BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

: BABBAN YAYA

Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to
Fauziyya S Madaki
Real Esha

Special Gift to Its Sadeek

Bismillah… Ina farawa da sunan Allah Mai Rahma maijin qai, BABBAN YAYA qirqirarran labari ne, yanda muka fara wannan littafi lafiya, Allah yasa mu gama lafiya, Allah ka haneni da rubuta abinda bazai amfani al’ummah ba, idan anga labari yayi daidai Dana rayuwar wata, to akasi aka samu, Allah yasa mudace

A taqaice, Babban Yaya labarin soyaiya ne,yan’uwan juna makusanta, kwatsam soyaiya tashiga tsakanin su, akwai rikitarwa aciki, saikin karanta Zaki gane wanene masoyinki na gaskiya acikin samarin ki? Saikin karanta Zaki gane ta wacce hanya ne namiji zaibi Dan gujewar auren yarinyar da bayaso salin Alin batare da damuwa ba? Abubuwan sunada yawa, koda kudin ka saida rabonka💃💃

PAID BOOK

1&2

“Wato Alhaji Umaru Naga alama saboda Ina zaune aqauye ban’isa na fadi magana a aiwatar da abinda nayi umarni ba”

Daga d’ayan bangaren Wanda aka kira da Alhaji Umaru yadafe goshinsa,(🤦🏻‍♂ï¸?) waye Kuma yata6o musu Babban yayan nasu?
Ajiyar zuciya ya sauke tareda gyara Zaman wayar dake kange a kunnansa yace “Yaya meyake faruwa? Kaida waye?”

“Au tambayata ma kake meyake faruwa? Umaru dakai da Usmanu kunfi kowa sanin abinda kuka aikata, tayaya zaku bar yaro agabanku shekara da shekaru yana zaune babu iyali? Shekara d’ai d’ai har shekara Talatin da shida NAUFAL yana zaune yana abinda yaga Dama yaqi aure, kukuma saboda ku ‘Yan boko ne kun rabu dashi yana abinda yaga Dama, ni danake Nan qauye ba zance kuyi abu kuyiba, a’a Sai abinda kukai niyya”

Cikin ladabi Alhaji Umar yace “Wallahi tallahi Yaya Bahaka bane, mu kanmu muna bakin kokarin mu akansa, bamu San Yaya zamu yi masa ba, munyi munyi dashi yakawo yarinyar dayake so Amma yaqi”

Cikin fishi Wanda aka kira da Yaya yace “zancen banza zancen wofi, kunje can qasar turawan dayake rayuwa ne kunganshi akame awaje daya? Tayaya yaro baligi irin NAUFAL zaku zuba masa ido? Yafada muku shi gunki ne kokuma dutsi da bazai buqaci mace ba? Jinake haka muke ganinsu a TV tsangal tsangal da gajeran wando suna tamola Waida sunan sana’ah, to Kana katse wayata, ka kirashi kafada masa cewa ni Abubakar yayan mahaifinsa Kuma me iko da fada aji acikin dangin Arabo, nace yakira yarinyar Amini na su daidai ta, idan ma ‘yar bokon yake nema irinsa itama yarinyar ba’a qauye tatashi ba bare ya rainata kamar yanda ya raina ni, zan sako Maka lambarta katura masa “

Alhaji Umar yace”To Yaya, insha Allah zanyi yanda kace, ga Alhaji Usman ku gaisa”
Yafadi maganar yana kokarin janye wayar daga kunnansa
Cikin sauri Yace “A a, barshi kawai, ai duk bakinku d’aya” daga haka yakashe wayar sa.

Alhaji Umar yadago Kansa ya kalli Usman batare da yace komai ba, kallo daya zaka musu ka tabbatar su din jini daya ne, kama suke da juna sosai kamar harta 6aci, basuda jiki sosai kasancewar su asalin buzaye

Alhaji Usman yace”magana yake akan Naufal ko?”

Alhaji Umar ya daga masa Kai, sannan yafada masa yanda sukayi dashi, batare da damuwa ba yace” Babu damuwa, katura masa number kawai, ya kira yarinyar, idan munyi sa’ah Wannan Karon andace shikkenan, mu Dama fatanmu ace yayi auren “

*** ** ***

Sanye yake da Jessy ajikinsa fara tas me dogon wando,kafarsa na d’aukeda farin kambos, kunnansa d’aukeda wani Bluetooth fari me shegen kyau, jogging yake Kansa aqasa, Amma duk da haka mutane Sai magana suke masa yana daga musu hannu kasancewar sa marar son surutu, wayar sa tafara qara yana duba Screen din wayar yaga ansa My Dady, dole ya dakata da gudun dayake tareda riqe waist dinsa yana Dan qaramin haki, dago Kansa yayi tareda amsa wayar bakinsa d’aukeda sallama

Sai a lokacin nasamu damar qare masa kallo, fari ne sosai ko’ina na jikinsa farine tass, hadaddan Gaye ne na fitar Hankali, yanayin tsarin idonsa ma kadai ya’isa yasa Nan take yasiye zuciyar yanmata, inde ka Kalle shi sau daya, dole saika sake waigawa domin sake kallon sa, gaida mahaifin nasa ya farayi Amma yana magana dimples dinsa suna futowa.

Alhaji Umar yace “akwai number wata yarinya Habiba Dana turo ma yanzu, kakirata ku daidaita, Yaya ne yace abaka number, yarinyar aminin sace, idan kun gama daidaita wa saika samu lokaci kadawo gida a tsaida maganar aure, banason jin wata magana Kuma daga baya”

Yana gama yimasa Wannan jawabin yakashe wayarsa

yasan dalilin dayasa Dady yakashe wayarsa, duk lokacin dasuka masa maganar aure Sai yasan irin maganar da yayi yaroqesu akan su qara masa lokaci, to lokaci har yanzu shiru yaqi zuwa 🤔

Wata zazzafar is’ka ya furzar daga bakinsa, cikin wata daddad’ar murya wadda daqyar zakaji meyake fad’a yace “ita Kuma wannan ta wacce hanya zanbi narabu da’ita?” wani tunani yayi, Nan take ya dauki shawarar zuciyar sa yayi Dialing number da’aka turo masa ta Habiba

Bugu uku ta dauka, batare da tayi sallama ba tace “Hello waye”

Sai yaji wani iri banbarakwai, kamar shi ace yakira waya Ana tambayarsa waye, Kuma ba kowa ke tambayar sa waye ba Sai budurwa, shida a koda yaushe yanmata sune suke bibiyarsa saboda su samu kusanci dashi Amma basa gabansa,ya tabbatar inda ace tasan asalin Wanda yake kiranta to babu makawa zata Iya zuba ruwa aqasa Tasha saboda tsananin murna.
Jin shiru har yanzu ba’ayi magana ba yasa tace “Hello wake magana ne?”

Saida yaja wasu second sannan yamotsa pink lips dinsa yace “Sunana Naufal Umar Arabo”

Saida taji yace Arabo sannan tace “Okay, ko kaine Yaron Dan’uwan Alhaji Habu Wanda yake zaune a qauye?”

“Yes”
Shine kawai abinda yace

Daga Nata bangaren tace “Ai sunyi magana da Abbanah, yace zai turomin d’ansa naganshi idan yamin Sai manya su shiga cikin maganar” (😱😂)

Baqin ciki ne yakama shi,ya yatsina fuskar sa, yaso ace yayi tozali da wannan yarinyar yaga me take taqama dashi har haka, har shi zatacewa idan yayi mata? Takuwa San waye shi?
Lumshe Idonsa yayi, hakan da yayi saiya Bawa gashin Idonsa damar bayyana, Zara-Zara dasu dogaye kamar na mace, fuskar Nan tasa murtuk babu alamar fara’ah yace “Yes, nine”

Itama tace “Sai cewa kake kaine kaine, kakasa cewa komai, kana magana kamar me koyon magana, yanda baka son had’in Nan nimafa baso nake ba, karkayi tsammanin sonake, kanamin magana daqyar Kanata wani yauqi saikace mace, fadamin zakai yaushe zaka zo naganka, bawai Kiran waya ba, saboda ni ba’acemin zaka kirani ba, ance min ne zaka zo naganka ko zakamin “

Zuwa wannan lokacin Kam ransa yagama 6aci,(😖😖)
Amma wani bangaren na zuciyarsa dad’i yakeji, ko babu komai yasan yarinyar bazata bashi matsala wajan rabuwar su ba tunda itama bata so, sassauta muryarsa yayi, ya dedeta Kansa, kamar me koyon magana yafara magana a rarrabe”Mene..ne yauqi?”

“Uhm au bakama San menene yauqi ba? Tabdi jam, Allah kenan mehada budurwa da samari Kala Kala,yau Kuma da Wanda nahadu kenan, nikuwa naso ace naganka bawan Allah,Inga mutumin dabai San menene yauqi ba, kafadamin yaushe zaka zo?”

Be damu da wannan dogon surutun Nata ba, asali ma so yake su qarqareta ayau dinnan kowa yakama gabansa, ahankali yace”ni… ni banda lokacin zuwa”

Daga Nata bangaren tace “to Ahaka zamuyi aure bakada lokacin kaina?”

Wani irin murmushin gefen baki yayi, cikin ransa yace anzo wajan, a fili kuwa saiyace “Banda lokaci, Ina wajan neman kudi, kinsan kudi sune gaba da komai, ni kaina banda lokacin kaina bare in samu lokacin wani, kawai neman kudi nasa agabana”

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button