GOJE

GOJE 39 and 40

Sai dai kuma a ranar tunaninta ya rushe dalilin hukuncin da mahaifinta ya yanke mata, be fito fili ya sheda mata abunda ke zuciyarsa ba, amma yayi mata hannunka mai sanda cewa mutukar bata fitar da miji a cikin satikan daya bata ba, to lashakka shi zai aura mata wanda yayi ra’ayi.

Tabbas mahaifinta yana tsananin sonta irin son da bayayi wa sauran ‘ya’yansa amma ta sheda cewa shi din kaifi d’aya ne, a haka yake baya ta’ba yanke hukunci ya janye, ita a ganinta kamar hukuncin yayi tsauri da yawa, har yaushe ta dawo da za’a d’ibar mata sati biyu ace ta fito da mijin aure kamar akwai rashin adalci a cikin al’amarin.

Ta samu mahaifiyarta da maganar cewa sati biyu yai mata kad’an tayi masa magana ya ‘kara mata sati biyu ya zama wata daya, Gimbiya Aysha ta nuna sam babu ruwanta a cikin maganar dalili ta riga ta san abunda yake rufe wanda ita Zinat din bata san dashi ba……….da ta samu Safah da maganar itama cewa tayi babu ruwanta kawai dai tayi kokarin ganin ta fitar da miji kafin lokacin daka a bata ya cika, sosai ta shiga cikin wani irin hali mai wuyar fassaruwa tunani kaf ya ta’allaka a gurin neman mafita, babu yanda za’ayi tabi wani daga cikin samarinta nada tace yazo ya aureta wannan zubar da mutunci ne, tsintar kanta tayi da tashin tsakiyar dare domin neman zabin Allah, duk da bata da wani cikakken ilmin addini, a hakan take gabatar da nafila ta zauna saman dadduma tana salatin Annabi kafin ta mika kukanta ga mai kowa da komai.


To kamar yanda suka tattauna maganar commissioner of police da Asp abunda ya faru kenan, domin a daran ranar da ya dawo ya bukaci zama dashi………………Suka fara tattauna maganganu kamar gaske sai dai kuma tafiyar ba tayi tsayi ba suka samu sa’bani dalili bambacin ra’ayi, a take gurin ya nuna masa cewa shi din Jan wuya! ne tafiyar su ba zata zo daya ba, ya nusa masa cewa bashi yakewa aiki ba ‘kasar sa yakewa aiki don haka bai isa ya gindaya masa wasu sharud’a wanda suka sa’bawa dokar aiki ba. mutukar yana bukatar tafiyarsu tazo dai-dai to kowa ya zauna a matsayinsa.

Sosai commissioner din yayi mamakin yaron, koda yake tun yana can ya samu labarinsa da kuma irin alakar dake tsakaninsa da Asp Musa Baharu wanda ya zame masa kadangaran bakin tulu, babu shakka ya sake ya bar wannan ala’kar ta cigaba da gudana to akwai matsala, dole ya shiga ya fita ya raba tsakaninsu, domin samun cigaba da gudanar da al’amuransa hankali kwance.

Ganin cewa ba zai samu yanda yake so ba yasa yayi saurin b’oye manufarsa yayi saurin gyara kuskuransa, kwantar da kansa yayi ya nemi maslaha dashi, sannan ya sheda masa cewa ya shirya tafiya training a sati a mai zuwa zai turashi can Abeokuta ‘karo sani akan aikinsa.” Cike da kwarin gwiwa ya amsa masa ba tare da wata fargaba ba.


Yau ne ya kasance cikar kwanakin da aka d’iba mata, kwance take sai juyi take ta rasa yanda za tayi da rayuwarta, tabbas da kuka yana magani da tuni yayi mata, babu yanda ba tayi da mahaifiyarta kan cewa ta sa baki a cikin al’amarin ba amma fafur! tace babu ruwanta ta dinga kuka tana rokonta amma taki sauranata, sai ta shiga kiran wayoyin ‘yan uwanta tana sheda musu halin da take ciki, ‘yan uwanta mata ne kawai suka saurareta amma Magajin sarki kashe wayarsa ma yayi yace hakan shine daidai idan bata fito da miji ba to duk wanda ya dace a daura mata aure dashi.

Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta mike zaune tare da sauke kafafunta k’asa! kawai ta tsirawa kasan kafet ido kamar me neman wani abu.

Turo kofar dakin yaja hankalinta ta tsirawa kofar ido har sai da ta shigo tare da sallama a bakinta, ido kawai ta zuba mata har ta ‘karaso kusa da ita, ta zauna gefenta tare da ajiye ajakar dake hannunta, wani irin kallo take mata kafin tace.” Me zan gani haka ni Sakina ‘kawata haka ki zama kamar wata zautacciya shin wai bayan kin dawo jinyya kika kwanta dubeki don Allah kin rame kinyi wujiga-wujiga dake.”!

Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke kafin ta kalleta da fadin.” Sakina baki da kirki wallahi ace wai don wulakanci sai yau ki kaga damar zuwa duba ni bayan ta dalilinki na samu matsala, yau satina uku da dawowa amma saboda baki da mutunci sai yau ki kazo.”

‘Yar dariya tayi da fadin.” Ki bari kawai ‘kawata wallahi abubuwa ne sukayi min yawa kin san dai harkar siyasa sai a hankali kullum cikin uzuri muke wannan dalilin ya hana ni zuwa duba ki amma wallahi kina cikin raina.”

Tace.”Ban yarda ba Sakina ai na gane matsayina a gurinki kin nuna min kudi ya fini babu komai ai.” Da sauri tace.”Don Allah kada wannan ya janyo mana samun sa’bani ‘kawata kiyi min uzuri ki kuma yafe min, kina nan a zuciyata.”

Ta’be bakinta kawai tayi ba tace komai ba.

Tace.” Zinat kina da damuwa gaskiya ba haka na san ki ba, ko dai mutanan nan sun samu nasara akanki ina nufin sunyi keta miki haddi”?

Girgiza kai tayi da fadin.” Ko d’aya Sakina kawai ina cikin wani lamari ne wanda na garara fita a cikinsa na rasa yanda zanyi.”

Tace.”Menene yake damunki.”? Kallonta tayi ta girgiza kai kafin ta sheda mata abunda ke faruwa.

Taja tsaki da fadin.” To yanzu ke ya za kiyi ? tunda kince ke ba zaki nemi tsoffafin samarinki ba, hakan yana nufin cewa kin amince da zabin mahaifinki.”

Hawaye ta share da fadin.” Sakina kai tsaye ba zan saduda ba, na san tabbas yau zai kira ni domin jin ta bakina ni kuma anan zan sake rokar alfarma ya kara min kwanaki ina tunanin kafin lokacin na samu mafita.”

Ta’be bakinta tayi da fadin.” Shikkenan ai amma wallahi da nice kai tsaye zan bijire na nuna rashin yarda ta, haba ai tuntuni an daina yayin auran dole.”

Girgiza kanta tayi da fadin.” Sakina ni yanzu sulhu nake nema da iyayena farin cikinsu nake bukata dole nabi komai sannu a hankali amma ni kaina bana tsammanin zan amince da auran wanda bana ra’ayi.”

Tace.”Wannan shine tunani mai kyau, ki zauna kiyi nazari da kyau domin ki taimaki rayuwarki.”

Haka suka wanzu a daki suna k’ulle-k’ullen yanda za’ayi su rusa hukuncin da yake da niyyar tabbata a ranar.

Sai yamma likis tayi mata sallama ta tafi bayan ta bata shawarwarin da take ganin sune kwanciyar hankalinta.

Lokacin da sakon maimartaba ya sameta sai da cikinta ya murd’a tsabar fargaba da tashin hankali, ta kai minti goma a zaune tana sa’kawa da kwancewa kafin tayi namijin kokarin amsa kiran.

Tun kafin ma ya fara magana ta fara kuka, kawai sai ya zuba mata ido yana kallo, ta rarrafa har inda yake ta rirrike k’afafunsa tana wani kuka da fadin.” Ranka ya dade kaji tausayina don Allah kada ka tarwatsa min farin cikin rayuwata bana so ka aura min wanda bana ra’ayi yanzu an dena auran dole idan kace za kayi min hakan zai janyo matsala babba.

Numfashi ya sauke kafin ya tallafo fuskarta, ya sanya hannu yana share mata hawaye rarrashinta yayi da fadin tayi shuru suyi magana ta fahinta.

Da ‘kyar ta iya dakatar da hawayen dake zuba, ta zuba masa idanunta dake cike da fargaba burinta kawai taji abinda ke bakinsa.

Babu alamun wasa a tattare dashi yace.” Wannan shi ya nuna min da cewa baki da matsaya kin dauki maganata a banza ace duk a cikin mane ma auranki baki da gwani wanda kike ganin zai zama abokin rayuwarki, wannan karon ba zan tausaya miki ba, domin ni na haifeki amma na gaji da ganinki a haka babu aure, tunda har na baki dama kika watsar to ni ina da wanda nake ganin ya dace dake wanda kuma nake da tabbacin cewa idan na bashi auranki zai rike min ke da gaskiya da Amana, wannan hukuncin nawa babu wanda ya isa ya janye shi ZINATU mutukar ni na haifeki to baki da mijin aure wanda ya wuce takwarana UMARU ina nufin yaron nan daya cece rayuwarki a daji a kwanakin da suka wuce shine wanda na za’ba miki a matsayin mijin aure, kuma na sheda masa kyautar da nayi masa a ranar suka dawo dake gida, shi din ya kuma tabbatar min da cewa ya kar’ba kyautar da nayi masa saboda haka kada ki bani kunya ko kiyi jayayya da umarnina, insha Allahu nan da wata biyu auranku zai tabbata da ikon Allah.”!

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button