GURBIN IDO

GURBIN IDO 66-70

Idanuwanta a kansa kamar yadda nashi yake a kanta,wani abu mai qarfi yaji yana fusgarsa zuwa gareta,wani abu mai nauyi da tasiri da bai taba jinsa a ransa ba.

Tsoro ya hanata motsawa daga inda take,gani take kamar wani abun zai sakeyi mata,ya karanci tsoronta tsaf,sai ya saki murmushin gefen baki har ya isa dab da ita,a hankali ya sauke zip din jacket din nasa qasa,ya kuma balle botiran gaban shirt dinsa me kauri,sai ya qara matsawa taqi gaba kadan ya manneta zuwa cikin qirjinsa,a tare suka sako ajiyar zuciya,yayin da yaci gaba da sauraren bugun zuciyarta yadda yake gudu fat fat,da alama akwai tsoro tattare da ita.

A hankali ya zura hannayenta ya zagaya dasu zuwa bayansa ta yadda zata rungumeshi sosai,shima haka din yayi ,ya zagaye hannuwansa ta bayanta abinda ya qara musu kusanci sosai,ta shige sosai cikin rigarsa,wani irin dumi da unique qamshin nan nasa ya sauka a hancinta,sanyin data soma ji bayan fitowarta yayi qaura,sai ya dora kansa saman kafadarsa,bakinsa saitin kunnenta cikin fusgar kalaman bakinsa sakamakon yadda tudun qirjinta ya fara rikita masa lissafi

“Relax, don’t scare,am not going to do anything angel” wata ajiyar zuciyar ta kuma saki,a hankali yaci gaba da shafan bayanta kamar yadda akema qaramin yaro duk sanda yake rigima,tsahon wasu mintuna sannan ya jata a hankali,suka dinga takawa kamar me koyon tafiya,saboda yasan akwai mikin ciwo a jikinta.

      Gaban mudubi ya tsaidata,sannan yaja mata kujera ya kuma zareta daga jikinsa yace

“Seat here” a hankali ta zauna tana rintse idanunta saboda yadda wajen har yanzu yake mata ciwo,ya lura da hakan,sai ya saki boyayyen murmushi,wani sashe na zuciyarsa kuma na jin tausayinsa kan barnar da yayi mata.

    Man shafawarsa ya dauko,ya bude ya dora saman mirror din,ya lakato ya daga tattausan tafukan hannunta da kallo da suke jazur, saboda tsaban fari har wani kwanciyar jini sukayi,ya lakata mata man sannan yace

“Lemme help you” sai ya koma daga bayanta ya fara shafa mata a baya.

      Idanunta ta lumshe kawai,zallan mamakinsa suna sake shigarta,kamar ba ja'afar ba,ja'afar din anni da amma,gaba daya kamar wani ja'afar na daban aka sauya mata,dukka ya kwance gaba daya.

       Wasu abubuwa taji suna mata yawo dukka jikinta,in a romantic way yake mata shafan man,tana iya kallonsa ta cikin madubin yadda gaba daya yanayinsa ya canza, tsoro ya sake cikata,ta riqe kukanta da kyau wanda ke shirin qwace mata,idan yace zai sake wani abu da ita ta tabbatar mutuwa zatayi,ba zata iya sake dauka ba.

        Sosai ya dinga qoqarin controlling kansa,bayan ya gama shafa mata zuwa inda yasan ba zata iya ba sai ya dauko hand drayer, already ya iya wannan,shike gyara ma su amna da amra kai sanda suna raye,harma shaheeda,tunda dukansu suna da yawan suma,mamarsu ce kawai bata kaisu ba,don su shi sukayo wajen yawan sumar,don baya sati baiyi gyaran fuska ba,tunda ba kasafai yake rage sumar kansa ba.

        Tsaiwa yayi shi da kansa yana kallon innocent face nata ta madubi bayan ya gama gyara mata gashin ya kuma kame mata shi da band,fuskarta ta fito fayau kuma tayi wani irin fes,idanunta sun sake girma da haske,hakanan siraren labbanta kamar an sake qawatasu,sai ya sunkuya yayi kissing tsakiyar kanta yana lumshe idanunsa.

          Dukka kayanta noqewa tayi taqi sakawa,daya fita ya bata option na ta saka kayan da taga sun mata a dakin,har nashi luggage din ya bude mata yace ta zaba.

        Wata farar turtle neck shirt nashi ta dauko,tana da dan kauri,sannan itama dogon hannu ne da ita,a sake take,don ba size dinta bane,ita ta saka,ta tsaya tana duban kanta a madubi,rigar tayi mata kuma tayi mata kyau sosai,saidai kuma tana kunyar ya ganta da kayanshi a jikinta,ta lumshe idanu tana shaqar daddan qamshin dake fita daga jikin tattausar rigar,batasan me yasa qamshinsa yake kashe mata jiki ba,bata gama wannan tunanin ba ya buda qofa ya sake shigowa dauke data leda mai kauri,sai ta bude fararen idanuwanta da sauri.

       Kamar wani sakarai ko kuma yau ya fara ganinta haka ya saki baki yana kallonta,bai taba ganin kyan rigar ba sai yau data sanyata a jikinta,kallon kallo sukaima juna kafin ta janye kallonta daga kansa,ya tako a hankali zuwa ciki yana ajjiye ledar,zuciyarsa nason ya qarasa gareta amma kuma wani sashen yana masa burki,yana kuma gaya masa

“Dole ka bita a hankali,sai ka rage tsoronka daka dasa mata tukunna, ayanzun a tsorace take dakai,dole kadan nisanceta kadan” da wannan shawarar ya samu waje ya zauna,ya fidda komai dake cikin ledar,breakfast ne da qamshinsa ya cika dakin,da alama wadanda suka tsarashi sun san sirrin girki

“Oya,come and take your breakfast” yayi maganar da mayen kallon nan nasa,qas tayi da kanta,sannan ta fara takowa a hankali,yabi qafafunta da kallo,yadda take tafiyar kawai ya isa ya shaida maka lallai wani abu me girma ya faru da ita.

      Suna cikin yin break din wayarsa tayi qara,sai ya duba me kiran,jabir ne kamar yadda ya zata,daga wayar yayi,amma sai ya sanyata a hands free ya dorata saman cinyarsa,idanuwansa akan fuskarta yayi masa sallama

“Yallabai,wai anya kuwa lafiya?”

“Me ka gani?” Ya tambayeshi kai tsaye

“Jiya nayita bugu na baku dinner dinku,yauma da safe haka zamu wuce strolling da fa’eema zata dan ga gari shima shuru” sai da yayi sipping coffee dinsa sannan yace

“To sai akayi yaaya?” Dariyar da yaketa riqewa ce taso fitowa,ya sake danneta

“A’ah wai kada ka mace ma mutane a daki ne,shi yasa nake cigiyarka,kuma jiya da dare naji dakin kamar ba lafiya ba,har zan kawo dauki fa’eema ta hanani” tsaki yaja yana saurin kashe wayar daga hands free din da ya sakata ya karata a kunnensa

“Amma qur’ani cewa yayi idan baku samu kowa cikin gida ba kada ku shigesu har sai an muku izini,idan ma akace ku koma to ku koma,na meye wannan bin qwaqwafin?,ni bazan huta ba?,ko kai kadai ne me iyali?”

“Allah ya baka haquri,daga abun arziqi?” Yayi maganar yana tuntsirewa da dariya,fatima nata mintsininsa da yi masa sign na ya daina don Allah,don shike maganar amma ita kejin kunyar, batasan yadda zasu hada ido da ja’afar ba,tana matuqar girmamashi

“Inda kazo min daki a jiyan ma saina farfashe maka kai,banyi laifi ba”

“Sai ogaaaaa,tuba nake” ya fada dariyarsa na fita gaba daya

“Da anni fa zan kira…..wallahi nace mata ba lafiya ba” ya sake fada cikin wani karsashi tare da son sake tunzuro ja’afar din

“Sai ka bada himma” daga haka ya yanke wayar kit,wani murmushi da baisan daga inda yake ba na fita a fuskarsa, jabir jabir?,dan uwan da babu kamarsa,yasan ya fahimci komai,don yaga gilmawarsa a fitar da yayi,ya kirashi ne kawai ya zolayeshi,kuma sai yayi din sannan hankalinsa zai kwanta,jabir ya masa haka ina ga anni,gardin case kenan,ya fada a ransa.

afiyyatulkiram: 70

   Seat din kusa da ita fareeda diyar sa'ade ta barwa maimunatu,dukkansu suna ta kallon maimunatu cike da zumudi a zukatansu,saboda suna da.labarinta sarai,sannan ita fareeda tana dan tuna wasu abubuwa da suka faru,tunda da dan wayonta suka bar gembu.

        Cikin tafiyar awannin da suka cur hannun sa'ade yana cikin na maimunatu,kaf maimunatu ta labarta mata dukkan abinda take da buqatar sani,saade ta lumshe idanu hawaye masu dumi suna fita akan fuskarta

“Wata shari’ar sai a lahira,inno taci amanata taci amanar shatu,Allah ya jiqanki ‘yar uwata,matsala na samu akan dukka abinda ya shafi bayanaina,aka samu wasu suka dauka sukayi amfani dasu suka aikata laifi,ya zamana ni ake zargi aketa nema,wannan dalili yasa abbansu yayimin kyakkyawan boyo,sannan akaci gaba da bincike,don yasan muddin ya fiddani aka kamani babu mai fitar dani sai Allah,wannan dalilin ya hanani dawowa gareku,saidai duk da haka nayi amfani da abbansu nayi aike gembu,waya kudi da kaya,ina amfani da wani boyayyen layi ina yawaita kiran inno akan yaya kuke ya lafiyarku?,koda yaushe nunamin take kuna nan lafiya,bana jimawa akan waya shi yasa bana samun damar cewa a bani ku,aike nake akai akai na kudi da kaya ashe baya samunku,ashe sun gama shirya abinda suka shirya,ashe sun cutar min da shatu na,sun kuma cutatar dake kema” sai suka sanya kuka gaba dayansu hannuwansu cikin na juna.

       Dogon numfashi ja'afar dake daga can bayansu ya saki,tunda suka zauna hankalinsa da nutsuwarsa tana kansu,duk da baijin abinda suke fada amma yana iya fahimtar kuka suke,yana kuma ji a zuciyarsa maimunatun kuka take da gasken gaske,yana ta son ya daure amma ya gaza,yana jin kukan nata yana tabashi sosai

“Please,ka gaya mata ta daina sakata kuka haka” ja’afar ya fada idanuwansa a kansu,kallonsa jabir yayi baki galala

“Kai,surukarka ce fa,sannan kuma mamanka ta wani fannin,ita za’a cewa ta daina saka matarka kuka?,bazan iya ba” shuru ya ratsa tsakani,kawai sai ganin ja’afar jabir yayi yana miqewa tsaye,da alama zuwa zaiyi kenan ya shaidar mata da kansa.

      Saurin damqoshi jabir yayi,don yasan tsaf xai aika

“Haba mana,kayi haquri mana romeo,dole fa suyi kuka,don bakasan komai bane” da mamaki ya juyo ya dubeshi,duba na son sanin abinda bai sani din ba,ba tare da yace komai ba jabir ya karanceshi,sai yace dashi

“Zauna na fada maka” ba musu ya koma ya zauna din,ya kuma tattara dukka hankalinsa ga jabir,yayin da jabir ya soma magana a nutse,dama.ya jima yana fatan zuwan wannan lokacin da ja’afar din zai san labarin maimunatu,yasan halinsa sarai,yana da wani irin tausayi na daban q zuciyarsa,sanin labarin nata zai sake haifar da wata alaqa mai girma a tsakaninsu,inda a baya ne,yasan halinsa……bazai taba tsaya ya saurareshi ba,coz bashi da interest,idan kuma yayi loosing interest akan abu babu mai sanyashi dole face mutum biyu zuwa uku a duniya,anni abbi da amma.

      "Ashe nesa a kusa take?,ke din matar ja'afar ce,ja'afar kamar d'a yake a wajena,saboda dan qanwar abbansu fareeda ne"

“Amma?” Maimunatu ta fada tana dan fidda idanu cikin mamaki,a karon farko sa’ade ta gyada kai

“Qwarai,wala’alla banda matsalar dana samu…..wadda sai yanzu ta warware,dani za’ayi bikinku,nasan anyi bikin,amma ban san amaryar ba,don a sannan ba cikin hayyacina nake ba,yau sati daya kwata kwata da bayyanar gaskiya,aka kuma damqe wadanda suka aikata laifin,wanna shine ya bani ‘yancina” kai maimunatu take jinjinawa,lallai soyayya ta gaskiya abace mai kima daraja da kuma wahala,ta jinjinawa abbansu fareeda da yadda ya bata dukkan kariya,duk da cewa basa a qasarsu,amma ya tsaya mata kai da fata don ganin ya kula da amanar da aka bashi

“Yaranki nawa diyam dita?,duk da nasan ba zai wuce guda daya ba tunda baku fi shekara da auren ba,saidai idan kinyo gadon dangin tamu daadar masu haifar twins” kunya ta kama maimunatu,saita kifa fuskarta a kafadar sa’ade,tana jin kamar ita da daadarta suke magana

“Babu ko daya” murmushi tayi tana gyada kai

“To Allah ya kawo masu amfani da albarka,yasa kiyita haifa mana bibbiyu,zuri’ar shatu na tayi dogon baya” tayi maganar cikin rauni dajin zafin mutuwar ‘yar uwarta,wanda bata sani ba gaba daya sai kwanan nan.

      Hawayen fuskarta ta dauke,ta waiwaya kadan baya inda su ja'afar suke

“Amma naji dadi da naga yadda ja’afar yake miki,da alama akwai tsaftatacciyar soyayya a tsakaninku” a kunyace ta saki murmushi tana yin qas da kanta,sai takejin kamar umma sa’aden tana iya karanto abinda ya faru tsakaninta da ja’afar din kwanaki biyar din da suka shude,don har yau bataji tafiyarta ta koma dai dai ba yadda take ada,sannan kuma ta fahimci akwai sauran dan ciwo ciwo a jikinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button