Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
GURBIN IDO

GURBIN IDO 25

Ad

_____

“To Allah ya kyauta,ya kuma shiga lamarin”

“Ameen ya hayyu ya qayyumu,jabiru ya turo nasa kudin ta hannun hisham,duk da naji yace akwai wasu kayayyakin daya siya musu shida jafar din,daso yayi ya biya harda na jaafar din na hanashi”

“Eh gwara da bai biya din ba,gaskiyarki anni,gatan sai yayi masa yawa ya gaza riqe abun da muhimmanci”

“Shina gani ai” anni ta fada da qwarin gwiwa,shi yasa takeson anty maama din,saboda tana da matuqar hankali da nutsuwa

“Ba damuwa,naga wasu akwatuna sabbin design masu goma goma,zan siyawa jabir a matsayin gudu mawata,shi kuma zan siya masa set daya,set daya kuma zan saka cikin lissafinsa”

“Yayi dai dai,Allah ha saka miki da alkhairinsa kema,ya qara muku zumunci,Allah ya qara hadamin kanku” anni ta fada cikin jin dadi

“Ameen summa ameen” daga nan suka shiga tsara yadda komai zai kasance daga kan kayan lefen zuwa sauran hidimomi na bikin,harda yadda za’a gyara maimunatu duka anni ta dora saman wuyan anty maama.

Bayan ta gama da anni kuma ta koma bangaren qannenta,a sannan su salma sun shigo,nan suka zauna suka tsara komai bisa tsari da kuma burgewa,saidai har suka ci suka cinye hirarsu babu giccin maimunatu.

Can cikin garden na gidan ta boye kanta,batajin komai a kan auren tunda batasan meye gundarin abinda ya qunsa ba,bata gama wayewa da sanin meye shi ba,bata saba da zabin abubuwa a rayuwarta ba bare tace wannan zabin bai mata ba,kota damu,kawai dai tana jin kunya da kuma nauyin mutan gidan,tunda tasan meye surukuta,ta gefe guda kuma wani lokacin zuciyarta nayin rawa da kuma d’ar d’ar,tunda ta sani cewa kowacce mace tana auren namijin daya ganta yace yana sonta,itama ta maida masa martanin tana sonshi,amma ita nata angon batasan wanne kala bane,daga wacce duniya zaizo?,yaya kuma zai karbeta?,wadan nan sune kawai abubuwan sa takan nanatawa kanta lokaci zuwa lokaci,saidai yadda taga kowa ya daukaki abun a gidan yana bata mamaki,sannan yadda su laila ke sanyata a gaba,suyita gaya mata abubuwa game da angon nata sai ta yita mamaki,don ita bataga alfanun hakan ba,kiyi kaza kiyi kaza,kullum maganarsu kenan,sun canza mata abubuwa masu yawa,kama daga manta turarenta sa sauransu,itakam duka bataga wannan takurar da tsare tsaren na meye ba,badai a daura aure bane kawai a kaita can gidan ba shikenan dai?,amma magana daya biyu sai suce kina da kishiya,saikinyi kaza kinyi kaza,itakam bataga wani abun damuwa da damun kai ba.

Cikin tsari ilimi da kuma gogewa anty maama ta hada lefe na alfarma,kowacce amarya ta rabauta da akwati goma goma,rana daya aka kai na samiha dana amaryar jabir Aaliya,said kuma kumbo da ammi abokiyar zaman amma ta qarawa kowacce amarya guda hurhudu,shima kowanne shaqe yake da kayan al’adun aure dana zamani,abun dai ya qayatar ya kuma bada sha’awa sosai.

Tarbar girma suka samu daga kowanne bangare na gidajen amaren,suka dawo gida suna yabon tarbar da suka samu,suna kuma tattauna yadda suka fuskanci dangin hajiya Aayah dama ita kanta haj aayah din keji da samiha,kasancewarta diyar fari a wajenta da zata fara aurarwa,su uku kuma kacal Allah ya bata.

Gembu aka yanke za’a kai lefan maimunatu,za’a kuma tafi ne har da ita,daa sunce abar kayan basai an kawo ba saboda gudun wahala da kuma zirga zirga,amma anni tace sam,aure za’ayi mata na gata da kuma ‘yanci cikin danginta kamar kowacce diya,za’a kai mata kayan kamar yadda aka kaiwa kowa,kuma za’a daukota daga gaban danginta a kawo musu ita.

Wannan abun da anni tayi yayi matuqar qara mata kima da daraja a idanun dangin maimunatu,ya kuma qara musu qaimin fidda maimunatu kunya,tare da nuna ita din jininsu ce,duba da abunda bare tayi mata?,ina ga su da suke jininta?.

Kamar yadda annin ta tsara kuwa haka akayi,bikin saura sati biyu suka daga gembu da maimunatu da kayan aurenta.

Gidan kawu sule suka sauka,qani ne ga mahaifin shatu mahaifiyar maimunatu,mutum ne mai zumunci ba laifi,qaddarar abubuwan da suka farun zasu faru yasa ya barwa fulera riqon shatu dama maimunatu,uwa uba kuma da yadda ta nuna tsananin tausayawar tata ga ‘yar uwarta,abinda yaja kawu sule kenan,ya dinga tunanin ko wannan abun ya kawo jituwa da gyaruwar alaqa tsakanin su shatun da yaran inno,yayi tunanin ya barta ko Allah zai sake dai daita al’amarin,kuma har yanzun nan baisan rayuwar da shatu da diyarta maimunatu suka fuskanta ba,yayita yabawa fuleran ma,ya tsammaci aiki tayi da hankali tace a kawo auren nan wajensu sabida girmamawa,baisan ko labari bata dashi ba,sai bayan da yuuma ta tabbatar sun sauka a gembu sannan ta aikaqa fulera da saqon ankai kayan,abinda ya dugunzumata,ya kuma bata mata rai,kamar yadda suke da maimunatu amma ace sai daga wajen baare zata samu labarin aurenta?,ta kuwa ci alwashin tafiya gembu cikin satin ko satin gaba,lallai sai ran kowa ya baci,idan sunsan wata ai basusan wata ba.

Ad

_____

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button