gaba.”

Ta girgiza kai da fadin.” Ban da gurinka domin yanzu Maijidda ce ke tsara maka komai kuma idan ta fadi magana dai-dai ne a gurina.”

Murmushi yayi yana kallonta, ya san kawai ta fadi wannan maganar ne saboda kishi amma shi duk cikin matansa babu wacce ke tsara masa magana yayi amfani da ita gwanda ma ita takan bashi shawarwari yayi amfani dasu, amma don ya kwantar mata da hankali sai yace.” Na amince da maganarki kuma zanyi wa tufkar hanci banji dad’in abunda suka aikata ba, kuma da kaina zan samesu na nuna musu kuskuransu.”

Ajiyar zuciya ta sauke da fadin.” Shikkenan tunda kace haka amma dai duk da haka ina so kayi min tsakani da matarka babu abunda ya shafeta dani da kuma zuria’ta.”

Domin a zauna lafiya yace.”Kada ki damu zanyi mata magana ta kiyaye shikkenan kowa ya zauna a matsayinsa.” Ajiyar zuciya ta sauke da fadin.” Hakan shine abinda ya dace.

To atakaice dai bai samu damar zaman fada ba sai da ya tabbatar da cewa ya kashe wutar da take kokarin ruruwa, ya kuma yi namijin kokari gurin nunawa Maijidda kuskuranta duk irin hujjojin data kawo masa be saurareta ba, yace.”Idan ita ZINATU tayi aikin kuruciya ke ya kamata ki nuna mata hanyar dai-dai, cewa taje gurin mahaifiyarta da ‘yan uwanta da suka damu da rashinta, amma kema sai ki ka aikata aiki irin na k’ananun yara abunda ki kayi sam be dace ba.”

Kuka ta shiga yi tana fadin.” An nuna mata iyakarta akan abinda take ganin tana da iko dashi, kuma ba tayi hakan da wata manufa ba amma tunda sun juya al’amarin da wata siga daban shikkenan zata cire hannunta daga kan ‘ya’yansu.”

Maganganun da tayi besa yaji tausayinta ba domin idan da sabo ya riga ya saba da jin irinsu kawai dai shi ya nuna mata kuskuranta ne.

Da kanshi kuma ya shiga dakin ZINAT din tana bacci ya tasheta sosai ya rufeta da fad’a irin wannan be ta’ba yi mata irinsa ba, a take a lokacin ya bata umarnin kan cewa tayi maza taje ta nemi afuwa a gurin mahaifiyarta.

Tana share hawaye ta shirya, ya sanya ta a gaba sai da ya tabbatar da cewa ta shiga sashen sannan ya nufi fadarsa.

Da sallama a bakinta ta shiga, ta amsa tare da tsira mata ido har ta ‘karaso inda take ta zube k’asan kafet kawai sai ta rushe da kuka tana takure jikinta.

Zuba mata ido kawai tayi tana mugun takaicin sangartar da take sai kace yarinya k’ankanuwa!

Tsawa! ta buga mata da fadin.” Za kiyi min shuru ko kuwa shashashar banza shashashar wofi.”!

Kokarin hana kanta kukan take amma hakan ya gagara yi take ita kanta takasa tantance me dalilin yin sa.

Tace.” To tunda haka ki ka za’ba bani da magana dake ki tashi ki koma inda kika fito.”?

Kasa tashi tayi sai dai tayi kokarin rage sautin kukan ya cigaba da fita kasa-kasa.

Taja tsaki da fadin.” Kullum kina girma amma kina cin ‘kasa! Zinatu ban san lokacin da za kiyi hankali ba, ya kamata ace wannan abunda ya faru dake ya zama izina a gareki amma sai gashi kamar kin ‘karo wani iskancin a inda ki kaje, to don baki mutun tani ba sai me? Allah dai yasa bake kad’ai na haifa ba ballanatana bakin cikinki ya kasheni! ina da wasu bayan ke kuma zan iya yafewa Maijidda ke babu abunda ya dameni.”

Cikin reshin kuka tace.” Mammah don Allah kiyi hakuri wallahi duk abunda ya faru dani tsautsayi ne, kuma ina jin tsoron zuwa a gurinki kiyi min fada shiyasa na zauna gurin aunty Maijidda.”

Tace.”Don Ubanki tsautsayi ko son zuciya? na dauka ranar da al’amarin zai faru sai da kowa ya hanaki fita amma ki ka fakaici idanuwanmu ki kama hanya ki ka fita ai naso wa’inda suka sace ki sun kasheki kowa ya huta.”

Ta dago kai tana kallon mahaifiyarta da mamakin jin furucinta.

Tace.”Eh ki kalleni da kyau! ni nayi wannan furucin saboda duk wani wanda zai zama annoba a cikin al’ummah to bashi da wani amfani a duniya rashinsa shi yafi alkairi.”

Yanzu take kukan gaske hawaye masu tsananin zafi suka shiga sharara a saman fuskarta! tunda take da mahaifiyarta bata ta’ba ganin bacin rainta ba irin na yau ba, har tana mummunan fata a kanta da rayuwarta gabadaya duk sai jikinta yayi sanyi.

Numfashi ta sauke kafin ta cigaba da cewa.” Shekarunki ashirin da hudu a duniya ya kyautu ace yanzu kin nutsu kinyi hankali kin fuskanci abunda yake gabanki amma kullum ke kina daukar kanki yarinya saboda mahaifinki yana sonki yana biye miki da dukkan abunda kike so, kin zauna shirme da shashanci ‘yan uwanki na dakin mazajensu har da zuriarsu, ‘kawayenki wasu daga ciki duk sunyi aure suna zaune lafiya da mazajensu, ke kuwa hakan baya burgeki kullum burinki ki sanya suttura masu tsada kiyi ado da gwalagwala ki shiga motar da kike so ki zaga duk inda kike so kina takamar cewa ke ‘yar mulki ce duk mazan da suka zo da niyyar auranki ki sai ki kore su to me zai sanya mutane ba zasu d’ora ayar tambaya a kanki ba.”?

Shuru tayi tana auna maganar mahaifiyartata, tabbas duk abunda ta fada a kanta gaskiya ne babu abunda tayi mata kazafi a ciki, manya mutune masu kudi da muk’amai daban-daban sun zo da niyyar auranta amma duk ta koresu saboda ta ganin kamar auran zai tauye mata rayuwarta, a yanzu kuma maganganun mahaifiyar tata sun jefeta cikin rud’ani mai tsanani ashe kallon ‘yar iska tantiriya jama’a suke mata.

Ta katse mata tunani ta hanyar fadin.” Daga yau sai yau babu ke babu Maijidda mutukar ni na haifeki na rabaki da ita ban hanaki gaisheta ba amma kada ki kuskura ki sake shiga sashenta ballanatana wata mu’amula ta had’aku, duk wani abu da kika sani naki ne to ki tura a dauko miki kada na sake ganin kafafunki a sashenta, bayan haka kuma ki tashi kije sashen ‘yar uwata ki nemi afuwarta akan irin abubuwan da ki kayi mata, idan kin gama da wannan to d’aya bayan d’aya ki kira wayar ‘yan uwanki ki gaisa dasu, har shi babban yayanku Magajin sarki wanda ki ka dauki karan tsana ki ka dora masa har kina gaba dashi saboda yana nuna miki hanya mai kyau, to shima ki nemi number sa don yanzu haka yana Egypt ki kirashi ki nemi gafararsa, wannan kadai za kiyi ki faranta min rai.”

Ajiyar zuciya ta sauke murya a dashe! tace.”Shikkenan Mammah zanyi duk yanda ki kace amma don Allah kema kiyi hakuri ki gafarceni ki kuma dena yi min mugun baki.”

Girgiza kai tayi da fadin.” Tunda kike shaid’ancinki na ta’ba jifanki da wata muguwar kalmar.”? girgiza kai tayi da fadin ” A’a.” tace.” To yanzu ma raina ne ya ‘baci da al’amarinki, idan kina bukatar albarka to kiyi gaggawar gyara kuskuranki sai mu samu zaman lafiya da juna.”

A sanyaye tace.”Insha Allahu zan kiyaye amma kice kin yafe mun.” jim tayi na ‘yan mintina kafin tace.” Na yafe miki Allah ya shirya min ke shirin addinin islama Allah kuma ya baki miji nagari wanda zaiyi jimiri da hakuri dake da halayenki.”

A zuciyarta ta amsa da “Ameeen ta dan samu sassauci kad’an, da kyar ta yunkura ta tashi tace. “Zan shiga gurin Mommy kamar yanda kika bukata.” Shuru tayi ba tace mata komai ta bita da ido har ta bude kofa ta fita.


Bayan kwana biyu da faruwar al’amarin, ta dan samu sassauci daga gurin mahaifiyarta, suna zaune lafiya wani sa’bani bai sake shiga tsakaninsu ba, kuma tana kokarin yi mata biyayya daidai gwargwado sai dai har yanzu mahaifiyar tata bata wani saki jikinta da ita sosai ba, A gurin Safah kawai ta samun walwala dan wani sa’in ma can take yini, wannan ce damar da ita Safah din ta samu take k’ara nusar da ita hanya mai kyau kuma take kwadaita mata son aure a cikin zuciyarta, sai dai kuma inda gizo ke sa’kar a yanzu bata da wani tsayayye a hannu lokacin da take kan ganiyarta take dasu rurutu amma duk ta koresu, a yanzu dai da zasu dawo da tantance nagartacce a cikinsu, ba kuma ta tunanin neman daya daga cikinsu a ganinta kamar hakan zubewar mutunci ne, ta san dai yanzu labarin dawowarta ya isa ace yaje kunnuwan masoyanta to tana zuba ido duk wanda ya damu da ita a cikinsu zai kawo kansa daga nan sai ta fitar da gwani.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button