GURBIN IDO 66-70

Kanta ta dauke daga qirjinsa saboda yadda qamshinsa ke kashe mata kowacce gaba ta jikinta yana kuma haifar mata da wani irin feelings,tare da tuna nata waccar ranar da ta kusa hallaka yadda dumi da qamshin jikinsa ya bata nutsuwa,ta zame a hankali,sai ya sauke hannayensa a hankali wadanda ya zagaye bayanta dasu,saidai still idanuwansa dake a wani jirkice suna kallon fuskarta data yi wani fresh
“Don’t do this again,idan ka tsorata ambaton sunan Allah ake” kai ta gyada masa idanuwanta na qasa,gaba daya lissafinta a yanzu na yadda zata sutura jikinta ne,ko daya bata samu zaizo ya risketa a haka ba,tana tsoron duk wani acting a gabansa kada ya hukuntata kamar yadda yace,don ta karanci fada da cikawa ne shi din da gasken gaske.
Zamewa a hankali ta baya ya zauna kan bed sofa,yana jin wani abu na tsarga masa mai tsananin qarfi cikin kowacce jijiya da hanyar jini dake jikinsa,matsalarsa na shirin motsawa ta hade masa kuma da zazzabin da tun dazu yake faman son ganin ya kauda shi bai taba shi sosai ba.
Cikin dakiya da juriya data arama kanta ta juya ta koma bakin madubin,a matuqar tsarge take tattare kayan dake kai tana maidasu muhallinsu,duk da abubuwa da yawa batasan ma inda take ajjiyesu ba,batasan me yasa ba,amma gaba daya hankalinta ya dauku ga dumin da taji a jikinsa,wanda har ya fara jirkicewa izuwa zafi,ta gama ta juyo a hankali da nufin isuwa zuwa gado.
Ya fahimci abinda take nufin yi,amma shi idanuwansa basu shiryama hakan ba,bai taba jin wani abu da idanuwansa suka jarabtu da kallonsa ba irin maimunatu,tun yana tuhumar kansa da qaryata kansa kan cewa ba ita yake kallo ba har ya fara gasgata zaton zuciyarsa
“Hadamim coffee” ya fada yana sabule boot din qafarsa dama socks din gaba daya,lallausar qafarsa ta bayyana,ya sauketa saman rug din dake shimfide iya wajen,yana fidda wata zazzafar iska daga bakinsa
“La haula wala quwwata illa billah” ya furta a fili sanda ta bacema ganinsa zuwa qaramin falon dake manne da dakin,wanda acan aka kebance wani guri aka zuba komai na amfanin kitchen.
Wayoyinsa ya ciro da suketa kuwwa ya kashesu gaba daya ba tare da ya tsaya duba me kiran ba,ya cilla wayoyin gefan sofan da yake zaune yana jin yadda mararsa ke sake curewa waje daya tare da wani irin ciwo me suka,idanunsa ya runtse yana kuma cizar labbansa na qasa.
A hankali take takowa riqe da mug da qaramin farantinsa,rufe idanunsan da yayi ya bata damar kallonshi sosai,ba haka tasan shi ba,duk da rashin fara'a da walwalarsa amma yanayinsa ba haka yake ba
“Gashi” ta fada a tausashe tana miqa masa cup din bayan ta isa gabansa,a hankali ya bude idanunsa,suka fara sauka kan fararen cinyoyinta sa rabinsu ya bayyana saboda yadda rigar tadan tattare a jikinta,janye idanuwansa yayi yaci gaba da binta da kallo,har zuwa sanda ya isa ga qirjinta dake tsaye kyam,suka kuma cika rigar baccin sosai,duk da ta jawo lace top din ta daure da igiyar data riqe tsakanin daya gefen da daya gefan,saidai babu abinda ta qara rufe mata,illa ma sanyata da tayi tayi looking so sexy,lumshe idanunsa ya sakeyi,bugun zuciyarsa na sauya,daya tashi bude idanun sai ya saukesu kan fuskarta,wadda tadan ya mutse kadan saboda qosawa data fara yi da tsaiwar
“She’s your wife,halal dinka ne” wanin sauti mai kama da rada ya dinga gaya masa daga can qasan zuciyarsa,qoqari yake ya toshe qofar da maganar ke fita,saidai kamar qara mata girma ake a zuciyarsa,sassan jikinsa kuma yana dada bada goyon baya
Hannu ya miqa a hankali ya zare plate din dake qasan cup din ya ajjiyeshi gefe,ya maida tattausan hannun nasa ya dora saman nata,ya hada da cup din ya riqe gaba daya,kana ya janyota cikin wanin salo na bazata,bai mata masauki ko ina ba sai saman cinyarsa,tsoro da mamaki suka kusa sawa numfashinta ya dauke,sai ta tsaya cak kamar wadda jinin jikinta ya daskare.
Kaman bai aikata ba,yaci gaba da riqe hannunta,yana kai coffe din bakinsa da taimakon hannunta,tamkar dai ita ke shayar dashi,wani irin kurba yake masa,kamar baijin zafin da yake dashi,ga duk me cikakkiyar nutsuwa zai karanci kamar ba cikin cikakken hayyacinsa yake sipping coffee din ba,idanuwansa akan fuskarta data bayyanar da tsoro da razana,ko sau daya bai iya dauke idon nasa daga kanta ba.
Bai iya gama shanyewa ba ya zare cup din daga hannunta yayi wurgi dashi da sauran coffee din a ciki,kafin kwanyarta ta bata abinda ya kamata ta tuna sai taji hannayensa saman qugunta,taja numfashi mai tsaho,kamar ba zata sauke ba sai kuma ta soma fiddashi a hankali
“Har yau baki daina tsoro na ba,kuma har yau baki gayamin me kike tsoro a tare dani ba” yakai qarshen maganar yana dora hannunsa guda daya saman igiyar dake riqe da rigar cikin jikinta.
Bai bata damar bashi amsa ba taji ya ja igiyar kittt sau daya gaba daya ta warware,a hankali ya zura hannunsa a tsakanin rigar ya kuma tura hannunsa ta cikin long sleeve din,sosai tafin hannunsa ya sauka kan fatar damtsenta,taushi da dumin hannunsa ya tsarga mata,tun daga kan fata qashinta zuwa bargota,yayin da dumin nata jikin ya sake kassarashi,tare da yin gaba da duk wani sauran haquri da juriyar da yakejin yana da ita.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 69
Ya tabbatar anni ba zata qyaleshi ba ba zata daga masa qafa ba,ko a yanzun ma baisan wanne kalar tijara zata masa ba idan ta fahimci abinda yake faruwa.
"Gaskiya kana sakani jin kunya wallahi" fatima ta fada tana jifan jabir da harara,ga mamakinta murmushi ne kwance saman fuskarsa,amma kuma hawaye ne ke shirin sauko masa,sosai hankalinta ya tashi
“Sweetheart…..menene?” Hannunta ya kama ya riqe gam yana duban fuskarta
“Real version na ja’afar dina ne ya dawo, alhamdulillah…….bansan wanne kalar godiya zan wa Allah ba,bansan wanne kalar godiya zan yima maimoon ba……jikina ya bani,sannan yanayinsa ya nuna tun daga yadda yake amsa wayata,my ja’afar has back” Sai siraran hawaye suka biyo gefan hancinsa,ajiyar Zuciya ta sauke,ta kuma riqe tafukan hannuwan nasa da kyau
“Alhamdulillah,ita zaka yita maimaitawa,sai kuma ka yawaita yima annabi salati saboda nuna zallar godiyarka ga ubangiji” kai ya jinjina yana sake qaunar matarsa,ko yaushe kalamanta akwai Allah a ciki
“In sha Allah,bansan da waa zan raba wannan farincikin ba bayan ke…..kinsan inda daa ne,ko uffan bazaice min ba,har nayi na gaji na gama,abinda bamu saba dashi ba kenan,duk miskilancin sa babu ni a cikinsa” kai ta jinjina,ita kanta taji dadin hakan sosai.
Wuni sur a dakin sukayishi shi da ita,shima kuma jabir bai sake namansa ba,sosai ta dinga dari dari dashi da kuma jin kunyarsa,don da daddare bayan ya sake sanyata ta gasa kanta,tana tsaye bayan ta fito amma taqi kallonsa,sai ya qaraso gabanta,ya dora hannunsa saman nata sannan ya dagasu ya dora kan kumatunsa na hagu da dama
“Me yasa bakison kallo na?,har yanzu tsoro na kike?,irin tsoron da nake gani a idanunki yanzu,irinsa na gani sanda hannuwana sukayi kuskuren marinki……na baki dama,ki rama marinki adadin yadda kikeso” zame hannunta tayi da sauri tana girgiza kai,ta kuma kasa ce masa komai
“Just do it….kar kiji komai” sake girgiza kanta tayi,bakinta yana rawa
“N……na yafe” shuru yayi yana sake zuba mata idanu,hannayensa zube a aljihun wandonsa yana kallonta,baya gajiya da kallonta kwata kwata,sai ya taka a hankali ya rungumeta ta baya,cikin wani sauti da yafi kama da rada ya soma magana
“Tun randa hannuwana suka kai kan fuskarki na gaza mantawa da abinda nayi mikin,nakeji ban kyauta ba,ban sani ba…..ko tun a sannan ubangiji ya zuba dukkan abinda zai zuba a tsakaninmu?,a lokacin da nake jin duk duniya ba wanda ya kaini rashi,na mareki ne a lokacin da nake cikin tsananin damuwa na rasa shaheeda da amra ta,bisa dukkan alamu Allah ya bani wata shaheedan……zaki samar min new amra?” Karon farko da murmushi mai cike da kunya ya qwace mata,sai ta juyo ta cusa kanta a qirjinsa tana murmushi,kafin kuma ta zare jikinsa a nata,binta yayi da kallo,baiso hakan ba,yaso ne su dan jima a tsaye ko hakan zai rage masa zafi.
°°°°°°°°°dukka kwanakin ukun da suka biyo bayansu kusan biqinta ya dinga yi,bai sake neman komai daga gareta ba,saboda ya tabbatar ta jigata a hannunsa,duk kuwa da cewa kawaici kawai yakeyi da kuma qoqarin kame kansa,amma yana ji a jikinsa,har yanzu bata sake masa jiki yadda yakeso ba,yanata qoqarin ganin yabi kowacce hanya data kamata da zai dasa mata soyayyarsa a ranta mai zafi,amma baiga alamun komai ba daga gareta,saidai shi din ya yadda da kansa,ya kuma tabbatar babu.macen da zata iya tsallake tarkonsa.
Shirinsa bai kammala ba,don haka sanya jabir ya gabatar masa da batun komawa sai ya dubeshi
“Wai nikam duka kwana nawa mukayi?” Cikin mamaki da dariyar yadda lissafi ya bacewa ja’afar din nasa yace
“Iya kwanakin da na gaya maka mana,har ka manta?”
“Gani nayi kamar bamu qarasa ba ko?” Yayi tambayar kamar yana kokwanto,dariya dai sai data zowa jabir
“Akramakallah mr ja’afar,kace kawai honeymoon yayi dadi” cikin basarwa ya dauke kai ya kuma sake hade fuska ganin jabir din yanason ramfoshi
“Mtsweew,matsalata dakai kenan,kawai akwai wasu ayyuka ne da ban kammalasu ba,banason kuma su zame min kwantai”
“Gaskiya ne yallabai…..saika bada himma,zaka iya kammalasu nan da yammacin gobe kafin tashin jirginmu ai,musamman idan ka samu network me kyau” kai tsaye ya fahimci inda jabir yasa gaba,sai ya shareshi kawai bai tanka masa ba.
Gyaran murya jabir din yayi
“Munata waya da anni ne,tana complain na an koma makaranta bamu dawo ba,maimoon din anata kira daga makarantarsu,har sunci satin farko”.
A sukwane ya waiwayo yana duban jabir din,sai da yaji zuciyarsa ta tsinke,tabdijan,ai shi gaba daya ma ya ma manta da wani batun makarantarta,ci gaba yayi da duban jabir din kamar wanda ke neman mafita daga garesa
“Yaya dai?” Ya tambayeshi yana dubansa,kansa ya dauke
“Nothing,kawai babu yiwuwar ta koma din”
“Banjin anni zata bari gaskiya,don tanata maganar kada a katseta”
“Eh,tunda ita ke aurenmu ba ni da ita?” Baki jabir ya bude dariya na matuqar cinsa
“Annin?”
“Eh maryam farouq kumo ba” idanu jabir ya fidda gaba daya sannan ya miqe shima kamar yadda ja’afar ya miqe
“Ah wallahi ka sha kaina,kafi qarfina,an tashi a wasan,zaka maimaita kuma a gaban wadda ka kama sunanta”
“And so what?” Ya fada cikin rashin damuwa,tunaninsa a yanzu shine kawai yadda zai fuskanci anni da maganar qin maidata makaranta,musamman idan ya tuna yadda kwashe dashi sanda take shirin hanashi kaita,hannunsa ya sanya ya shafi sumar kansa tare da furzar da iska daga bakinsa.
°°°°°°°°°°°tun saura awa guda jirginsu ya tashi zuwa nigeria suka isa OR tambo international airport din,don haka dole suka zauna a gates zaman jiran cikar lokaci.
Jabir da ja'afar gaba daya suna waje basu shigo ba,sai ita da fatima,jifa jifa suna taba hira da ita,saidai hankalinta gaba daya ya kasu kashi biyu.
Kashin farko yana ga qofa,tana duban ta inda ja'afar din xai bullo,yau kawai da suka dauki mintuna ba kusa da juna ba sai takejin kamar tayi missing wani muhimmin abu,daya kuma gefen hankalinta yana ya daukuwa ne ga wasu matasan yara su biyu,dayar a qalla zatayi shekara goma,yayin da dayar kuma takai kusan shekara sha biyar,tunda suka zauna a wajen take kallonsu,fuskarsu taketa kalla,sai take ji cikin jikinta da ruhinta kamar ta sansu,kamar ta taba rayuwa da ita,abu na biyu kuma mamarsu da tunda suka shigo wajen fuskarta na kallon babban glass dake wajen,wanda ta nan kana iya hango farfajiyar airport din da jiragen dake girke a wajen,shuru ita daya,bata magana da kowa,saidai lokaci bayan lokaci takan waiwayo tayi ma yaran dake amfani sa wata tab da alama game suke,ta musu magana ta sake maida kanta ga wajen,kamar wadda ke cikin wani zuzzurfan tunani.
A duk sanda tayi magana sai maimunatun taji gabanta yayi mummunar faduwa,saboda sautin muryar irin tata sak,kuma irin ta daadarta,saidai sautin yafi nata nuna shekaru,batasan mene yaketa fusgar hankalinta akanta ba,ta kuma gaza ganin fuskarta,sannan kuma ta gaza dauke idanuwanta daga kan 'yanmatan.
Sau biyu babbar ciki na kallonta,itama sai ta maida kanta ga tab dinta,bata kuma sake dagowa ba,taso sosai ta daina kallon nasu don kada su tsargu,amma kuma ta gaza hakan,tana jin kamar ana fusgar idanuwanta ne.
Cikin haka taji maqogaronta ya dan bushe kadan,sai ta dubi fatima
“Bari na samo ruwa”
“Ehenn,ki tahomin dashi” a nutse ta miqe,ta fara takawa zuwa wajen dispenser dake girke a gefe guda,wadda daura take da matar da hankalinta keta daukuwa a kanta,dab da zata qarasa ja’afar din ya shigo wajen,da fari bata ganshi ba amma shi ya ganta,daga bisani ne taji kamar qamshinsa ya cika wajen,sai ta waiwaya,yana tsaye yana kallonta kansa tsaye,baya ko jin nauyin mutanen dake zazzaune a wajen.