GURBIN IDO

GURBIN IDO 66-70

       Jin bata amsa ba sai ta dora

“Haka nake fata,ki samu mijin marainiya,kuma ina da cikakken fatan cewa zaki samu haka daga ja’afar,indai yaro yana gadon dabi’u daga mahaifiyarsa,aishatu mutum ce nagartacciya,kawai qauna mai tsafta tsakanina da ita,bansan yaya zataji ba sanda labarin KE JININA CE ya risketa” sa’ade ta qarashe maganar tana gyada kai murmushi na kubce mata.

     Duk yadda umma sa'ade taso ja'afar yabar mata maimunatu su wuce gidanta ko kwana daya suyi amma ya murje idanunsa,bai ma yarda ta ganshi ba,don tuni ya isa motarsa yayi zamansa a owners corner yana jiran isowarta,awannin data dauka ba tare dashi ba sai yake jinsa kamar wanda ya rasa wani sashe na jikinsa,ya sauke hannunsa da yake duban lokaci dai dai sanda take takowa zuwa gaban motar,fareeda da umma sa'aden suna biye da ita.

        Sosai ya zuba mata idanu ransa yana motsuwa,yana kuma tuna labarinta da jabir ya bashi,wani irin nau'in tausayi na musamman na ratsa zuciyarsa kamar zai narkar da ita,how she survive?,rayuwa ba uwa ba uba?,babu yaya babu qani?,ba soyayya ba kulawa?.......tabbas ta cancanci samun komai,ta cancanci ta samu duk wani abu data rasa a baya,sai ya lumshe idanunsa sanda suke gab da motar,yana daukarma kansa wani alqawari,wanda ba wanda ya gayawa,tsakaninsa ne da ubangijinsa kawai.

        "Ina fatan za'a kawomin ita ko ni ayimin alfarma nazo na ganta ko yallabai?" Sa'ade ta fada tana murmushi,kai ya jinjina mata da nashi miskilallen murmushin ya amsata a taqaice

“In sha Allah” tasan halinsa ba tun yau ba,don haka itama bata wani damu sosai ba,ta maida qofar ta rufe musu tana musu fatan sauka lafiya,kafin itama ta juya zuwa motocin da suka zo daukarta,zuciyarta cike fal da kewar maimunatu,wanda inda so samu ne su kasance tare,su kwana gado daya tana sake jin labarin rayuwarta.

        Bata gama dai daita zamanta a cikin motar ba ta tsinci hannunta cikin nasa,ya daga hannun nata a hankali ya cusa cikin qirjinsa yana lumshe idanuwansa.

        Shuru tayi kamar yadda shima yayi shurun,tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa fat fat da qarfi bisa qaramar tazara sosai a tsakani,mintuna kusan uku suka kwashe a haka sannan ya bude idanuwansa ya azasu a kanta

“Awa shida kawai?,ta yaya zan jurema wasu awannin da suka fi haka tsaho da yawa?” Ya fada da mugun taushin,salon maganar daya haifar mata da wata kasala da kuma wani yanayi na daban a zuciyarta,saidai ta share ta kuma danne,taso ta zame hannunta amma ya hana hakan faruwa,yaci gaba da riqon hannun nata cikin nasa.

^^^^^^^^^^Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke sanda ta fito daga wanka,gajiyar da bata jita ba a daxun yanzu tana sauko mata,ta bata kusan awa uku,tunda ta shigo dakin take waya da ‘yan sannu da zuwa gami da zolaya a fakaice,su laila harma da afra,wanda wayar tasu ta sake qara mata kwadayin komawa makaranta,saboda ta bata labarin yadda aketa zuba karatu,don ba zasu jima ba zasu zana jarabawar qualifying su wuce zuwa ss three kai tsaye.

Tsaye tayi gaba mudubi sanye da towel hoodie robe fara tas,idanuwanta nakan kayanta data gama shiryawa tsaf na komawa makaranta tun kafin suyi wannan tafiyar,tafiyar data zame mata mabudi kuma mafari na kalolin rayuwa iri daban daban.

A hankali yake saukowa daga samansa hannunsa riqe da wayarsa yana dannawa,shima yayi wanka ya canza kayansa zuwa wata lallausar over size shirt da three quater wanda ya tsaya masa iya qaurinsa.

Karo na uku idanuwansa suka sauka a sashenta,ya sake canza akalar tafiyarsa zuwa qofar sassan,yayi knocking na wani lokaci,sannan yasa hannu ya murda handle din amma sai ya jishi a riqe gam,hannunsa ya daga yana kallon tafin hannunsa da ya danyi qura,mamaki ya kamashi,jikinsa kuma ya bashi lallai wajen ba kullewar dazu ko jiya bane,amma ina ta fita ba tare da izninsa ba?,ina taje?,bayan ya bar mata digits din da zata nemeshi?,bashi da wannan amsar,don haka ya juya yana barin wajen zuciyarsa na sosuwa,ransa kuma fal da bacin rai.

Samun kansa yayi da nufar sashenta,ya buda qofar ya tura,wannan sassanyan qamshin nata da ya kama sashen har yanzu yana nan daram,sai ya lumshe idanu yana nufar qofar dakin da yake jin tana ciki,tunda dashi tafi amfani.

Har ta gama igiyar robe din ta soma kwancewa taji an turo qofar dakin,sai ta tsaya cak cike da mamaki tana dubansa,don batayi tsammanin ganinsa a dai dai lokacin ba,tana ganin lokacine da zata sake tunda zaya zauna a sassansa.

Yana kuma kallonta yana sake takowa zuwa ciki,wani abu kuma yana narkar masa da zuciyarsa,wankan da tayi ya sake sawa fuskarta tayi fresh sosai,akwai sauran lema a gashin girarta da kuma gaban kanta,zuciyarta ta shiga bugawa sanda taga yana nufota direct,amma kuma sai ta gaza daga qafafuwanta har ya cimmata.

Dab da ita ya tsaya wanda taku daya zaiyi ya hade duk wata tazara dake tsakaninsu,a nutse ya daga hannunsa ya dora saman igiyar rigar,jaa daya yayi mata ta ware,rigar wankan ta fara ware kanta da kanta, tunda dama igiyar ke riqe da ita.

Cikin gigita ta sanya hannunta ta damqe gaban rigar,qaramin murmushi ne ya subuce masa yana duban idanuwanta da suka hautsine da tsoro,har yanzun da sauran aiki kenan ya raya a ransa,yana ci gaba da kallon nata ya zura hannunsa ta tsagar gaban rigar,bata ankara ba ta tsinci sassanyan tafin hannunsa saman cikinta saitin cibiyarta.

Cak numfashinta ya dauke na wucin gadi, kafin ta samu nasarar fusgoshi kuma hannunsa ya fara yin sama,har ya samu nasarar isa muhallin da taketa bawa kariyar,sai ji tayi ta ratsa hannuwan nasa a tsakaninsu da wani salo da ya sanyata dauke wuta.

Qugunta ya riqo da kyau sanda qafafunta suka soma rawa,ya matso da ita jikinsa sosai yana sanya hannunsa ya zare hannuwanta dake riqe da gaban rigar,sannan a hankali ya hada tafin hannunsa da ainihin fatarta mai santsi da laushi ya fara zame rigar gaba daya daga jikinta.

Qanqameshi tayi da kyau don hana faruwar hakan,ta tabbatar idan ya samu nasarar rabata da rigar komai zai iya faruwa,don babu wani abu daya rage a jikinta sai ita,cikin rarrabewar numfashi da yadda laushin fatarta ke shirin zautar dashi ya dora bakinsa saman kunnenta

“Don’t scare,baccin gajiya kawai nazo muyi” sake qanqameshi tayi tsigar jikinta na tashi,bakinta na rawa tace

“Ammm…..bar…..bari na saka riga” dago fuskarta yayi da kyau yana duban tsakiyar idanuwanta da idanunsa da suka soma kaduwa,kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace

“Waye ya gaya miki saka riga ya halatta a irin wannan lokacin?,this is unfair….kamar ha’inci ne fa?,ya zaki lullubemin abun rufar da babu kamarsa a duniya da wata suturar da bata kama qafarsa daraja ba?” Ya fada cikin wani irin shauqi da baisan gana bayyana ba,ya kuma juye mata dukka nauyin maganganun hade da nauyin qwayar idanuwansa,gaba daya jikinta sai ya saki,ta runtse idanuwanta,tana sauraren yadda yake rabata da rigar gaba daya,sannan ya dauketa kai tsaye zuwa kan gadon bayan ya sauke dukka labulen dakin ya kuma rage hasken qwayayen dake ciki,sai dakin ya bada wani ni’imtaccen yanayi.

        Sosai ya manne fatar jikinsu waje daya,ya boyeta cikin faffadan qirjinsa,kusan tare suka saki ajiyar zuciya,ya sanya hannunsa saman kanta a hankali yana shafar sumarta,idanunsa a rufe yana jin bugun zuciyarta,kana daga bisani kuma yaji ya sauya,alamun dake nuna bacci ya dauketa,hannunsa ya dauke daga saman kan nata,ya jata jikinsa sosai yana jin kamar ya bude qirjinsa ya sakata a ciki,babu jimawa shima wani daddadan bacci yayi awon gaba dashi.

Arewabooks:Huguma

gurbin ido

Previous page 1 2 3 4 5 6

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button